Sunday, July 28, 2013

LABARIN AMIRA YA SANI ZUBAR DA HAWAYE




LABARIN AMIRA YA SANI ZUBAR DA HAWAYE

Amira yarinya ce da ta biyo maza a gun mahaifiyarta da mahaifinta, wato tana da yayyi uku maza. Allah cikin hukuntawarsa ya sanya soyayya da shakuwa tsakanin Amira da Mahaifanta guda biyu dakuma yayyinta maza suna kula da Amira yadda ya kamata suna tarairayarta, sannan Amira yarinya ce mai fara'a ga yakana ga ladabi tana barin duk abin da aka ce ta bari, Muta...ne da dama sun fahimci irin yadda Baban amira yake kaunar diyarsa ta yadda hatta Masallaci da ita yake zuwa, ko a Masallaci mutane da dama sun san Amira suna mata wasa duk lokacin da suka zo da Mahaifinta.

Wata rana Maman Amira ta gayawa Abban Amira cewa zasu je gidan biki a danginsu, dan haka tana son ya kaisu a motarsa. Babu wani bata lokaci Abban Amira yace su shirya zai kaisu ya ajiye su a gidan bikin. Umman Amira ta yiwa Amira wanka tana gama shafawa Amira mai sai Amira ta tashi aguje taje ta dauko wata riga fara mai korayen maballai da beza mai ban sha'awa, tace umma sakamin wannan! Umman Amira ta ce gaskiya bazan sa miki wannan rigarba gidan biki zamuje, idan na sa miki bata ta zakiyi, nan Amira ta kara cewa Umma dan Allah ki sa min wannan rigar, Umman Amira ta kara nanata mata cewa gaskiya bazan sanya miki wannan rigarba! Nan amira ta tafi da gudu dakin mahaifinta sanye da "under wears" Babanta yace ya baki sa riga ba,sai tace Umma tace bazata sa min wannan Rigarba, ta dauko rigar ta nuna masa, nan mahaifin Amira ya kira Umman Amira yace ki sa mata wannan rigar mana, Tace Haba! Abban Amira gidan Biki zamu je idan na sa mata bata rigar nan zata yi kaga kuma fara ce, Jin haka sai Amira ta sa kuka, babanta ya rarrasheta yace yi hakuri.

Nan umman Amira ta kamo hannunta taje ta sanya mata wasu kaya riga da wando masu ruwan kasa, amma dai fuskar Amira babu Annuri. Hakanan suka kama hanya zuwa gidan biki, sun tafi da zummar zasu kwana biyu saboda bikin dangi ne, can bayan Magriba a gidan biki jama'a sun cika sai wani Yaro ya taho a Guje yana cewa ga Amira can na Gudawa a waje, kan kace kwabo umman Amira ta garzaya inda ta kamo hannunta tana fada tana cewa yanzu a waje yakiyi kashi sai na miki duka, nan Amira ta kara cewa a dorata a FO, aka miko Fo ana dora Amira sai da ta cika Fo din nan taf! Hankalin Umman Amira ya tashi domin tasan babu lafiya, nan da nan ta kira kaninta Nasiru yazo damotarsa inda suka garzaya Asibitin Nasarawa da Amira. Allahu Akbar! Kafin su isa asibitin Amira ta rasu! Suna zuwa likita ya karbeta ya yi mata gwaji-gwaje, ya ce musu ai ta rasu!

Daga nan fa biki ya kare, mutane da yawa sun yi jimamin mutuwar Amira ainun. Umman Amira ta bugawa Abban Amira waya akan yazo dan ta sanar d shi halin da ake ciki, ko da yazo ashe tuni ya samu labarin cewa Allah ya yiwa diyarsa Amira rasuwa. Abin da Abban Amira ya fara cewa da Umma Amira shine "ME YA SA BAKI SANYA MATA RIGAR DA TAKE SOBA" wannan magana ta girgiza Umman Amira matuqa da gaske! Abban Amira bai gushe ba yana maimata wannan magana, me ya sa baki sanya mata rigar da take so ba, yana zubar da hawaye yana maimaitawa! Yace ta rasu da bakin cikin abinda take so bata samu ba. Umman Amira tace har aka yi wata guda da Rasuwar Amira Abbanta yana maimaita wannan maganar "ME YA SA BAKI SA MATA RIGAR DA TAKESO BA" Ta rasu tana da bakin cikin abinda take so bata samu ba. Umman Amira tace hakika duk sadda ya ambaci wannan magana sai na girgiza ainun. Ni kaina da nake baku labarin na girgiza da Rasuwar Amira na santa yarinya ce mai fara'a da san mutane ta rasu bata wuce shekaru uku zuwa hudu ba. Ya Allah ka jikan Musulmi.

Yasir Ramadan Gwale
21-07-2013



No comments:

Post a Comment