Friday, October 4, 2013

Su Wa Ye Asirinsu Bai Tonu Ba?



SU WAYE ASIRINSU BAI TONU BA?

Sau da yawa 'yan Najeriya muna yin addu'ar ALLAH ya tona asirin miyagu azzalumai, batagari, mahara, masu kisa, barayi, masu cin hanci, masu garkuwa da mutane da sauransu. Ko shakka babu wannan addu'ah da 'yan Najeriya suka jima suna yi ALLAH ya karba, ya kuma amsa, ya tona asirin duk wanda aka nemi asirinsa ya tonu. Abin tambayar anan shi ne idan asirin miyagu ya tonu sai me kuma? Shin akwai wasu barayi a Najeriya manya da kanana da ba'a sansu ba? Shin ba ALLAH ne ya tona musu asiri ba? Akwai wasu masu kisan mutane da ALLAH bai toni asirinsu bane? Barayi da kansu suka dinga kafa kwamitoci suna cewa a binciko barayi kuma binciken yayi tafiyar ruwa har da wadan da suka kafa su. Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan da kansa yace yasan duk barayin man fetur, shin ba ALLAH bane ya tonawa shugaban kasa asiri ya yi wannan furuci? Shugaban ya taba fada cewa a cikin gwamnatinsa akwai 'yan Boko Haram, Marigayi tsohon mashawarcin kasa na tsaro Gen. Azazi da kansa yace PDP sune Boko Haram, shi ne masanin dukkan wasu rahotannin tsaro na sirri, shin ba ALLAH bane ya tona masa asiri ya yi wannan furucin ba? Yanzu su waye suka rage Asirinsu bai tanu ba? Duk inda ake saida giya da masu shan giyar an sansu, ansan masu yin zina da Luwadi da Madigo da dukkan ayyukan badala ansan su, suma mau aikatawar sun san angane su, amma saboda an san duk ba gaskiya garemu ba, shi yasa babu wanda yake jin kunyar aikata ba daidai ba! Ina ganin ya kamata mu sauya salon addu'armu mu koma cewa ALLAH YA BAMU IKON HUKUNTA WADANNAN GUNGU NA AZZALUMAI, domin tuni ALLAH ya gama tona musu asiri, ya rage namu kawai mu dauki mataki, indai kuma ba Mala'iku muke jiran a aiko su yi musu hukunci tun anan duniya ba.

A karshen shekarar 2011 aka kama wata mata Lucy Danaga Kirista ta yo safarar makamai a cikin buhunhunan hatsi zuwa jihar ADAMAWA, ALLAH ya toni asirinta aka kamata, shin me aka yi tun daga wancan lokaci zuwa yanzu? An kama wasu batagari kiristoci su takwas a kauyen MIYA BARKATE a jihar Bauchi da yunkurin tayar da Boma-bomai a coci, shin me aka yi tun a wancan lokaci zuwa yanzu? A jihar Bayelsa an kama wani Kirista da shiga irin ta Musulmi ya yi yunkurin tayar da Bom a coci, shin me aka yi masa? A jihar Fulato an kama kwanturola na kwastan da yin safarar makamai zuwa ga 'yan kabilar Berom, shin me aka yi masa? A dai jihar Fulaton kuma aka kama wani kirista wanda ya tayar da Bom a COCIN CHURCH wanda dukkan bayanai suka tabbatar da cewa cocin da ya kai hari anan yake zuwa yin ibada, shin me ya faru?

Idan muka koma batun cin hanci da rashawa mutum nawa EFCC ta kama da laifin satar dukiyar jama'a? Ina Saminu Turaki da ya saci Biliyan 38? Ina Gwamna Alams na Bayelsa, da Gwamna Locky Igbenedion na Edo, da Danjuma Goje na Gombe, da Aliyu Akwe Doma na Nassarawa da sauran tsaffin gwamnoni da dama shin ALLAH bai tona musu asiri ba? Abin mamaki Kotu a England ta yiwa tsohon Gwamnan Delta James Ibori hukunci saboda ya yiwa 'yan Najeriya sata ba 'yan Burtaniya ba! Shin babban bankin Najeriya bai bankado badakalar bankuna da dukiyar jama’a ba? Ina batun badakalar Halliburtun, da Baswani Brothers, da Siemens, da Fanshon 'yan Sanda? Duk wadannan ALLAH bai tona musu asiri ba, uwa uba ina batun mutanan da rahoton Hon Farouk Lawan ya bankado da ci da gumin talaka na kusan Naira Tiriliyan daya, Ina batun rahoton kwamtinin Nuhu Ribadu da aka bankado sama da fadi ta kusan Tiriliyan biyu? Duk wadannan ba ALLAH bane ya tona musu asiri?

Amma saboda kasar ba gaskiya ake ba, Shugabanni marasa gaskiya, talakawa da sauran mabiya duk marasa gaskiya, shi ya sa bamu san wani abu darasi daga rayuwar baya ba. Duk wasu abubuwa da suka kamata a dauki darasi akansu babu wanda bai faru ba, amma babu wani darasi da ake dauka, kai kace makafi da kurame ne al’ummar da ake zalunta a Najeriya. Mun gani a kasar Burtaniya saboda mutanan gaskiya ne, rayuwar gaskiya ake yi Tony Blair bai kai karshen wa’adin mulkinsa bay a sauka, Gordon Brown shima bai tumma wa’adinsa bay a san inda dare ya yi masa, saboda me, saboda sun aikata ba daidai ba; Sulvio Baluskoni a Italiya shi mai bai karasa wa’adinsa ba, har kotu yaje duk saboda al’ummarsu da gaske suke, dan haka babu yadda Nanun zata cisu alhali basu ci ba.

A ganina ALLAH ya riga ya gama karbar addu'ar 'yan Najeriya da suke neman ya tonawa dukkan batagarin al'umma asiri. Yanzu kawai abinda ya rage shi ne wane shiri al'ummar Najeriya suka yi na tunkarar wadan da ALLAH ya bankada asirinsu, ko kuwa shi kenan idan asirin mutum ya tonu ya wadatar? Yanzu muna cikin halin ga Barawo kuma Ga Mai Kaya ne! Amma barawon yasan mai kayan mutumin banza ne babu abinda zai iya yi masa, shima mai kayan yasan ba da gaske yake ba, dan haka barayi da miyagu suke watayawarsu yadda suka ga dama, suna yake hakora a wajen taruka kamar ba su aikata komai ba. Yanzu me ne ya rage mana? Duk masu dibga mana sata mun sansu, duk masu tayar da Boma Bomai mun sansu, duk masu yin garkuwa da mutane mun sansu. Me kuma ya rage? Dukkan wata mafita da makoma sahihiya da mu 'yan Najeriya wadan da aka zalunta aka sace mana dukiya, aka kashe mana 'yan uwa, mafitar tana hannunmu, wadan da suke Ikirarin sune Shugabanninmu babu wani abu da zasu iya yi, domin kodai daman suna daga cikin wadan da ALLAH ya tonawa Asiri, ko kuma Ansata ambasu ladan ganin Ido, ko kuma suna gani ana satar suka kawar da kai.

Idan da dagaske hukumomi suke son gyara tabbas da anyi. Dukkan wani abu day a kamata a fada dangane da gyaran kasarnan anfadeshi, duk wani rubutu day a kamata a yi anyishi, kusan duk wani abu da za’ayi maimaitawa kawai ake yi, barayi ne kawai ke samun cigaba daga satar Miliyan zuwa Bilyan har zuwa Tiriliyan. Ina kwamitocin da aka kakkafa, ina rahotannin da suka bayar? Ina kwamitin Justice Uwais, da Kwamitin Alfa Balgore, da Kwamitin Shehu Lemu, da Kwamitin Giltimari da sauran kwamitoci da aka kakkafa domin bayar da shawarar yadda za’a kyautata lamura, duk sunyi rubutu sun bada dukkan irin shawarwarin da ake bukata da kuma mafita, amma ina suka shiga? Muna tsammanin wadannan gungu na miyagu azzalumai ne zasu kawowa rayuwarmu sauyi?

A lokacin da aka nada Attahiru Jega a matsayin sabon shugaban hukumar zaben, Gidan Mumbayya House sun shirya wata tattaunawa mai suna “Path way to the credible election” Farfesa Alkassim Abba na Jama’ar jhar Adamawa day a gabatar da kasida, ya yi bayanin duk irin yadda lamura suka tabarbare, bana mantawa wani dalibin jami’ah ya yi tambayar MECECE MAFITAR HALIN DA MUKE CIKI! A lokacin Farfesan ya bashi amsa da cewa mafita tana hannunka da kai da sauran abokanka, da dama mun dauka cewa baker Magana ya fada masa. Amma yanzu tabbas n agama gamsuwa cewa mafitar duk wannan halin da muke ciki tana hannunmu. Yanzu zabi ya rage ni da kai da sauran al'ummah wadan da aka zalunta, mu takawa abin burki. Domin duk wadannan masu aikata laifukan ba za su daina ba, kuma ba za su taba jin kunya ba, domin waliyyan Shaidan ne, shi yake yi musu wasiyya da aikata laifuka, tunda suka kafurcewa ALLAH dole su yiwa shaidan biyayya. Abu ne a bayyane amma wa ye ya isa ya ce UWAR SARKI MAYYA CE! Shi ne inda gizo ke sakar. ALLAH ka bamu ikon daukar mataki akan Azzalumai miyagu wadan da suka cuce mu.

Yasir Ramadan Gwale
04-10-2013

No comments:

Post a Comment