Wednesday, May 6, 2015

Talaitaccen Tarihin Imam Ahmad Bin Hambal


IMAM AHMAD BIN HAMBAL (IMAMU AHLUSSUNNAH)

Imam Ahmad asalin sunansa Shi ne: Ahmad bin Muhammad Bin Hanbal Bin Hilal Bin Asad, Ash-shaibani, Al-marwazi, Abu Abdullah. An haifi Imam Ahmad a shekara ta (164A.H), a Birnin Baghdad na Iraqi, ya kasance daya daga cikin manya-manyan malaman duniya, malami ne wanda ya hada ilimi da tsoran Allah da kuma aiki da abin da ya sani na gaskiya.

Wani Malami Ibrahim alharbi a zamanin yake cewa, ban taba ganin mutumin da Allah ya tara masa il...imin mutanan farko da na karshe ba kamar Imam Ahmad, ana yi masa lakabi da imam Ahlussunnah saboda jajircewarsa da tsananin riko da Sunnah lokacin fitinar: cewa kur'ani makhluq ne, wanda imam Ahmad ya tsaya a kan cewa kur’ani zancen Allah ne kuma ba makhluq ba ne.

Imam kutaiba yana cewa: mafi alkhairin mutane a zamaninmu shine: Ibn Mubarak sannan wannan saurayin, wato Imam Ahmad bin Hanbal, idan ka ga mutum yana son imam Ahmad to ka tabbatar cewa wannan mutumin Ahlussunnah ne. Imam Ahmad ya rasu a shekara ta (241A.H).


Yasir Ramadan Gwale 
06-05-2015

No comments:

Post a Comment