Tuesday, July 1, 2014

Abinda Ya Faru Da Ni A 2010

ABINDA YA FARU DA NI A 2010

Ranar wata juma'a na yi wanka na tafi masallacin Al-Furqan misalin karfe goma na safe, bayan da na isa masallaci na yi alwala zan shiga Masallaci ina goge ruwa a fuskata, sai ga waya ta na ruri, ko da na duba sai naga wani abokina ne ya kirani, na d'aga muka gaisa, yace Yasir kana ina? Na ce masa ina masallaci yanzu haka, sai yace, to Dan Allah kayi maza-maza ka hau mota ka zo Abuja yanzu-yanzu. Sai naji garam! Yace karka damu ka hau mota yanzu dan ka iso da wuri.

Banyi wata-wata ba na koma gida na shirya jakata na dauki katin ATM na yi Sallama da gida na tafi. Na kama hanya sai Dangi randabawul nan na samu mota na hau, muka dan bata lokaci kafin mu tashi, zoooo muka kama hanya, mun sami Sallah Juma'a a hanya ina zatan kusa da Zariya. Bayan nan muka kama hanya muna tafiya zummm muna tafiya, mun isa Abuja bayan Sallar Isha, na bugawa Abokina waya nace masa gani na zo Abuja.

Daga nan yace naje Area 11 wajen masallacin Juma'a na jirashi, na dauki mota kuwa sai Ministers gate. Ina tsaye sai ga shi an tukoshi a 406 mai launin koriya, yace na hau, na bude kofa na shiga, daga nan Muka shiga cikin unguwar Maitama wajen Masallacin Juma'a na Maitama. Muka je gidan wani Alhaji dan kano ne mutumin kirki kwarai da gaske, muna shiga muka sameshi yana kallon NTA a wani katafaren falo, yana kishingide a jikin wani tuntu na fata, ya nuna mana kan tebur, abokina yace Yasir bisimillah kaci abinci, na duba teburinnan cike yake makil da kayan dadi, ga kaji ga kifi ga apple ga soyayyar doya ga abubuwa kala-kala har da alale irin mai kwai a cikinnan.

Bayan da naci na gyatse, na sha ruwa da lemuka iri-iri har da Shuwefs. Sai naga duk mutanan dake falon a zaune suke a kan kafet nima na zauna a kasa, maigidan sanye da farar jallabiya da bakar hula ya mikomin hannu muka gaisa, daga nan ya nuna min wani fulas dogo yace ga kofi can dauko, da na dauko na zuba sai naga kunun tsamiya ne mai rai da lafiya, na tsiyaya na kukkurba. Haka dai na cika cikina taf har da kyar nake nishi, abinku da wanda yaga banza! Lol

Muna zaune sai abokin nawa sukai waya yace gashi nan zuwa. Muka hau mota muka tafi wani gida anan dai unguwar maitama ne, muna isa naga gidan dan'karere mai gadi ya fito ya bude mana kofa, muka shiga sai na duba ashe akwai jar miya a jikin farar shadda ta, muka tarar da wasu mutum hudu, daya daga cikinsu dan kano ne wani dan siyasa ne, na shanshi shima ya sanni, yana zaune akan kujera yana daddanna waya muka gaisa da shi sunansa Musa Gwadabe, gefe kuma wasu manyan mutane ne su biyu suke hira, daga jikin bango kuma ga wani mutum ba tsoho bane sosai sanye da fararan kaya da hularsa a karkace irin yadda muke ganin hotunan Alh. Isah Kaita ke karkata hula mutumin yana karatun al-qur'ani.

Muka samu waje muka zauna, da mutumin ya gama karatun Qurani sai naga mutum biyun nan dake gefe sun juyo wajensa sai na fahimci shi ne mai gidan. Bayan da suka gaisa ya kira wani daga cikin masu gadi nan da nan aka kawo wani katon daron abinci, akwai tuwon semo da teba a ciki sannan ga miyar bushashshiyar kubewa da kaji zukul-zukul a ciki ga kuma wata irin miyar ganye ina jin ko Edikong Ekong ce, nace ni kam na koshi amma dai zan danci kazar, suka bushe da dariya. Nace ai mu a Kano bama yin miyar yauki da Kaza.
Bayan da aka gama cin abinci sai ruwa ya sakko shaaa, muna zaune, sai abokina ya matsa kusa da mutumi yace masa Ranka Ya dade wannan shi ne Yasir Ramadan Gwale, mutumin ya miko min hannu muka gaisa na sanya hannu biyu muka gaisa.

Da muka gama gaisawa sai yace kasanni? Nace Ranka ya dade ban sanka ba, amma tunda na zo nan dole zan sanka. Yace sunana Sani Zangon Daura, sai Musa Gwadabe yace bakasan Danmasanin Daura ba? Nayi masa mujamala nace kwarai kuwa, daga nan mukai Sallama abinda zai gudana ya gudana aka kaini masauki . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . .!

ABINDA YA FARU DA NI RANAR ASABAR A FACEBOOK [2]

Sai kuma mu dawo labarin abinda ya wakana tsakanina da Hala Ebrahem. Ina zaune ina ta tararrabin yadda zan fita daga dakinnan sai naga an had'a projector an kunna, aka kuma kunna wasu fitulu ba masu haske sosai ba, can sai ga wani mutum ya zo da kyamara ya yana daukar hotuna, sai naji tsoron kar yazo kaina ya dauki hotona ban san ina hoton za shi ba, da naga ya kusa zuwa kaina sai nayi dabara na kara wayata a kunnena na sunkuyar da kai kamar ina waya, har sai da na fahimci ya wuce sannan na d'ago.

Baifi minti goma ba, sai naga wani mutum yazo ya dauki abin Magana ya gaishemu ya yi mana barka da zuwa sannan yace RAMADAN KAREEM daga nan na dan samu nutsuwa nace watakila ba mugwaye bane. Ya ajiye abin Magana ya tafi, can sai ga wata budurwa sanye da bakaken kaya da jan kallabi itama ta dauki abin Magana ta danyi surutanta, amma ni hankalina duk ba kanta yake ba, ina ta sakar yadda zan gudu.

Ilai kuwa sai naga wata ta tashi tayi bakin kofa inda gabza-gabzan mutanan suke, ta yi musu Magana suka bata hanya. Nima na tashi a tsure na nufi kofa, sai nace musu zanje waje na dawo, suka bude kofa kuwa, nan naji wata iska ta shigeni me sanyi. Na sauko daga kan bene, na tarar da ragowar shidannan na bakin kofa suma nace zanje na dawo suka bani hanya na wuce.

Da yake lokacin da na fito magriba tayi sai naje wani masallaci dake kusa da wajen nayi Sallah, na ja gefe na tsaya ina tunanin irin yadda nayi kasada haka kurum ban san mutumba ya kirani kuma na zo, nan dai na hakkake cewa koma dai me ya faru kaddara ce da babu wanda zai iya tsallake mata. Ina zaune ina tunanin abinda ya faru, sai ga Hala ta kirani tace ina nake, nace mata na zo wani Masallaci zanyi Sallah, tace idan nayi Sallah na kirata, na zauna na huta, da na koma kusa da wajen sai naga mutane suna fitowa, sai na kira Hala tace min naje wajen da ake shiga kofa zan ganta da Koren Gyale da Bakar riga.

Sai na koma can baya dan in hangota naga wacece, inda tace na duba banga alamar da ta nunamin ba. Sai na kuma dauko waya zan kira, ina kira sai batirina ya mutu, nan na sake kunna wayar na dauki lambarta ko zan samu wani ya kirata, ina tsaye sai naga wannan da nace muku Naga yayi kama da Kiriminal yazo wajena yace na biyoshi, na bishi banyi fargaba ba, sai ya hadani da wata siririyar yarinya, ta miko min hannu mu gaisa, sai na saka hannuna a al-jihu na gyada mata kai, ta dauki wayarta naji ta kira Hala tace mata gani ga Yasir, sai ta nunamin wasu mutane a tsaye bakin wasu fulawoyi tace naje wajensu, daga wajen ina hango bakin titi nasan ko ihu na yi zan samu agaji.

Ina zuwa sai naga samari ne guda uku da wani mutum ya dan manyanta, da kuma wata mata sai wasu 'yan mata su biyu sun kewaye wata a tsakiya, kuma budurwar nance mai bakaken kaya da jan dankwali take yi musu jawabi. Ina tsaye ina duban hanya ko da zanga dugu-dugu zan iya arcewa, ahaka matarnan ta dinga Magana da su daya bayan daya suna tafiya har sai da kowa ya waste daga ni sai ita sai kuma siririyar yarinyar da ta rakoni.

Matar tace min ina da tambaya? Nace babu, tace me ya sa, nace haka kurum, tace to ni zan iya tambayarka? Nace mata a'a, sai tayi dariya tace ai ba tambayar jarabawa zan yi maka ba, nace eh duk da haka ba sai kin tambayeni ba, tace to ita tana da tambaya, sai nace to da sharadin idan zaki yi tambayar da turanci. Tace ba komai, daga nan ta fara yimin wasu surutai wai suna da kamfani da zan iya saka kudi naci riba cikin kankanin lokaci, tace idan na saka Dala dubu biyu a cikin kwana 8 zanci ribar Dala Dubu Goma, tace min akwai wanda yaci ribar Dala Dubu Talatin a cikin sati uku, nan dai na fahimci ashe abin Damfara ce.

Da ta gama jawabi sai nace bani business card dinki sai ta fara inda-inda, nace a ina kamfanin naku yake, sai tace zan karbi lambarka duk lokacin da ka shirya sanya kudinka kayi min Magana, ni kuma zan zo na sameka! A raina nace yanzu ke kinga nayi kama da wanda za'aiwa irin wannan zancen banzan, ai san banza na baikai haka ba.

Haka dai muka rabu ina ta ta'ajibin abinda ya faru. Amma kuma har na baro wajen banga Hala Ebrahem ba. Kunji karhsen abinda ya faru. Babu bukatar na rantse dan wasu su yarda da ni Amma Wallahi yadda na gaya muku haka abin ya faru. 'Yan damfarar da suke aiko mana da sakwanni ta Inbox na hadu da su ido da ido. Amma abinda na fahimta masu aiko da sakwannin nan mutane watakila da suka sanka.

YASIR RAMADAN GWALE
01-07-2014

No comments:

Post a Comment