Saturday, May 16, 2015

Gaisawar Buhari Da Mace Ya Jan yo Cecekuce


YANZU DAN BUHARI YA GAISA DA MACE SAI ABINDA YA ZAMA LABARI? 

Gaskiya ni banga wani abin yamadidi da GMB ba akan wannan Musabiha din ba. Domin ai ba wannan ne karon farko da aka taba ganinsa ya gaisa da mace ba. Amma me yasa sai a wannan ne mutane zasu yi ta yada hoton?

Gaisawa da mace laifi ne a Musulunci to amma, idan har GMB yayi hakan to laifin tsakaninsa ne da mahaliccinsa. Bai kamata mutane su shagaltu da bayyana laifin wani ba, alhali su sun take nasu. Babu wanda zai shiga tsakanin Allah da bawansa.

Ya kamata al'umma su shagaltu da tattauna abubuwa masu muhimmanci da zasu janyowa rayuwarsu da ta 'ya 'yansu cigaba, ba tattauna akan wani abu da mutum ba zai iya dakatar da shi ba.

Buhari ya aikata laifi, shin me yasa mutane ba zasu sameshi sui masa Nasiha ba. Kamar yadda da dama suka kalubalanci Sheikh Gumi akan me yasa ba zai yiwa GMB nasiha shi da shi ba.

Har ga Allah abin na bani mamaki yadda naga mutane sun baiwa wannan musabiha muhimmanci wajen tattaunawa bayan ga abubuwa muhimmai, da ya kamata ayi muhawarori domin samun mafita daga halin da ake ciki.

Kuna kallo aka zagi Manzon Allah aka keta alfarmar Musuluncin da muke tut iya da shi a cikin garin kano mutane basu dauki wannan a bakin komai ba sai gaisawar GMB da mace?

Alfarmar Manzon Allah fa aka taba! Aka Zage shi, amma jama'a basu kalli wannan a matsayin abinda zasu bada lokacin su ba sai batun laifin da wani ya aikata tsakanin sa da mahaliccinsa? BI ABI A TA WA UMAR YA RASULULLAH. 

Yasir Ramadan Gwale 
16-05-2015

No comments:

Post a Comment