Wednesday, July 31, 2013

LABARIN AMINA DA MIJINTA ADAMU MAI CIKE DA HIKIMA


LABARIN AMINA DA MIJINTA ADAMU MAI CIKE DA HIKIMA

Amina ta auri mijinta Adamu tun kusan shekaru 48 da suka gabata. Gaba dayansu Amina da mijinta babu wanda ya yi ilimin Boko kafin su yi aure, haka nan suka tashi daga makarantar Allo babu wani karatu da suka yi, bayan da Adamu ya girma ne, ya kama sana’ar gidansu wato sukar nama, dan Adamu ya tashi ya samu kanin mahafinasa Sunusi yana taya mahaifinsa gasa tsire, anan gurin sana’ar mahaifinsa ya koyi yadda ake fede dabba, a kasa ta, a kuma sayar tare da samun riba, haka kuma, Adamu ya koyi yadda ake yin sukar tsire a jikin tsinkayen da ake gasawa akan tukuba. Bayan da Adamu ya kawo karfi ne, ya kuma samu dan jari daidai gwargwado ya bude nasa wajen gasa nama a bakin titi, cikin ikon Allah da agazawarsa ya sanyawa Adamu albarka a cikin sana’arsa, har ya dara mahaifinsa samun kasuwu.

Adamu yana cikin wannan sana’a tasa ne ta gasa nama, ya auri wata makociyarsu Amina, yarinya ce mai hankali, ga tarbiyya da ladabi da biyayya, ga kunya da yakana. Rayuwar aurensa ta zama abin sha’awa domin suna zaune lami lafiya babu wani abu na rashin jituwa da yake tsakaninsu. Amina kuwa, kullum sai tayi asuwaki da tsinken tsire dare da rana, daman abu nasu, maganin a kwabesu. A kwana a tashi Adamu ya samu karuwa inda matarsa ta Haifa masa zankadeden yaro namiji, wanda ya radawa sunan mahaifinsa Muhammadu Auwalu, yaro ya tashi cikin managarciyar rayuwa, abin misali a wajen mahaifansa, haka dai Amina ta yi ta kwankwatsawa Adamu ‘ya ‘ya masu cike da koshin lafiya.

Kasancewar Adamu da matarsa Amina ba su yaki jahilcin Boko ba a rayuwar kuruciyarsu suka ce lallai ‘ya ‘yansu sai sun ci gajiyar wannan karatu na boko. Auwalu da kannensa Sani da Salisu, duk an sanya su makarantar Boko inda suke zuwa makarantar da ke kusa da unguwarsu suna dawo a kullum. Wani aiki da Amina ta baiwa kanta shi ne, tace, ita kuwa sai ta koyi karatun Boko ta hanyar ‘ya ‘yanta, wannan ta sanya, duk lokacin da su Auwalu suka dawo daga makaranta, Amina bata barinsu su yi ta watangaririya a unguwa, sai ta zaunar da su tace kowa ya dauko littafinsa ya karanta mata abinda aka koya musu; haka zata bi kowannensu daya bayan daya tana tambayarsa ya karanta ta ji, anan ne fa yara suke gardama da mahaifiyarsu, domin sai sun karanta sai tace ba dai-dai suka karanta ba, alhali kuwa Amina bata sani ba, tana yin haka ne kawai dan ta gwada fahimtarsu, anan zasu dinga yi mata musu akan cewa abinda suka karanta dai-dai ne ita ce bata fahimta ba, Ashe duk karatun da su Auwalu suka yi Amina tana rikewa, idan sun tafi makaranta sai ta samo alkami da takarda tana bitar abinda aka koya musu, haka har ta iya ta kuma haddace, tun su Auwalu suna firamare Amina take binsu a karatu, tana koyar karatu a wajensu, ba tare da su yaran sun fahimci cewar ita mahaifiyarsu bata iya karatu ko rubutu ba.

Bayan da yara suka girma Auwalu ya kamala makarantar sakandare da sakamakon jarabawar GCE mai kyan gaske, ya wuce jami’ah ba tare da wani bata lokaci ba. A daidai wannan lokacin kuwa Amina ta iya rubuta wasika da Hausa, sannan ta iya karanta kalmomin turanci masu sauki. Da farko Amina ta ringa baiwa mutanen gidansu mamaki inda ta ringa tura Auwalu ko Salisu ko Sani da rubutacciyar wasika ta gaisuwa ya kai gidansu, sai ayi ta mamaki a ina Amina ta iya rubutu da karatu har da zata aiko da wasikar da sai an kirawo dan makwabta yazo ya karantawa mahaifanta, amma duk da haka suka yanke hukuncin cewar ai tunda yaran Amina suna zuwa makarantar Boko sune suke rubuta mata wannan wasikar.

Abu kamar wasa har sai da Amina ta iya yin gajeruwar Magana da turanci da ‘ya ‘yanta duk kuwa da cewa a mafiya yawancin lokaci idan tana yi musu turancin yaran kan bushe da dariya tare da yi mata gyara, amma basu taba fahimtar cewar mahaifiyarsu bata je makarantar Boko ba. Mahaifinsu Auwalu kuwa malam Adamu mai Nama tuni likkafa taci gaba, inda ya bude guraran gasa nama da dama, Allah ya buda masa sana’arsa, bai taba gajiyawa ba wajen biyan kudin makarantar ‘ya ‘yansa, yana kula da dukkannin bukatunsu na makaranta dai-dai gwargwado.

A kwana a tashi Muhammadu Auwalu ya kammala karatun Injiniyan Kwamfuta, a yayin da Muhammadu Sani kuma ya karanci ilimin duwatsu da albarkatun kasa da ake kira Geology, salisu kuwa yana aji na kusa da na karshe a jami’a inda yake karantar fannin aikin Injiyan Gona wato Agricultural Engineering.

Mahaifansu guda biyu Amina da Adamu farinciki a tattare da su kada ka tona, domin suna alfahari da wadannan yara nasu da kuma karatrun da suka yi, domin abinda su basu yi katarin samu ba yau ga ‘ya ‘yansu sun samu. Tamabaya, shin kana jin akwai wani mahaluki da zai cewa Amina karatun Boko Haramunne ta saurare shi ko ta yarda da zancensa? Shakka babu amsar wannan tambaya bayyananna ce. Haka kuma, zamu fahimci cewa ashe ‘ya ‘ya suna iya zama makaranta ga uwa mai wayo irin Amina, Lallai dole iyaya mata su ja ‘ya ‘yansu a jiki sosai domin sanin irin halin da suke ciki da kuma fahimtar yadda za’a bullowa lamarinsu, da ma daukar wani darasi abin koyi a tare da ‘ya ‘yan kamar yadda Amina ta yi.

A ganinka wane irin kanu ya kamata a baiwa wannan labari? Muna addu’ar Allah ya karbi ibadunmu a cikin wannan wata mai alfarma.

Yasir Ramadan Gwale
31-07-2013

No comments:

Post a Comment