Thursday, October 10, 2013

Wanne Ne Maganin Musulunci Wanne Na Kafurci?

WANNE NE MAGANIN MUSLUNCI WANNE NA KAFURCI?

Allah SWA bai halicci wata cuta ba face sai da ya halicci maganinta kamar yadda Malamai suka gaya mana. Manzon Allah SWA da kansa ya yi bayanin wasu cututtuka kuma ya yi bayanin maganinsu, haka kuma, Manzon Allah ya bayar da wasu addu'o'i a matsayin garkuwa ta musamman ga wasu cututtuka. Cuta ma'anarta tana da fadi, rashin lafiyar jiki cutane, rashin lafiyar Imani ma cutane, shafar aljanu da dangoginsa duk cutane, dan haka duk wadannan cututtuka babu wata cuta da aka ce ta Musulunci ce ko ta kafurci, kamar yadda Musulmi zai iya kamuwa da kowacce irin cuta haka ma wanda ba Musulmi ba zai iya kamuwa da kowacce irin cuta. Sai dai fa irin garkuwar da manzon Allah SAW ya baiwa Musulmi kamar Azkar na safe da yamma, da Hailala da Salati da karatun al-qur'ani, da sauransu wannan garkuwa ne ga Musulmi.

A saboda haka, babu wani maganin wata cuta da mutum zai ware ya alakanta shi da Musulunci ya nuna duk wanda ba shi ba na kafurci ne, ko da kuwa idan ansha za'a samu sauki. Shaidan ya yi magana manzon Allah SWA ya ce abinda ya fada gaskiya ne, amma shi din makaryaci ne, dan haka ko kafiri ya yi magani sai ka dauki maganin ka barshi da kafurcinsa. Malamai sunyi bayanin cewar duk wani magani da binciken Likitoci ya tabbatar da cewar yana maganin cuta kaza to Wannan maganin ya halatta Musulmi ya yi amfani da shi, matukar ba ayi amfani da wasu sinadarai da suka sabawa Musulunci ba, kamar Alhanzir da sauransu.

Yana da kyau al'umma su fadaka, kada wasu masu tallar magani su dinga yaudararsu da cewa magani kaza na MUSULUNCI ne, sabaninsa kuma na kafurci ne. Da yawan masu tallar irin wadannan magunguna akan samu marasa tsoron Allah su dinga fadawa Mutane zuma da man zaitun da habbatus Sauda da dangoginsu sune maganin Musulunci sabaninsu kuma maganin Nasara ne, eh Musulunci bai hana yin amfani da maganin Nasara ba. Duk wanda ya fada maka haka ya yaudareka, kamar yadda zuma take magani haka bincike na likita ya tabbatar da cewa Kafenol da dangogin Maganin Bature suna yin magani.

Babban kuskure ne mutane su dauka akwai wani kantin saida Magani ISLAMIC CHEMIST, duk wani dakin sayar da magani matukar an gwada maganinsu an samu sauki to shima Islamic chemist ne, ko da kuwa wanda ba musulmi bane ya yi maganin. Kamar yadda na fada a baya, cuta bata da alaka da addini haka shima magani. Kirista zai iya amfani da Man-zaitun ya sha ya samu sauki, kamar yadda Musulmi zai iya amfani da Paracetamol ya sha dan ya samu sauki, babu inda aka ce ya sabawa addini dan ya sha maganin bature.

Yana da kyau mutane su yi tattalin lafiyarsu. Duk mara lafiya kamata ya yi a kaishi asibiti likitoci su gwada shi su san ciwon da yake damunsa, da kuma irin maganin da ya dace da shi, amma wasu kanyi kuskure kawai daga ciwo ya kama su sai su samu irin wadannan masu magungunan su yi ta dafka musu wasu abubuwa da ka iya tsananta ciwon da yake damunsu a matsayin magani, tunda babu wasu gwaje-gwaje na kimiyya da suka yi wajen gane cutar da kuma maganin da ya dace da ita. Haka kuma, mafi yawan irin wadannan magungunan dace ne kawai, domin wani yana iya shan hulba da Habbatus Sauda su yi masa magani wani kuma su tsananta cuta a gareshi. Wasu marasa tsoron Allah sai su fake da yiwa mutane wa'azi da fadin Allah ya ce Annabi yace, daga karshe kuma su b'uge da tallar magani da tallata hajojinsu.

Duk maganin da binciken kimiyyar likitoci ya gano cewa yana magani ya halatta a yi amfani da shi, matukar ba zai cutar ba, ko kuma baya dauke da wani abu da Musulunci ya haramta kamar giya, dan haka, kada kawai dan kana fama da ciwon "sugar" wani ya ce kaje ka yi ta shan Hulba da zaitun da sauransu ba tare da ya gudanar da kwakwaran bincike na kimiyya akanka ba. Eh gaskiya ne Hulba da sauransu duk suna maganin cututtuka, amma ba daidai bane wasu su dinga Yaudarar mutane da sunan cewa Magani kaza shi ne na Musulunci koma bayansa kuma na kafurci ne. Da maganin Bature da sauran zuma da Hulda da na 'yar me ganya duk sunansu magani, duk wanda bincike ya nuna cewa yana magani to shima ISLAMIC MEDICINE ne idan akwai wani magni da aka kebance da Musulunci. Allah ya sa mu gane.

Yasir Ramadan Gwale
10-10-13

2 comments:

  1. tabbas,maganan gaskiya ne,Amma ka sani akwai bambanci tsakanin magungunan sai dai ka sake nazari da bincike

    ReplyDelete