Thursday, October 10, 2013


MUNA KIRA GA GWAMNATIN KANO TA GAGGAUTA KORAR ALI BABA FAGGE

Kalaman da aka ruwaito Hon Ali Baba Agama Lafiya Fagge yana yi akan Malaman Addini cin fuska ne ba wai ga Malaman Addini ba har da Gwamnatin Kano. Hakika damuwa ta kai damuwa, a ce daya daga cikin Mashawartan Gwamna wanda ya kamata yafi kowa taka tsan-tsan da kokarin bin Addini sau da kafa shi ne yake furta irin wadannan munana kalamai masu zubar da kima da mutunci da haiba, wannan abin kaico ne, abin assha ne, abin Alla-wadai ne. Bayanai sun nuna cewar ba wannan ba ne karon farko da shi wannan mutum ya taba yin irin wannan gagarumar katobara ba, a baya ma ya taba yin maganganu masu kama da haka, rahotanni sun same mu cewar Hukumar Hisbah karkashin Jagorancin Mal.Aminu Ibrahim Daurawa ta ja hankalin wannan mutum akan abinda ya fada kuma har ya nuna damuwarsa akan kuskuren da ya yi, da nuna cewa a gafarce shi sharrin shaidan ne.

Abin mamaki sai gashi a jiya ya sake maimaita irin kalaman da ya yi, har ma yana kama sunan kwamandan Hisbar a matsayin daya daga cikin wadan da yake kira da su dinga sayan fina-finan Hausa dan karin samun gogewa wajen yada da'awa. Wannan cikakken rashin mutunci ne da nuna kaiwa maqura wajen nuna dan isakanci da tsageranci da jahilci da gidadanci da kidahumanci da toshewar kwakwalwa. Haka kuma, wadannan kalamai tamkar ya kwancewa gidansu da danginsu zani ne a kasuwa cewar basu bashi wata tarbiyya ta Islama da duk d'a nagari yake samu daga Iyayansa ba.

Lallai muna kira ga Mai girma Gwamna Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso ba tare da wata-wata ba ya fito ya nesanta kansa da wadannan munana kalamai na mai bashi shawara ta fuskar Addini, kuma ya gaggauta sallamarsa daga wannan mukami. Dan mutum irin wannan da yake maganganu da suka yi kama da na mai tabin hankali bai kamata a ce shi ne zai baiwa Gwamnati shawara a Addinance ba. Muna nuna bakin cikinmu da damuwarmu da kaiconmu akn wadannan miyagun kalamai da wannan mutumin ya yi. Allah ya raba wannan Gwamnati da mutane irinsu Ali Baba miyagu fandararru masu kafurcewa gaskiya.

Muna yi masa addu'ar Allah ya shirye shi. Amma tabbas wadan nan kalamai zasu jima suna yi mana ciwo a duk sadda muka tuna su.

Yasir Ramadan Gwale
10-10-13

No comments:

Post a Comment