Thursday, July 4, 2013

TARIHIN KAFUWAR KUNGIYAR IKHWAN (Muslim Brotherhood) A KASAR MASAR


TARIHIN KAFUWAR KUNGIYAR IKHWAN (Muslim Brotherhood) A KASAR MASAR

Daga Yasir Ramadan Gwale

An kafa kungiyar Ikhwanul Muslimeen ko Muslim Brotherhood kafin daga bisani ta rikide zuwa jam'iyyar sisaya a shekarar 1928. Ita wannan kungiya wani Malamin Makaranta ne da ake kira Sheikh Hasan Ahmed Abdel Rahman Muhammed al-Bannah, shine ya kafa ta, tare da taimakon wasu abokansa su shida ma'aikata a yankin Suez. shi dai Shiekh Hassan Al-Bannah malamin makaranta ne da ya yi fice wajen kira zuwa ga yin adalci a tsakanin al'ummah, an sanshi sosai wajen wayar da kan al'ummar Musulmi akan al'amuran da suka shafi Addinin Musulunci, haka kuma, Al-Bannah mutum ne da yayi kaurin suna wajen kiran mutane zuwa ga tafarkin Shari'ah Islama tun a wancan lokaci. A matsayinsa na Malamin Makaranta kuma karamin Limami yayi amfani da damarsa tun a wancan lokaci wajen cusawa matasa koyi tare da Riko da Addinin Musulunci, kuma ya shahara da adawa da salon mulkin turawan Ingilishi da na faranshi tare da kutsen turawan Burtaniya a kashe daban daban, ya kuma yi yaki tare da Allah wadai da danniya da rashin gaskiya.

Tun lokacin da aka kafa Ikhwanul Muslimeen ta mayar da hankali ne wajen Ilmantar da  al'umma da ayyukan jinkai da taimakawa al'umma. Wannan aikin da MB suka faro a wancan lokacin ya sanya suka samu karbuwa da tagomashi sosai a wajen al'umma, nan da nan suka fara aiwatar da aiyyuka irin na Siyasa tare da kunna kai cikin Sha'anin Mulki da siyasa dan wayar da kan al'ummah su san menene hakikanin 'yancinsu tare da sanin amfanin gwamnati a garesu. Tun daga kafuwar Ikhwan a shekarar 1928 har kusan wajejen shekarun 1938 wato shekaru goma da kafuwarta tana gudanar da mu'amalolinta ba tare da wata tsangwama ba.

Daga nan Jam'iyyar Muslim Brothers ta shiga aiki gadan gadan da sauran kungiyoyi na kasashen duniya, sai dai kuma, 'ya 'yan kungiyar sun fuskanci tsangwama da matsawa sosai musamman a hannun Shugaban Masar na wancan Lokacin Mahmud Fahmi Nokrashi, domin a lokacin masu rike da madafun Iko sun fara ganin Ikhwan na neman zama barazana a garesu, a lokacin ne aka kama tare da garkame 'ya 'yan kungiyar aka kuma cusguna musu, tare kuma da karbe wasu muhimman takardun gudanarwa na kungiyar. A shekarar 1948 kusan shugabannin Ikhwan 32 aka daure su, aka kuma gana musu azaba tare da kiransu da kungiyar 'yan ta'adda, saboda kawai suna kiran abi tsarin addini a harkokin gudanarwa na hukuma. A ranar 28 ga watan Disambar 1948 aka samu wani dalibi mai suna Abdel Meguid Ahmed Hassan inda yayi kundumbala ya aika da Shugaban Masar na lokacin Mahmud Fahmi Nokrashi lahira a zaman daukar fansar matsawa da tsangwamar 'ya 'yan kungiyar ta Ikhwan, kimanin wata guda da rabi aka samu wasu mutane da ake kyautata zaton magoya bayan shugaban da aka kashe ne suka bi dare suka kashe Shugaban Kungiyar Ikhwan Sheikh Hasan Ahmed Abdel Rahman Muhammed al-Bannah a babban birnin AlKahira, bayan kisan Albannah ne aka nada wani tsohon babban me shari'ah Hassan Isma'il al-Hudaybi a matsayin sabon shugaban Ikhwan.

Sannan kuma, a shekarar 1952, aka zargin kungiyar Ikhwan da farwa wasu gine-gine da ake aikata badala a cikinsu a babban birnin alkahira da suka hada da gidajen rawar disko da gidajen shan barasa da wajejen shakatawa inda ake haduwa maza da mata, da gidajen kalln fina-finai da wajen wake wake da kade-kade kusan 750, wanda galibinsu aka tabbatar mallakar turawan ingilishi ne na Burtaniya.

05-07-2013

1 comment:

  1. Masha Allah Allah sakada alheri tambaya ta anan don Allah ina zansamun littafan Yan ikhwan da karance karancensu

    ReplyDelete