Thursday, July 18, 2013

SHUGABA UMAR HASAN AHMAD AL-BASHIR: ZAKIN AFURKA [3]



SHUGABA UMAR HASAN AHMAD AL-BASHIR: ZAKIN AFURKA [3]

Bayan da aka gwabza kazamin fada tsakanin kungiyoyin Sudan Liberation Movement (SLM) da kuma Justice and Equality Movement (JEM) karkashin jagorancin Abdulwahid Muhammad Nour da Ibrahim Khalil, da kuma gwamnatin Khartoum a gefe guda karkashin Jagorancin Shugaba Bashir, hakika sakamakon yayi muni ainun. Sannan kuma a daya bangaren ga yakin da ake kafsawa tsakanin Kudancin Sudan da kuma Arewaci, a dan haka gwamnatin Khartoum taga babu abinda ya kamata kamar neman hanyoyin da za'a warware bakin zaren wadannan matsaloli da suka yi mata daurin gwarmai. Gwamnatin Bashir ta fara yunkurin sasantawa akan Tebur da  Sudan People’s Liberation Movement/Army (SPLM/A) dan ta kawo karshen fadan da yake tsakaninsu da mutanan Kudanci. Bayan da gwamnatin Khartoum ta nemi shugabannin yankin Kudanci wato su John Garang a sasanta dan neman samun zaman lafiya, wannan abin bai yiwa kasashen yamma dadi ba domin ko shakka babu suna cin kasuwarsu da wannan dogon rikici na kudu da Arewa. Ba tare da kai ruwa rana ba John Garang ya amince da bukataun gwamnatin Khartoum na samun zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.

Me zai faru bayan da John Garang ya amince da sasantawa? Wasu bayanai sunce wasu daga cikin kasashen da suke makwabtaka da Yankin Kudancin Sudan karkashin zugar kasashen Turai sun zuga Garang akan kada ya amince da gwamnatin Khartoum dan sasanta wannan rikici, amma Mista Garang yayi kunnen uwar shegu inda ya kama hanya ya nufi Khartoum ya sadu da Shugab Bashir dan shirya yadda za'a fara tattaunawa inda aka amince da Naivasha ta kasar Kenya kafin daga bisani a koma Adis Ababa tare da sa idon su Thabo Mbeki na Afurka ta kudu. Dawa tayi nama an kuma samu warware matsalolin da sukayi tarnaki sosai, inda aka cimma yarjejeniyar baiwa Garang mukamin mataimakin shugaban kasa na daya da kuma Dr Tabita Vitrus a matsayin Ministar lafiya da kuma mukaman wasu ministoci.

Kwatsam sai aka wayi gari cewar John Garang ya hau wani jirgin sama mallakar Kudancin Sudan ya kuma rikito a yankin na kudancin Sudan. Hakika wannan al'amari ya girgiza gwamnatin Khartoum, dan gudun zargin mara tushe, amma babban abinda ya karfafa musu guiwa shine Garang ya mutu ba'a yankin Arewacin Sudan ba, kuma ba'a cikin jirgin gwamnatin Khartoum ba, kamar dai mutuwar su Yakowa da Azazi da suka mutu a can kudancin Najeriya ba a Arewa ba balle a zargi Boko Haram da cewar sune suka tunkudo jirgin nasu. Dan haka duk wata kofa ta zargin Gwamnatin Shugaba Bashir a rufe take! Rahotannin Asiri kuma sun tabbatar da cewar Amerika na da hannu wajen kisan Garang a cikin jirgin da ya fadi da shi, sakamakon amincewar da yayi na a sulhuntawa da gwamnatin Bashir, dan haka wannan ta sanya dole a sauya wani salon tunda wannan shirin ya kwade musu. Dan haka har yau dinnan da Amerika da sauran munafukan da suke tare da Garang a wancan lokacin babu wanda ya ke bincikar ya akayi Garang ya fado a cikin jirgin da yayi sanadiyar halakarsa, saboda su suka aika kayansu lahira suka kashe suka binne wannan al'amari, ita kuma gwamnatin Khartoum daman gaba ta kaita gobarar titi.

Sannan kuma, a daya bangaren kuma na yankin Dafur, Abdulwahid Muhammad Nour ya fahimci cewar lallai makirci aka shirya musu domin su yaki gwamnatin Khartoum, musamman ganin abinda ya faru da Garang. Dan haka ne suka yi karatun ta nutsu suka ga cewar lallai ashe su ba gwamnatin Khartoum suke yaka ba, kansu suke kashewa domin duk fadan da suke yi da gwamnati a iyakar Dafur suke yi gidajensu suke konawa, haka kuma mutanansu suke kashewa, saura da me! Kawai sai suma suka nemi sulhuntawa da gwamnati, suka yi fatali da Ghaddafi da kuma zugar kasashen turawa. Anan kuma batun larabawan Janjaweed ya taso, da kuma batun shigar Majalisar dinkin duniya inda suka kafa United Nation Mission in Dafur (UNAMID), da kuma batun su Liou Morino O'campo, da kuma baun kama Bashir da laifukan yaki da cin zarafin Bil-Adama a Dafur. . . . . . . Zan cigaba Insha Allah.

Yasir Ramadan Gwale.
18-07-2013

No comments:

Post a Comment