Tuesday, July 1, 2014

Abinda Ya Faru Da Ni Ranar Asabar A Facebook

ABINDA YA FARU DA NI RANAR ASABAR A FACEBOOK

Kamar mako guda da ya wuce na ina goge irin sakwannin da ake turomin a Inbox na babu gaira babu dalili da wasu mata ke turowa, wanda sun addabi mutane da yawa da irin wadannan sakwanni nasu. Ina cikin haka sai ga wata Hala Eberahem ta aiko min da sako, nan da nan na aika mata da martini nace da ita "Very Stupid" na goge sakonta, bayan wasu 'yan dakikoki sai ta sake aiko sako tana cewa "thank you" can sai ta kuma aikowa tace "sorry", a raina nace daman ana iya samun wadannan shedanun a yi Magana dasu.

Bayan wani lokaci a ranar ta sake aiko min da sakon ban-hakuri. Sai na yi mata Magana, ta gaishe ni, na sake yi mata Magana, da alama bata iya turanci sosai ba, sai naga ta fara yin Magana da larabci, haka muka yi Magana muka rabu. Bayan kwana biyu sai ta sake aiko min da sako a dai-dai lokacin da na sake bude shafin Inbox dina, ina ganin tace "Hi" ban-yi wata wata ba nace "very stupid" saboda ina zaton irin su ne suka aiko da sako, sai bayan da sakon ya tafi sai naga alamar munyi "conversation" ban lura da sunanta ba, abinda na fara cewa a raina, shi ne, yau dai na yi kwakyariya.

Bata damu ba sai ta aiko min da skon cewa tana da wata muhimmiyar Magana da ni, amma ga lambar wayarta na kirata. Sai na yi mamaki, na yi kasadar kiran wayar da layina, sai naji mace ta dauka, bayan munyi Magana mun gaisa sai tace, dan Allah akwai wani "event" muhimmi lallai tana son na halarta, a raina nace to wannan ta sanni ne daman kuma tasan inda nake har take gayyata ta. Ta yi min kwatancen wajen, sai naga nasan kusa da inda ta kwatanta min, amma kuma bangane ainihin inda za ai event din ba, bayan da muka gama waya sai na share.
 
Ranar Asabar tace min za'ai abin da karfe hudu na yamma. A lokacin da muka yi Magana, ta gayamin cewa idan naje wajen za'a tambayi sunana na gaya musu, sannan kuma za'a tambayi a dalilin wa na zo na fadi sunanta. Ranar Asabar ina zaune a daki tare da abokaina mu uku, sai ga wayarta da karfe hudu daidai, bayan na daga sai nace mata ai na manta yauce ranar, amma gani nan zuwa nan da minti 45, na baiwa abokaina labarin abinda ya gudana tsakani na da ita, suka ce "Lallai Yasir a gaisheka da kokari, haka kurum zaka dauki kafa kaje wajen da baka san dalilin kiranka ba . . ." Nace musu kudai idan kunji ni shiru to ga kwatancen da ta yi min kubi bahasina.

Nayi wanka na dauko wani tsohon Jeans da na jima ban sashi ba, na dauko wata riga mai dogon hannu na saka, na kawo hulata (tashi-kafiya-nace) na saka na kawo gilashina nasa saka, abokina ya kalleni yace, yau wacce rana Yasir ya sanya kananan kaya. Nace kudai ku yi adduah Allah ya sa alheri ne. Na hau mota tiryen-tiryen sai kusa da inda akaimin kwatance, da naje daidai wajen sai na samu wani mutum a zaune yana karanta jarida na tambayeshi ko nan ne waje kaza, sai yace eh, nace to kasan inda ake wani dan al'amari? Yace bai sani ba, muna haka sai ga Hala ta kirani, sai nace ga wani masanin wajen yi masa kwatance.

Bayan da na bashi waya suka yi Magana sai ta yi masa kwatance, yace ya gane, yace min ka hango wani dogon gini gashi can daga gabas, to hannun hagu da shi akwai wata karamar hanya, ka shiga nan ne wajen. Na kama hanya, ina 'yan kula-uzai . . . na isa daidai wajen kuwa, sai na d'an lab'e ina hango me ke faruwa a wajen, sai na hangi wasu mutane gabza-gabza su shida sanye da bakaken kaya sun tsuke sun sanya jan lakatayen, na dubesu nace ai kuwa duk cikinsu babu wanda ba zai iya makureni ba, har zan koma, sai nayi karfin hali.

Na dauki waya na bugawa Hala nace gani a wajen, tace na shiga wajen zasu tambayi sunana, za kuma su tambayeni a dalilin wa na zo na fadi sunanta. Na yi Shahada ina zuwa sai naga gabza-gabzan nan sun jeru a bakin kofa, bance musu komai ba na tsaya, sai wani ya yi min ishara zuwa ga wani mutum da yake zaune da takardu a gabanshi, ina zuwa wajensa yayi min fara'ah da alama mutumin ba yaro bane, ya tambayi sunana na gaya masa ya duba takarda sai gashi, yace a dalilin wa na zo, na fada masa ya duba sai ga sunanta, to a lokacin da nake tsaye ashe akwai wasu mutum biyu mce da namiji da suka zo bayana suka tsaya.

Kawai sai gani na yi ya musu ishara su tafi da ni, macen ta shiga gabana namijin ya tsaya a bayana suka ce muje, na bisu zugui-zugui muka hau wani bene, muna hawa amma ina hango mutanan waje ta cikin gilashi, suka kaini cikin wani daki, ina shiga sai naga an kunna fitulu marasa haske, ga kujeru anjera a dakin ga kuma wasu mutum 6 a bakin kofa ta cikin dakin ba ta waje bag a kuma wasu mutane zasu kai goma a zaune a wajen, suka nunamin wata kujera na zauna ina 'yan addu'o'in da suka zo min, can sai naji an saki disko mai karar gaske, nace To fah! Na dauko wayata na kira abokina, nace nifa gani an kawo wajen shedanci, abokina yace Allah ya kiyaye, nace Amin.

Ina zaune sai naga an kashe fitila, dakin yayi duhu amma kana ganin mutane wanda ka sani zaka iya shaida shi, ina 'yan addu'o'ina, sai na dauko wayata na kira wannan Hala din, sai tace min kar na damu kawai na zauna zamu hadu zuwa jimawa, ina zaune ina kallon mutanan da ke wajen, can sai naga an shigo da wani sai aka ce ya zauna kusa da ni, ai da na kalli gayen sai naga gaskiya wannan ya yi kama da Kiriminal, nan dai na fara tsoro amma dai na dake.

Ina zaune ina tunanin yadda zan gudu amma ina duba kofa naga kartinnan 6 suna tsaye jingine bakin kofa, sai nayi tsoron kar naje suce ba zan fita ba, ga dakin da duhu sai kawai hasken waya kake hangowa, can sai naga wani ya zo da projector zai hada. Naga gashi ana shigo da mata da maza wajen. . . . . . . . . . Zan katse labarin anan na baku labarin abinda ya faru shigen irin wannan a 2010, daga nan kuma sai na jona kuji yadda muka karke da su Hala Ebrahem. Sai mun hadu gobe idan Allah ya kaimu. Mu sha Ruwa lafiya.

YASIR RAMADAN GWALE
30-06-2014

No comments:

Post a Comment