Tuesday, May 26, 2015

Gareka Malam Fatuhu Mustapha


GAREKA FATUHU MUSTAPHA

Wato irin kiyayyar da abokina Dan Bidiah Fatuhu Mustapha suke yiwa Sunnah ta kai matuk'a. Yanzu kuma, sun gaji da yin soki burutsu akan su Ibn Taymiyya da Muhammad Bin AbdulWahhab, sunga ba ci, sun koma ganin laifin, Saudi Arabia wai dan me, Mamlakar zata baiwa 'yan Najeriya guraben karo karatu su karanci addini?! A cewar Fatuhu Dan Bid'ah, me yasa basa bayar da damar karanta sashin lafiya da injiniya da sauran fannonin rayuwa ga 'yan Najeriya.

Alhamdulillah, muna yiwa Allah godiya da wannan falala da yayi mana. Babu abinda zamu ce ga Al-Saud sai godiya da adduar fatan alheri, domin yanzu haka adadin mutanan da suka zama daktoci a katafariyar Jami'ar Islamic University of Madinah sun kai 25 'yan Najeriya. Wannan jami'ah, ta zama sila wajen ceto miliyoyin al'ummar Najeriya daga B'ata da Bid'ah da shirka da kangarewa Allah.

Abinda su Fatuhu ba su sani ba shi ne, mun fi bukatar sanin addini da yadda zamu bautawa Allah ba tare da mun hada Allah da wani abin halitta ba wajen Ibada (Shirka). Alhamdulillah, Ilimin Tauhidi da su Fatuhu basa son al'umma su sani, kullum yaduwa yake kamar wutar daji. Al'umma kara samun wayewa suke game da addinin, ko wane lungu da sako kahe zaka ga ana karantar da Sunnah, gidajen Radiyoyi da kafafe irinsu Facebook ba abinda kake ji sai maganar Sunnah.

Shi ya sa kullum hankalin su Fatuhu a tashe yake irin yadda suke ganin, kullum kasuwar Bid'ah kara mutuwa take, jama'a sai watsi suke yi da D'arikun Sufaye suna kama Hanyar Sunnah mikakkiya da zata sada su da Allah da ManzonSa ba tare da sunyi shirka ba. Wannan abin da alama ya dugunzuma su Fatuhu, sun rasa abin yi. Shi yasa kullum daga su ce, Ibn Taymiyya kaza da kaza, sai su ce Wahabiyya, Izala da sauransu.

Amma, Albishirin su Fatuhu, ina fatan zasu ce Dabino Ajwa. Muna matukar jin dadi ku ce mana Wahabiya sama da ko wane suna da zaku Jingina mana. Abin da kawai muke so ku gane, shi ne, mu ba wai Daular Sa'udiyya muke bi ba dan yiwa Allah bauta. Muna bin addinin Allah ne, kamar yadda ya aiko ManzonSa Sallallahu Alai Wa Sallam da shi. Muna da yakinin alkhairan da Daular Sa'udiyya ta wanzar yafi sharrinsu, munyi Imani su ne daular da suka fi kowacce Daula a duniyar yau Bin Tafarkin Sunnah. Bamu taba ganinsu a matsayin wasu ma'asumai ba, muna tare da su a inda suka yi daidai, muna kuma barranta daga garesu a inda suka kaucewa Addini. 

Daga karshe, ina amfani da wannan kafa, domin yin kira ga abokina Fatuhu da ya watsar da duk wasu Bidi'o'i da yake yi da sunan addini ko bin darikun Sufaye, ka zo mu bi Sunnar Baban Qassim Sallallahu Alaihi Wa Sallam, hanya d'od'ar da zata sadaka da Allah Madaukakin Sarki lami lafiya ranar gobe alkiyama.

YASIR RAMADAN GWALE
26-05-2015

No comments:

Post a Comment