Tuesday, July 16, 2013

SHUGABA UMAR HASAN AHMAD AL-BASHIR: ZAKIN AFURKA



SHUGABA UMAR HASAN AHMAD AL-BASHIR: ZAKIN AFURKA 

Shugaba Umar Hassan Muhammad Ahmad Al-Bashir na Sudan yana daya daga cikin shugabannin Afurka masu karfin hali da rashin nuna tsoron kasashen Turai da Amerika a zahiri. Tun bayan da Kotun duniya mai bincike laifukan yaki ta bayar da sammacin kama shi a duk lokacin da ya kuskura ya tsallaka kasarsar Sudan zuwa wata kasar musamman kasashen da suka sanya hannu akan yarjejeniya da kotun ICC, amma wannan ba sanya shi shgaba Bashir din ya tsorata ba. Domin tun bayan fitar da wannan sammaci wasu daga cikin kasashen Afurka irinsu Uganda da ke da makwabtaka da Sudan suka nuna Shugaba Bashir da yatsa cewar duk lokacin da ya kuskura ya tsallako musu kasa sunansa kamamme. Amma duk da haka Shugaba Bashir ya tsallaka zuwa wasu daga cikin kasashen Afurka musamman Adis Ababa da Masar da Tchadi duk karkashin wannan tarko da aka dana masa, baya ga kasashen gabas ta tsakiya da ya dnga ziyarta akai akai, sannan yayi doguwar tafiya zuwa kasar Chana da ta kada hantar da dama daga jam'an gwamnatinsa dan suna ganin za'a iya kamashi kafin isa ko dawowarsa.

A taron da ake gudanarwa na kasashen Afurka a Abuja a makwannan, shugaba Bashir yana daga cikin mahalarta taron kuma shine wanda yafi daukar hankali a kusan dukkan shugabannin da suka halarci taron kasancewar yana da wannan sammaci akansa. Wannan ta sanya kungiyoyin da turawa suka kyankyashe su suke ta kumfar baki akan cewar lallai Najeriya ta gaggauta kamashi kuma ta mikashi zuwa ga ICC, amma abinda basu sani ba shine, akwai kyakykyawar huldar Diplomasiyya tsakanin Khartoum da Abuja, domin babu yadda shugaba Bahsir zai wanke kafa ya kama hanya zuwa Abuja dan halartar wannan taro alhali yasan akwai turaku da aka dana masa ba tare da an samu kyakkyawar tuntuba tsakanin Khartoum da Abuja ba. A 'yan watannin da suka gabata Shugaba Goodluck Jonathan shima ya kai ziyara zuwa birnin khartoum kuma sun karraashi, kasancewar akwai tsohuwar alaka a tsakann Sudan da Najeriya. Wannan ce a ta sanya shugaba Bashir ya samu tarya mai kyau a daidai lokacin da ya isa Abuja, abinda bai yiwa masu rajin kare maganganun turawa dadi ba.

Me ya sa ake son kama shugaba Bashir ne? Kamar yadda aka kwazazatawa duniya cewa kotun duniya dake Hague ta kama shugaba Bashir da aikata laifukan yaki da cin zarafin Bil-Adama a yankin Dafur dake kudancin Sudan. Hakika anyi barna kuma anyi ta'adi a yankin Dafur. Amma yana da kyau mutane su san cewa haka kurum Shugaba Bashir ba zai dauki Makami yana kashe al'ummar kasarsa ba, kasashen Turawa da Amerka basu da gaskiya ko kadan, domin sune kanwa uwar gami akan abinda ya faru a yankin Darfur idan kai tsaye baka ce shirya abin suka yi ba, domin gogawa shugaba Bashir laifin da zai kai ga tunkude shi daga kan karagar Mulki. Kasancewarsa mai yawan ambaton addinin Musulunci da kuma san aiki da Shari'ar Musulunci ya sanya ake ta yi masa wannan tarnaki, haka kuma kasar Sudan wata kasace da suke ganin idan aka rusa ta kamar anc nasara akan kasashen Musulmi da suke a Nahiyar Afurka. Amma zance na gaskiya Shugaban kasar Libiya da aka kashe kusan zamu iya cewar shine mutumin da yayi uwa yayi makarbiya akan wannan rikici, domin kuwa su 'yan tawayen da suke a yankin Darfur Gaddafi shine komansu, shine yake basu kudi da makamai da dukkan abubuwa gudanarwa domin kitsa tawayen da a tunaninsa zai hana kasashen Afurka zaman lafiya, inda wannan zata bashi damar aiwatar da mafarkinsa na zama shugaban kasar hadaddiyar Afurka........... Zan ci gaba insha Allah.

Yasir Ramadan Gwale 
16-07-2013

No comments:

Post a Comment