Thursday, July 4, 2013

TARIHIN KAFUWAR KUNGIYAR IKHWAN (Muslim Brotherhood) A KASAR MASAR [2]



TARIHIN KAFUWAR KUNGIYAR IKHWAN (Muslim Brotherhood) A KASAR MASAR [2]

Bayan da Ikhwan ta tsinci kanta a wani irin wadi na gaba kura baya siyaki, wannan bai sanya wadan da suka gaji ragamar jagoranci daga Marigayi Albannah sun yi kasa a guiwa ba. Maimakon hakan ya sanya suyi rauni sai ya kara karfafa musu guiwa tare da dagewa akan abinda suka yi Imani shine mafita kuma hanya mikakkiya ta kubutar da al'ummar kasar Masri daga yannan 'yan kama karya da babakere. Domin sabon shugabanta yayi shiri da tanadin fuskantar dukkan wani irin kalubale da zai iya taso musu daga wajen masu mulki da suke ganin Ikhwan a matsayin wata babbar barazana ga dorewar Mulkinsu.

A zamanin Shugaba  Gamal 'Abd al-Nasser awjen shekarar 1952, wasu mutane da ba'a san ko su waye ba, sunyi yunkurin Halaka shugaba Nassir, inda yunkurin bai ci nasara ba, nan take kuma aka dora alhakin wannan hari ga Ikhwan. A wannan lokaci Shugaba Nassir ya gallazawa 'yan Ikhwan sama da duk wata gallazawa da aka yi musu a baya, domin kuwa kusan sai da aka cike gidajen Kurkuku da 'yan Ikhwan taf, banda horo mai tsanani da suka dinga fuskanta. Amma duk da haka wannan bai karya lagon matasan da suka sadaukar da lokacinsu da rayuwarsu dan wanzuwar Musulunci karkashin Ikhwan ba, mai makon abinda Shugaba Nassir yayi ya zogaye karfin kungiyar saima ya sake karfafata tare da samun jajirtattun matasa 'yan amutu.

Haka kuma, manyan mutane irinsu fitaccen Marubucin nan Sayyid Qutub suna daga cikin, mutanan da suka sha dauri a gidajen yari. An zargi Sayyid Qutud da hannu dumu dumu wajen hambarar da Gwamnatin Shugaba Nassir, zargin da ya musanta,  yayin da daga bisani aka sallameshi daga kas. Sai dai duk da sakin da aka yiwa Sayyid Qutud bai sha ba, domin kuwa sai da aka zartar masa da hukuncin kisa ta hanayar rataya a ranar 28 ga watan Augustan 1966, shekarar da aka kashe Sardaunan Sokoto Firimiyan Jihar Arewa Sa Ahmadu Bello da Tafawa Balewa Allah ya jikansu da gafar ya yafe musu kurakuransu. Kafin Zartar da hukuncin kisa akan su Sayyid Qutub an zargeshi da nuna tsanani wajen harkokinsa da kuma nuna matsanancin Kishin Addini a cewar hukumomi. A lokacin su Sayyid Qutub an samu baraka a cikin Ikhwan a yayin da wasu suka barranata daga irin salonsa na da'awa, da kuma gwagwarmaya.

Bayan Shudewar Gwamnatin Shugaba Nassir, wanda ya karb Gwamnati daga hannunsa Anwar Sadat ya dan sassautawa Ikhwan akan matsin da ta sha a baya. Duk da cewa Sadat ya sassauta tsananin kiyayya ga Ikhwan amma kuma hakan bai sanya ya dena ganin a matsayin haramtacciyar kungiyar tsagerun Musulmi masu san shigar da sha'anin addini cikin aikin hukuma ba. Daga baya, bayan da Anwar Sadat ya dai-daita akan karagar Mulki ya fito da kiyayyarsa a fili balo-balo ga Ikhwan da sauran kungiyoyin Addinin Musulunci a zamanin Mulkinsa. Shugaba Sadat ne shugaban da ya fara ayyana hulda ta kut da kut da haramtacciyar Kasar Israela, wanda wannan ya zama babban makamin da Ikhwan suka yi amfani da shi wajen Adawa da Shugaba Sadat, sai dai bayan da ya karbi Mulki a shekarar 1970, ya gamu da ajalinsa a tsakiyar filin wasa na babban birnin Alkahira a lokacin da yake karbar faretin bangirma a gaban dubban jama'a a ranar 6 ga watan Oktoban 1961, inda wani soja daga cikin Masu fareti ya saita dai-dai inda Shugaba Sadat yake zaune ya sakar masa harsashi, nan take ya aika da Shugaba Sadat Lahira, wannan soja da ya kashe shugaba Sadat ance dan wata kungiya ne da ake kira Tanzim al-Jihad.

To yanzu Mun gangaro zamanin Hosney Mubarak, zamu yi bayani akansa da irin nasa salon. Sannan kuma mukoma baya mu kalli wasu manufofin Ikhwan din da wasu al'amuran na kungiyar. Mu tara a gaba.

No comments:

Post a Comment