Thursday, October 17, 2013

Wa Ye Masoyin Manzon Allah SAW?


WAYE MASOYIN MANZON ALLAH?

Kaunar Manzon Allah SAW shi ne yi masa cikakkiyar da'a da biyayya ba tare da tuhuma ko titsiye akan duk abinda ya zo da shi ba Salallahu Alaihi Wasallam. Sahabban Manzon Allah SAW su ne manyan abokansa, Almajiransa, Aminansa, Majibintansa masu kaunarsa SAW kauna ta hakika, sun yi masa cikakkiyar biyayya irin biyayyar da babu wani mahaluki da ake yiwa ita a fadin duniyar nan. Bisa tsarin addinin Musulunci na ADALCI da kyautata zato, baka taba ji a tsakanin Sahabbai an kira wani da sunan cewar shi ne "MASOYIN MANZON ALLAH BA" ko shakka babu ana kyautata zaton cewar duk wani Musulmi ya fifita soyayyar Manzon Allah SAW akan kansa, balle wani mahaluki.

A dazu da rana muka samu labarin rasuwar wani Mawaki a cikin Birnin Kano da ake cewa yana wakokin yabon Annabi SAW. Wannan mawaki yana wakokin yabon Annabi ne da kida da busa sarewa da jita da sauran kayan kide-kide wadan da suka sabawa koyarwar Manzon Allah SAW, wanda yin hakan sabawa hakikanin koyarwar Manzon Allah SAW ne, muna yi masa uzurin watakila ya aikata hakan bisa rashin sani. Allah ya yafe masa kurakuransa.

Abinda ya biyo bayan rasuwar wannan bawan Allah shi ne, irin yadda muka ji ko muka ga wasu na daukaka shi da sunan cewa "MASOYIN MANZON ALLAH" shin akwai wani Musulmi na hakika da ba masoyin Manzon Allah bane? Masu yin wannan kiran shin suna nufin cewar shi wannan mawaki ya fi su kaunar Manzon Allah ne? Idan ka ce wane Masoyin Manzon Allah ne, to kamar kana cewar duk wanda ba shi ba to ba masoyin Manzon Allah bane. Haka idan ka ce Musulmi sune masoyan Manzon Allah, dan haka duk wani wanda ba Musulmi ba to ba masoyin Manzon Allah bane, wannan babu wanda zai zarge ka da yin kuskure.

Akwai wani marubuci bature Kirista, wanda ya rubuta wani littafi mai suna FITATTUN MUTANE 100 a duniya, a cikin mutum dari da ya zana, Manzon Allah SAW shi ne na farkonsu, ya kuma yi kalamai na yabo sosai akan Manzon Allah SAW, Shi kenan wannan sai ya bayu a garemu cewar wannan marubuci masoyin Manzon Allah ne, alhali bai yi imani da addinin da Manzon Allah ya zo da shi ba. Lallai soyayyar Manzon Allah SAW ba furta kalamai ko rera waka bane, soyayyar da zaka yiwa Manzon Allah ta amfaneka a Lahira ita ce yi masa cikakkiyar da'a da biyayya da Sallalamawa dukkan koyarwarsa da ta sahabbansa shi ne abina zai tsiratar da mutum a ranar gobe kiyama. Allah ya yi dadin tsira a gareshi Salallahu Alaihi Wasallam da Alayensa da Sahabbansa da wadan da suka bi tafarkinsu da kyautatawa har ya zuwa ranar sakamako.

Allah ka jikan Musulmi, wadan da suke kwance marasa lafiya gida da asibita Allah ya basu lafiya.

Yasir Ramadan Gwale
17-10-13

No comments:

Post a Comment