Thursday, July 17, 2014

Shekaru 20 Bayan Da Aka Yiwa Musulmi Kisan Kiyashi A Srebrenica: Kotun Duniya Ta Yi Adalci

SHEKARU 20 BAYAN DA AKA YIWA MUSULMI KISAN KIYASHI A SREBRENICA: Kotun Duniya Ta Yi Adalci

Munira Subasic take cewa da misalin lokacin zawali muna zaune a sansanin 'yan gudun hijira a Srebrenica tun bayan barkewar yaki a Bosnia inda aka farwa Musulmi da kisa babu ji babu gani, tun cikin shekarar 1992, da gumu ta yi gumu yaki yayi yaki ne can wajen shekarar 1995 aka kwaso ragowar Musulmin da suka yi saura aka tattaremu a Srebrenica karkashin kulawar sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya, a cewa Munira muna zaune da zawalin wannan ranar sai ga rundunar mayakan turawa karkashin jagorancin General Ratko Mladić suka kewayemu, suka ware mata daga cikinmu da tsofaffi sai ya rage saura zaratan samari da kuma mazajenmu.

Munira ta kara da cewa da idona naga an hallaka mijina da kuma d'ana, a wannan ranar sai da aka kashe sama da mazaje 8000 a gaban idan sojojin Majalisar dinkin duniya ba tare da sun daga ko icce ba, duk kuwa da irin kururwa da neman taimako da muka dinga yi, muna a taimakawa mazajenmu, amma ihunmu ya kare a kunnen kurame.

Tsohon sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Mista Kofi Aan ya bayyana abin da ya faru a Srebrenica da cewa kisan kiyashi ne da aka yiwa wata al'umma; ya kuma kara da cewa abin da ya faru wani bakin shafi ne a cikin kundin tarihin majalisar dinkin duniya, yaci gaba da cewa, wannan kisan kiyashi da aka yi a Srebrenica shi ne irinsa na biyu a tun bayan yakin duniya na biyu da aka yiwa a Turai, ya kuma bayyana shi da wani abin Allah wadai da dan Adan ya aikawa dan Adam.

Sai dai tun bayan wannan ta'addanci da sojojin turawa suka aikata a watan yulin 1995 a Srebrenica, wadan da abin ya shafa sun shigar da kara kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya dake Hague a kasar Holland. A jiya dai masu gudanar da wannan Shari'ah sun yanke hukunci na karshe tun bayan shekaru 20 da aikata wannan kisan kiyashi, inda suka zargi kasar ta Holland da alhakin abinda ya faru, domin suna da masaniayr hakan zata faru amma suka sanya aka kawo musulmin Bosnia zuwa Srebrenica, haka kuma kotun ta bukaci a biya iyalai 300 diyyar raykan da aka kashe musu.

YASIR RAMADAN GWALE
17-07-2014

No comments:

Post a Comment