Monday, July 21, 2014

RA'AYINA: Ziyarar Wasu Malamai Zuwa Fadar Shugaban Kasa Dan Yin Karin Kumallo

RA'AYI NA: ZIYARAR WASU MALAMAI ZUWA FADAR SHUGABAN KASA DAN YIN KARIN KUMALLO 
 
Ni kam banga wani abin cece kuce ba dan wasu Malamai sun je fadar Shugaban Kasa sun karya kumallo tare da shi a yayin da suka kai Azumi. Wannan ai ba wani abin bata lokaci bane, a matsayinsu na 'yan Najeriya suna da ikon amsa gayyatar karin kumallo idan Shugaban kasa ya gayyace su. Addinin Musulunci ai ba Addini ba ne da yake kyamar wanda ba Musulmi ba, Manzon Allah SAW ya karrama Abu Sufyan Sarkin Makkah a lokacin kuma shi ba Musulmi ba ne.

Ni fatan da nake yi ma ace sun yiwa Shugaban Wa'azi sun gaya masa Me Allah Yace, sun gaya masa irin nauyin hakkin Shugabanci da irin nauyin da yake kan Shugaban kasa na yiwa 'yan Najeriya Adalci a matsayinsa na Shugaban kasa. Allah ya sa sun karanta masa Al-Qur'ani ya saurara, na yi Imani Shugaban ba'a taba zama kusa da shi an karanta masa ayoyin Al-Qur;ani ba. Ai a Africa an taba yin wani Shugaban Kasa da Ya Musulunta yana kan Mulki, idan aka yi sa'a ai sai Shugaban ya tuba yabi Allah.

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mohamma har masallacin Idi yake zuwa dan taya Musulmi murnar Sallah, duk da shi a Zaune yake baya yin Sallar sannan kuma idan ya koma gida ya yanka rago. Ko babu komai ai ya nunawa Musulmin kasar cewa shi Shugaban Kasar ne baki daya ba na wasu mutane kawai ba.

Yanzu idan Malamai basa kusantar masu Mulki suna gaya musu gaskiya suna yi musu wa'azi, shin su Doyin Okupe ko Ruben Abati muke tunanin zasu dinga yiwa Shugaban kasar Wa'azi? Ai ni babban Buri na ma shi ne Kungiyar Izala ta shirya gagarumin Wa'azin Kasa a sake gayyatar Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan a samu Alaramma Yahuza Bauchi ko Alaramma Ahmad Sulaiman sun dinga rera karatun Al-qur'ani Shugaban yana ji da kunnensa.

Dan haka ina kira ga duk wani Malami ko Alaramma da ya samu gayyata zuwa fadar shugaban kasa dan su karya kumallo to ya amsa wannan gayyata, kuma ya yi kokari ya yiwa Shugaban kasa wa'azi ya karanta masa alkur'ani ya saurara. Jama'a kuma ya kamata a daina aibata Malamai dan sun amsa gayyatar Shugaban kasa. Ai mu 'yan Najeriya ne, Goodlock kuma shi ne shugaban kasa ko muna so ko bama so, ko mun ki ko mun so babu yadda muka iya shi ne dai Shugaban kasa.

Yanzu jama'a shi kenan sai mu hadu mu duka mu nade hannu, mu ce ba za'a yi gwamnati da mu ba sai lokacin da namu ya samu? To idan namu bai samu ba shi kenan sai mu yi ta zama a haka? Ku su mutanan kudu kame hannu sukai lokacin da namu suna Mulki suka ce babu ruwansu sai lokacin da nasu ya samu? Allah ka shiryi Shugaban kasar Najeriya Alfarmar wadannan kwanaki, Allah ka sanya Imani da tsoronka a cikin zuciyarsa, Allah ka sa ya fahimci irin girman hakkin da yake kansa na jagoranci. Allah kai ne mai juya zukata Allah ka juyo da zukatansa zuwa ga aikata daidai. Mu kuma mabiya Allah ka kara mana juriya da hakuri kuma ka bamu ladan hakuri. Allah ka nuna mana gaskiya a duk inda take ka bamu ikon aiki da ita, ka nuna mana karya ka bamu ikon kauce mata.

YASIR RAMADAN GWALE
21-07-2014


No comments:

Post a Comment