Tuesday, July 9, 2013

SU WAYE SUKA KASHE MANA 'DALIBAI A YOBE?



SU WAYE SUKA KASHE MANA 'DALIBAI A YOBE?

Wannan wata Muhimmiyar tambaya ce, mai matukar Muhimmanci da ya kamata mu nemi amsarta. Kamar yadda dukkanmu muka sani ne, a kwanaki uku da suka gabata aka je har wata makarantar kwana a garin Mammado dake jihar Yobe aka kashe wasu dalibai sannan aka bankawa gawarwakin wuta! Hasbinallahu wani'imal wakeel. Wannan tashin hankali da me yayi kama! Me wadannan yaran suka yi da suka cancanci kisa ta irin wannan hanyar? Wa suka yiwa laifi? Me ye dalilin da ya sa aka kashe su? Shin dan su Musulmi ne ko kuwa dan sun samu sukunin zuwa makaranta domin kawar da jahilici?

Kasancewar kowannenmu yana da masaniyar cewar ita wannan jihar ta Yobe tana karkashin Dokar ta baci ne, kuma shugaban kasa da shugaban rundunar sojojin Najeriya sune kadai suke da masaniyar yadda al'amuran tsaron jihar yake gudana. Shin tsakani da Allah wa zamu zarga da wannan mummunan aikin na ta'addanci? Mutanan da ake cewa Boko Haram? wanda dukkan bayanan da sojoji suke bayarwa yana nuna cewar an fatattaki sansanoninsu a dukkan wadannan jihohi, inda suka koma dazukan da ke kan iyaka suna sulalewa, ko kuwa Sojojin da suka aikata irin haka a garin Baga?. Hakika wannan al'amari akwai daure kai da rikitarwa ace irin wannan mummunan aikin ta'addanci ya faru a lokacin da Sojoji suke makare a jihar Yobe da sunan aikin dawo da zaman lafiyar da yayi hijira a wasu sassan jihar.

Har yanzu bama gama hucewa daga radadin kisan da aka yiwa 'yan uwanmu kusan sama da mutum 200 a garin BAGA na jihar Borno ba, wanda dukkan bayanai suka tabbatar da cewar Sojojin Najeriya ne suka aikata wannan mummunan aikin ta'addanci karkashin kulawar Shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda Kirista ne da Shugaban rundunar sojojin Najeriya Manjo Ihejiraka wanda shima kirista ne. Ciki da wajen Najeriya da kungyoyin kare hakkin bil-adama sukai ta yin Allah wadai da abinda akayi a garin Baga, shugaban kasa ya kaddamar da kwamitin bincike wanda tundaga lokacin shikenan aka binne maganar. Daga Karshe muka jiyo Gen Ngubadiya yana cewar wai su 'yan Boko Haram ne suka sanya kayan sojojin suka aikata ta'addanci a garin Na Baga! Kuma zancen ya hau ya zauna a kunnen jagororinmu.

Kamar yadda Tarihi ya nuna mana cewar Sojojin Najeriya Musamman Kiristoci daga cikinsu sun jima suna aikata ta'addanci akan al'ummar Musulmi Arewa. Ba wannan ne karan farko ba, domin dukkanmu Mun san cewar Manjo Kaduna Nzeagwu kirsita ya kashe mana manyan 'Yan Arewa a 1966, wanda muka yi asarar Sa Abubakar Tafawa Balewa da Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da sauran manyan mutane. Haka kuma, Sojoji suka kashe Gen. Murtala Muhammad da Gen. Zakariyya Maimalari wanda kiristoci daga cikin sojojin Najeriya suka aikata irin wannan danyan aiki a baya.

Wannan fa tarihi ne ya nuna mana yadda aka jima ana kashemu babu laifin fari babu na Baki. Mu wa muka taba kashewa? Shin mun kashe Gen. Ojukku da ya haddasa mana yakin Basasa? Ko kuwa mun kashe Gen. Lakwot Zamani da ya kashe mana dumbin 'yan uwa a Kudancin Jihar Kaduna? Ko mun kashe Air Commador Jonah David Jang wanda aka kashe dubban Musulmi karkashin ikonsa a jihar Plateau? Wadannan mutane ne da sun aikata mana ta'addanci kiri da muzu amma babu wanda muka dauki ko da allura muka nuna shi da ita, amma abi yaranmu har cikin dakunan kwanansu ayi musu irin wannan kisan gilla!

A kwanakin baya da akace wasu Bama bamai sun tarwatse a barikin Sojoji a JAJI dake jihar Kaduna, Shugaban sojojin Najeriya Ihejirika ya zargi Cammandan da yake Lura da wannan bariki Gen. Muhammad Isa wanda Musulmi ne aka zargeshi da abinda suka kira "Negligence of Duty" Wato Gazawar aiwatar da aikinsa, suka yi masa ritayar karfi da yaji sannan kuma suka kawo Kirista suka maye gurbinsa da shi, shin wannan me yake nuna mana, wanne irin hoto ake bamu, bayan mutananmu Musulmi da aka yiwa Ritayar dole kuma gabaki daya aka maye gurabensu da Kiristoci daga Yankin Kudu maso Kudu da kudu maso Gabas.

Shin ba shugaban kasa bane yake da hakkin tsare rayukan 'yan Najeriya da dukiyoyinsu? Menene amfanin dokar tabacin da aka kafa a wadannan jihohi, inda har za'a aikata irin wannan mugun aiki, kuma wadan da suka aikata su sulale salin alin babu wanda ya gansu! Sojojin da suka hana rike ko da wayar salula ballantana wani makami ko bunduga. 

Lallai muna kira da gwamnatin Jihar Yobe da dattawan Arewa da 'yan majalisunmu na Arewa su matsawa Shugaban Sojojin Najeriya lamba tare da Shugaban kasa su bamu bayanin su waye suka kashe mana yara? Wallahi bamu da haufi mutum ko Bakuraishe ne shi idan aka kamashi da laifi ayi masa hukunci daidai da abinda yayi. Rashin Adalcin da wannan Shugaban kasar yake Nunawa karara babu inda zai kai wannan kasar sai kara dagulewar lamura, su sani wallahi bazamu zuba ido ana yi mana irin wannan kisan gillah ba, Lallai tura ta kai bango.

Yasir Ramadan Gwale 
09-07-2013 

No comments:

Post a Comment