Monday, July 7, 2014

Labarin Da Ya Tayar Min Da Hankali A Cikin Azumin Nan

LABARIN DA YA TAYAR MIN DA HANKALI A CIKIN AZUMIN NAN

Furera Bagel ta bayar da wannan labari akan Timeline dinta kamar haka: Tana cewa, ina cikin matukar damuwa da tashin hankalin abinda ya faru, inda har na dinga ganin abin a mafarki. Tace, wani lokaci na ziyarci gidan yayata dan sada zumunci, sai na sameta cikin wani irin yanayi marar dad'I kwarai da gaske. Da na tambayeta dalilin halin da ta ke ciki, ta bani labarin kamar haka:

Wannan abin ya faru da wata 'yar uwarmu ne, wannan matar tana cikin wani irin matsananci halin rayuwa, daga baya kuma wani mummunan al'amari ya kuma bijiro musu. Ita dai wannan matar sunyi aure da mijinta Shekaru 25 da suka gabata, wanda tun bayan aurenta da mijinta aka kama mata dakin haya guda daya tana cikinsa tsawon kusan shekaru 20; kwatsam bayan wani lokaci sai mijin matar ya kara yin wani sabon aure, anan ne mijin ya kara karbar wani dakin haya guda daya a gidan da yake zaune, inda kowaccensu take zaune a daki daya.

Amma wannan mutumin bai kama daki ko guda daya ba, domin 'ya 'yansa da suka tasa su zauna a ciki ba! Matar takan kwana da 'ya 'yanta budurwoyi a daki daya idan mijinta na dakin daya matar, amma yaranta maza sai su tafi makwabta su kwana tare da sauran 'yan uwansu maza. Can bayan wani lokaci, dan wannan mata mai kimanin shekaru 12 ya kamu da rashin lafiya, inda aka kaishi asibiti dan yi masa magani. Amma bayan wani lokaci rashin lafiyar wannan yaro ta sake tasowa, anan ne suka yanke shawarar daukar yaron dan kaishi a yi masa gwaje-gwaje dan gane cutar da take damunsa.

Bayan da aka dauki jinin yaron dan skekaru 12 aka auna ne, aka tabbatar musu da cewa yaron yana dauke da cutar HIV mai karyar garkuwar jiki. Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un! Uwar yaron ta shiga cikin damuwa da tashin hankalin yadda yaro kankani ya kamu da cutar kanjamau irin wannan!

Tun farko, matar bata taba samun nutsuwar danta yaje gidan makwabta ya kwana da wadan da suka grime shi a shekaru ba, amma kasancewar mijinta yaki kamawa yaransa dakin haya a gidan, babu wani abu da zata iya yi illa ta kyale yaron yaje makwabta ya kwana duk dare, amma daga wannan lokacin matar ta kudiri aniyar dole al'amura su sauya daga yadda suke faruwa. Nan ne fa matar ta kuduri aniyar samarwa kanta da 'ya 'yanta mafita, ta fara yin sana'ar toye-toye a bakin titi duk safiya, ta sanyawa ranta burin mallakar gida dan tsugunar da 'ya 'yanta.

Allah buwayi gagara misali, ya baiwa wannan mata ikon mallakar fili, cikin hukuntawarsa Subhanahu Wata'Ala, ta gina gida mai daki biyu da falo da kicin da ban-daki da tsakar gida. Amma a lokacin da ta mallaki wannan gidan tuni 'ya 'yanta mata guda biyu sunyi aure, kun san abinda mijinta yayi kuwa? Kawai sai ya saki waccan matar da ya kara aurowa daga baya, sannan yabi matarsa sabon gidan da ta gina ya tare tare da ita.

Dan wannan matar da yake yaro ne mai shekaru 12, yana nan yana cigaba da karbar shawarwari da magunguna akan cutar da yake dauke da ita mai karya gaekiuwar jiki, adaidai wannan lokaci ne kuma, ciwon yaron ya sake tsananta, dukkan karfin jikinsa ya kare, garkuwar jikinsa tayi matukar rauni. A lokacin da yayar Furare Bagel ta ziyarci mahaifiyar yaron ne ya yi musu bayanin yadda aka yi ya kamu da cutar HIV! Yaron yace, "lokacin da nake zuwa gidan makwabta na kwana ina karami sosai, idan ina kwance sai wani mutum ya zo ya tilasta min kwanciya tare da shi dan biyan bukatar sha'awarsa tare dani, yakan yi min ta karfi ba dan ina so ba, mutumin ya ciga da zuwa wajena duk dare yana tursasamin kwanciya da shi lokaci mai tsawo da ya wuce. Mutumin da yake yi min wannan abu kuwa shi ne makwabcinmu da nake kwana a gidansa, yaron yace mutumin kamar mahaifi yake a wajensa"! Wannan shi ne labarin da yaron ya basu, inda ya nuna cewar wannan mutumin da yake zuwa wajensa da daddare yana kwana da shi ne ya sanya masa wannan cuta ta HIV.

Hakika wannan labari ya tayar min da hankali a cikin wannan azumi matuka. Furare Bagel a cikin jawabinta ta ce, shin me yasa ba zamu taimakawa wannan mata ba wajen kama wannan makwabcin nasu dan gurfanar da shi a kotu a tuhumeshi da laifin yin lalata da kananan yara ba? Ina lauyoyi daga cikinmu masu san taimakon masu karamin karfi? Lallai ya kamata mu taimakawa wannan mata da aka riga aka kashe mata yaro.

YASIR RAMADAN GWALE
07-07-2014

No comments:

Post a Comment