Saturday, May 30, 2015

Goodluck Jonathan Ya Cancanci Jinjina Da Yabo


GOODLUCK JONATHAN YA CANCANCI JINJINA DA YABO A WANNAN ZABE

Ba shakka maganar ba zata yiwa wasu dadi ba, amma gaskiya ce dole mu fade ta. A hakikanin gaskiya dole a yabawa tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan​ a wannan zabe da ya gabata. Wasu na ganin ai babu wani abun yabawa dan Jonathan ya amince da shan kaye,  wanda wannan Sam ba gaskiya bane, a magana ta gaskiya. 

Me yasa nace haka? Mu kalli kasar Syria, kuma mu kalli abinda ke faru a kasar yanzu, sannan mu kalli yanayin da muke ciki. Mutanan kasar Suriya suka ce, sun gaji da mulkin Shekaru fiye da Ashirin na mulkin zurriyar Assad, dan haka suke san ayi sabon zabe dan samun sabon Shugaban kasa. Amma Bashar  Assad a yace Allah ya kashe duk mutanan Syria shi ba zai sauka ba.

Haka ne ya faru, Assad Yaki sauka ya tabbatar da kansa a Mulki a lokacin da jinin al'ummar Siriyawa yake kwarara a birane Alepo da Dar'a da Homs da Damaskus. Ya rushe kasar gaba daya, ya kashe dubban mutane, a yayin da Miliyoyin suka fice suka bar kasar, da yawan Siriyawa sun zama almajirai a kasashen duniya da dama, Assad ya raba mutane da garuruwan su abin alfaharinsu, da yawan wasu sun bar siriya har abada. 

Yau ko da kasar Suriya ta samu zaman lafiya, shekaru nawa za'a dauka kafin a gina inda Assad ya rurrusa?  Ba komai yasa Bashar Assad aikata wannan mugun ta'addancin ba illa kawai yunkurin tabbatar da kansa a mulki ko ana so ko ba'a so. Yanzu fa batun da ake kasar Suriya ta zama Kango, an rushe ko ina, babu wani abu da yake aiki, ba makarantu, babu asibiti, babu kamfamoni, babu sufuri, komai ya koma zero! Duk sabida tabbatar Bashar Assad akan mulki.

Yanzu tsakani da Allah, da Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi taurin kai irin na Bashar Assad a me muke zaton zai faru a Najeriya? Yaki ne gagarumi wanda za'a samu ba tare da mun shirya ba. Kasashen duniya musamman Turai da Amurka zasu marawa Jonathan baya, musamman idan ya makalawa mutanan Arewa Boko Haram. Yai ta kashe mutane domin tabbatar da kansa a mulki, kuma kasashen duniya na bashi goyon baya.

Duk wanda yake kallon abinda ke faruwa da musulmin Rohingya a kasar Burma ko Myanmar zai tabbatar da cewa kasashen Turai da Amurka munafukai ne, domin duk wani shugaba da zai gallazawa Musulmi suna iya d'aga masa kafa a kauda kai daga gareshi kamar yadda har yanzu babu wanda ya zargi hukumomin Myanmar da aikata laifi ga Musulmin Rohingya, illa Majalisar dinkin duniya dake maganar agaji kawai.

Yanzu idan Najeriya ko Arewa ta fada cikin Yaki gashi ba wani tanadi ake da shi na kariya ba me zai faru? Haka nan mutanan Arewa zasu fantsama kasashen Nijar da Kamar da Chadi da Sudan da sauransu domin neman mafaka. 

Amma a sabida kaucewa fadawa irin wannan hali irin na Mutanan Suriya tare da sallama wa zab'in al'umma, da kuma kaucewa fadawa Yaki.  Duk kuwa da cewar kasashe da dama sunyi Nazarin cewar a wannan lokacin Najeriya zata shiga mummunan Yakin da Allah ne kadai yak san karshensa. Allah cikin ikon sa ya tsallakar da mu fadawa Yaki.

Abin da wasu har yanzu basu fahimta ba shi ne, dan an ce Goodluck Jonathan yayi abin a yaba masa, ai ba shi ke nuna an tsarkaka shi daga laifukan da ya aikata ba. Ba shakka Jonathan nada nasa laifukan masu yawa kamar kowanne tsohon Shugaban kasa a Najeriya, amma wannan ba zai zama dalilin da zai sanya mu kasa yi masa adalci ba.

Na taba fadin cewar, Jonathan mutum ne mai matukar Hakuri da kuma kauda kai. A gefe guda kuma yana da sakaci ainun da abubuwa na wajibi a gareshi, harkar tsaro da cin hanci da muguwar sata da kazamar cuwa cuwa duk sun dabaibaye harkar man fetur a Gwamnatinsa, amma bai yi wani abun ku zo mu gani ba na dakile hakan. 

Amma duk da haka yayi abin a yaba masa kuma a jinjina masa wajen nuna dattako da karbar kaddara tun kafin a ayyana sakamakon zabe. Wannan manazarta da dama suka dinga cewar ya tsallakar da Najeriya daga fadawa Yaki da zubar jini. Shi kansa sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari​ ya yabawa Jonathan ta wannan fannin, ya kuma sha alwashin tsare martabar Jonathan a matsayinsa na tsohon Shugaban kasa.

Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya a kasarmu.

Yasir Ramadan Gwale 
30-05-2015

No comments:

Post a Comment