Wednesday, July 23, 2014

Makaryata-Mayaudara-Munafukai

MAKARYATA: Wato babu wani abu a cikin harkokin Diplomasiyya kamar karya da yaudara da sauyawa gaskiya wurin zama. Dukkan maganganun da Kerry ya yi a Cairo da wadan da Ban ki-Moon ya yi a Tel Aviv da wadan da Netanyahu da Mahmoud Abbas suke yi sai ka rasa ina hankalin mutnan duniya yake irin yadda suke juya gaskiya kiri-kiri akan abinda ke faruwa a Ghazza. Ta yaya Isareal ta kashe mutanan Ghazza sama da mutum 600 daga 8 ga wannan watan zuwa yau, su kuma 'yan Hamas ana cewa sun kashe 'yan Israela 28 amma duk da haka a UN da Whitehouse da Cairo a dinga ce mana wai Israela na da 'yancin kare kanta! Ta yaya za a iya fahimtar da ni wannan dodoridon?

Israela ta kashe mata da yara da tsoffi ta rusa masallatai ta doki asibitoci da makaranta tana kai hare-hare ta sama da ta kasa da ta cikin teku ace amma wai kare kanta ta ke yi. Amma kuma wai ace Israela ba Palasdinawa ta ke yaka ba, ita da 'yan Hamas take fada. Wannan wacce irin yaudara ce haka, mutane da hankalinmu a maida mu kamar bama fahimtar rayuwa!

Su kansu Shugabannin kungiyar Hamas din da galibinsu sun tare a kasar Qatar suna kwance cikin Ni'ima ana can ana kashe talakawa sai dai kawai surutai da suke ta faman yi marasa kan gado. Itama Gwamnatin Abbas dake Ramallah daman ita da hannun Israeli a kafuwarta babu wani katabus da zasu iya yi. Illa shirme da shirita, domin shekaru nawa ana tattaunawa a Camp David wace irin matsaya ce ba'a cimma ba, babu wani abu da aka cimma da Israela bata sa kafa ta shure ba, amma kuma su Abbas suna cewa wai a tattuna. Ina amfanin Shan ruwa idan baya maganin kishruwa?

Amma kuma duk wannan cin kare babu babbaka da Israela ta ke yi su Abbas da 'yan kanzaginsu sai su nunawa duniya cewai wai abinda yake faruwa ba na addini ba ne, tsakanin Laabawa ne da Yahudawa 'yan share wuri zauna. Allah ka kiyashe mu tabewa.

Hanya guda daya ce da kasashen Larabawa (Musulmi) zasu iya ladabtar da Isarela akan Ghazza. Wannan hanyar kuwa ita ce, su ce sun daina hako Man Fetur har sai Israela ta kwashe tarin jami'an tsaronta daga yankunan Palasdinawa da ta mamaye, sannan su dawo da sayar da man fetur, Na yi Imani irin wannan yaren ne kadai zai shiga kunnuwan Amerika da ita Israelar. Wanda wannan wata hanya ce mai wuyar bi da irinsu marigayi Sarki Faisal na Sa'udiyya ne kadai zasu iya bi babu wata fargaba, Allah ya jikansa da gafara.

Babu shakka abubuwan da suke faruwa a Ghazza kullum kara kazancewa suke yi, asarar rayuka karuwa ta ke yi cikin sauri. Allah ka agazawa wadannan mutane.

YASIR RAMADAN GWALE
23-07-2014

No comments:

Post a Comment