Friday, May 29, 2015

BUHARI: By an Shan Rantsuwa Kuma Sai Me?


BAYAN SHAN RATSUWA UMAR SAI ME?

Yau Juma'a Babbar Rana a Musulunci, aka rantsar da sabon zababben Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari​ a matsayin Shugaban kasa Karo na biyu kuma shugaba na goma sha shida. Kamar yadda manazarta ke ta fadi, kalubalen da ke gaban sabon Shugaban kasa yana da yawa ainun, sannan al'umma sun zura ido, sun kasa kunne wajen ganin anyi aiki sha yanzu magani yanzu.

Jam'iyar APC da Shugaban kasa sunyi alkawura a lokacin yakin neman zabe. Anyi alkawura musamman akan abinda ya shafi Tsaro da Tattalin arzikin da Ilimi da sha'anin tafiyar da Gwamnati da sauransu. A bisa wadannan alkawaruka da ma wasu al'umma da dama suka zabi sabon Shugaban kasa da jwm'iyawrsa a watan da ya gabata.

Fatanmu da addu'ah da zamu yi wa wannan Gwamnati shi ne, Allah ya basu ikon sauke wannan nauyi, babu shakka Allah ya basu dama ta yin duk  wasu ayyuka da zasu kyautata rayuwar 'yan Najeriya birni da karkara. Muna kuma da yakinin cewar Shugaba Muhammadu Buhari​ zai iya fiye da yadda ake tsammani. Ya Allah ka sahale masa wannan gagarumin aiki. Allah ka sa alkawuran da ya dauka su zama hujja a gareshi ba hujja akansa ba.

Suma sabbin Gwamnonin da aka rantsar a yau, muna yi masu fatan alheri da kuma tuna musu girman kalubalen da ke kansu. Allah ya basu ikon yiwa al'umma hidima, tare da tsare mutunci da martaba da addinin wadan da suke jagoranta. 

Allah ka sa wannan sauyi ya zama alheri ga Najeriya da duk 'yan Najeriya a ko ina suke a duniya. Allah yasa ayi shugabanci bisa gaskiya da adalci. 

Yasir Ramadan Gwale 
29-05-2015

No comments:

Post a Comment