Tuesday, October 8, 2013

Dan Giya


DAN GIYA: Ina zaune naji wasu mutane suna labarin cewar duk dan giya ya fi kowa dacewa da samun matar aure ta kirki. Suka ce zaka samu mafiya yawancin 'yan giya, idan sun sha sun bugu su yi ta yiwa matansu amai suna zazzaginsu amma matan na hakuri, kuma suna nuna soyayya a garesu. Wannan maganar ta shiga kunnena sosai.

Wannan ya tuna min da wata waka da wani mawaki ya raira mai suna ZAMA NA AURE, inda yake cewa "Zama na aure yana da dadi yana da daci . . ." Mawakin ya bayar da wasu labarai guda hudu a cikin wakar tasa, a labari na uku daya bayar ya yi kama da abin da naji wadannan mutanan suna tattaunawa akan dan giya. Ga abinda wakar ta ke cewa:

Zama na Aure Yana da dadi yana da daci maĆ”urata ashe soyayya da dadi…

Shi ko Gambo kunga dan giya ne

Sai can dare zai dawo gida nai

Da rangaji zai shigo gida nai

Ta kasa barci matarsa zaune

Bugu na kofarsa ma dabanne

Ta je ta bude ya yi shigowa

Da ya shigo zai fara hararwa

Ruwa ta debo tai tsabtacewa

Yana ta zaginta da dadawa

Ita ko kwalla take zubarwa

Kullum nasiha take gare shi

Dan ilimi gunta kwai yawan shi

Dan ilimin addini akwai shi

Sannu a sannu a kwan-a-tashi

Ya nutstsu tsaf-tsaf idan ka ganshi

Ya daina shaye ya canza halinshi

Gambo ai soyayya da dadi…..

Wannan labarin shakka babu ya yi kama da abinda naji wadannan mutane suna tattaunawa. Haka kuma, akwai wani mutum da na sani shi da kansa ya bani labari cewar a lokacin da yake shan giya, matarsa har wanka take yi masa, ya zageta ya fasa mata kaya amma bata damuwa, tana nuna masa soyayya tana masa Wa'azi da Nasiha. AMMA ME YA SA 'YAN GIYA SUKE DACEWA DA MATAN KIRKI?

No comments:

Post a Comment