Sunday, October 13, 2013

SHUGABA GOODLUCK JONATHAN: Babban Mai Zunubi Ne!!!


SHUGABA GOODLUCK JONATHAN: Babban Mai Zunubi Ne!!!

Hakika shugaban kasa Goodluck Jonathan ya shafawa fuskarsa toka, inda karara ya fito yake yakar Musulmi ta sunkuru da kuma bayyane. Irin yadda shugaban kasa yake amfani da addini yake yakar Musulmi a AREWA da KUDU MASO YAMMA abin ya kai innanaha, domin har ta kai cewar ko kunya baya ji wajen nuna kiyayyarsa ga Musulmi da Musulunci a kusannan dukkan rabon mukamai na gwamnatin tarayya, da kuma bayar da damarmaki ga 'yan kasa, inda babu kunya babu tsoron Allah shugaban yake ware Musulmi tare da nuna fifiko ga kiristoci na kudu da na Arewa. Kamar yadda ya faru a baya, kowa yaga yadda Shugaban Sojojin Najeriya Brigadier General Ihejirika ya zabge dukkan manyan sojoji Musulmi daga dukkan manyan mukamai, ya maye gurbinsu da kiristoci gaba ki daya, wannan karon ba wai 'yan Arewa kawai aka taba har da Yarabawa 'yan kudu Musulmi, abin da ya tabbatar da cewar shugaban karara Musulunci da Musulmi ne baya so a dukkan harkokin gudanar da gwamnatin wannan kasa.

Sanin kowa ne cewa yankin Kudu maso yammacin Najeriya inda Yarabawa suke da rinjaye, kuma Musulmi sune suke daukar kaso mafi yawa na al'ummar yarabawa, amma babu wani Minister ko mai baiwa shugaban kasa Shawara Musulmi da Goodluck ya dauka daga yankin, duk wani nade-naden da zai yi a wannan yankin KIRISTA yake nadawa babu kunya babu tsoron Allah. Kowa yana ji yana gani, amma anyi shiru, kowa baya son ace yana amfani da Addini dan kar ya raba kan kasa, amma shi shugaban yana yin gabansa gadi wajen cin dunduniyar Musulmi da kwashe musu kafafu, tare da amfani da kungiyar CAN suna ta kuwwar Iblis cewar ana nunawa kiristoci bambanci.

Kwatsam kuma sai muka ji rahoton cewar sojojin da ake dauka a makarantar horon soja ta Kaduna NDA nanma ankwashe kafafun musulmi warwas. Inda bayanai suka nuna cewar a cikin daliban da aka dauka a Kaduna 14 guda 11 duk kiristoci ne guda 3 ne kacal Musulmi, haka jihar Adamawa inda aka dauki dalibai 13 amma 11 duk kirista 2 ne kacal Musulmi, a Taraba ma haka aka yi kamar yadda aka yi a Adamawa inda 2 ne kacal Musulmi sauran 11 duk kirista ne, a jihar Plateau kuwa duk 13 gaba daya kirista aka dauka babu Musulmi ko daya. Wannan fa shine irin misalin rashin adalcin da shugaban kasa yake nuna mana ba tare da tsoro ko kunyar abinda zai je ya zo ba.

Haka kuma, kowa yana ganin yadda aka zuba mana sojoji galibinsu Kiristoci a musamman jihohin Adamawa, Borno da Yobe da sunan dokar ta baci suna ta yi mana kisan babu gaira babu dalili. Kiri-kiri ga sojoji da uniform suna aikata kisan kai ga talakawa bayin Allah da basu san hawa ba balle sauka sai a kauda kai a ce wai 'yan ta'adda ne suka yi mana wannan aika-aikar. Ya zama dole mu fito mu kalaubalanci wannan mummunan zunubin da shugaban kasa yake tafkawa. Najeriya kasarmu ce mu duka, mu bamu ce a dauki hakkin wani a bamu ba, amma ya zama dole, wajibi, tilas a bamu namu hakkin, kuma dole a ringa daukar ma'aikata gwargwadon adadin al'ummar da suke a Najeriya, wannan abin da shugaban kasa yake wallahi summa tallahi matakaine na yiwa Musulmi mummunar illa, koma anyi angama.

Muna da labarin irin abin da Shugaban Kamaru Poul Biya yayi wajen kakkabe hannun duk wasu Musulmi daga samun wasu manyan mukamai na soji da 'yan sanda da kwastam da sauran mukamai na siyasa. Irin wannan abin da Biya ya yi wallahi shi wannan shugaban namu yake aiwatarwa, amma abin mamaki duk mun zura ido muna ji muna gani ana yi mana wa-kaci wa-tashi. Lallai mu hadu mu hada karfi da karfe wajen ganin mun ce bamu yarda da wannan cin-kashi da wariya da ake nuna mana ba. Irin wannan zunubi da Shugaban kasa yake aikatawa babu inda zai kai kasarnan sai ramin halaka da da-nasani. Tabbas idan bamu tashi mun farka ba, to nan gaba mu da 'ya 'yanmu wallahi sai dai karfin Imaninmu ya kwacemu a hannun abokan gabarmu. ALLAH YA KIYAYE.

YASIR RAMADAN GWALE
13-1013

No comments:

Post a Comment