Wednesday, July 23, 2014

PALASTINE: Tun Ina Yaro Karami

PALASTINE: TUN INA YARO KARAMI

Tunda na tashi na fara wayo nake jin sunaye irinsu Madeline Olbright, Ahmed Yassin, Yassir Arafat, George H.W Bush, Bill Clinton, Shimon Firez, Yitzhak Rabbil, Ariel Sharron, Hosny Mubarack da sunayan gurare irinsu Camp David, Geneva, Oslo, New York, Whitehouse, Pentagon, Sham-el-Sheikh . . . Daga nan na fara fahimtar batun tattaunawa tsakanin Israela da Palastine, ina iya tunawa tun Gemun Malam Yassir Arafat bai yi fari fat nake ganinsa a kusa da Bill Clinton da Shimon Firez ana daukarsu hotuna a Camp David ana ta turanci, ina iya tuna lokacin da idan an nuno wata dattijuwa tana sanye da jan baki gashinta ruwan zuma a gaban lasifikoki da yawa tana turanci naji a gida ana cewa wannan dai shedaniyar mata ce, har na saba da ganin hotonta a TV na fahimci sunanta Madeline Olbright, har na fahimci ita ce sakatariyar harkokin wajen Amerika.

Tafi tafi na saba da jin labarin irin tattaunawar da ake yi a gidan shakatawar Shugaban kasar Amerika na Camp David, da Sham-el-Sheikh a Masar, idona ya saba da ganin wani dattijo da ake turawa a kan kujera yana zaune da farin hirami akansa da dogon gemunsa, mutane suna ta zuwa suna sumbatar hannunsa da kumatunsa ashe shi ne Shugaban Hamas Sheikh Ahmad Yassin Allah ya jikansa.

Tun a wancan lokaci idan na tashi da safe nakan ga mahaifina yana jin BBC ko VOA ana labarin tattaunawa a Geneva ko a Sham-el-Sheikh a lokacin nake sauraron su Sale Halliru su Isa Jikamshi suna bada labarin fadace-fadace da ake yi a kasashen Larabawa musamman Palastine,

A lokacin da gidan talabijin na Al-Jazeera na larabci ya fara watsa shirye shiryensa na fara jin kalmomi irinsu INTIFADA ina ganin wani mutum da lasifika a hannu yana larabci idan ya gama yace Akram Khuzam Al-Jazeerah Moscow nake jin irinsu Tayseer Alluni suna ta bayani yadda ake ta yin gaganiya a duniya.

Tun a wancan lokacin da na saba da jin labarin abinda ke faruwa a Palasdinu na san sunan Ghazza da Ramallah da Hizbullah da Fatah da Hamas da Jihadil Islami. Har yanzu haka ina jin wannan labari kuma akan matsala kwaya daya da na tashi naji ana ta batunta a ko da yaushe ita ce dai har yanzu ake tattaunawa, wanda a ganina duk wasu maganganu da ya kamata a fada tuntuni anyisu a baya.

Har ta kawo gashi yanzu da na kakkaranta tarihi da dama akan abinda ya faffaru a baya ba ni da wayo, har na zama ina da masaniyar irin wainar da ake toyawa a gabas ta tsakiya kuma zan bibiyi abinda yake faruwa a Ghazza na yi sharhinsa. Duniya Makaranta ce mai cike da dumbin ilimi! Lallai al'ummar Palastine sun jima suna cikin ukubar Israela. Allah ka yaye musu wannan masifa da bala'i.

YASIR RAMADAN GWALE
23-07-2014


No comments:

Post a Comment