Sunday, July 14, 2013

ZIYARAR PASTOR TB JOSHUA: AL-MUSTAPHA YA 'BATA RAWARSA DA TSALLE


ZIYARAR PASTOR TB JOSHUA: AL-MUSTAPHA YA 'BATA RAWARSA DA TSALLE

A jiya rahotanni sun nuna cewa Manjo Hamza Al-Mustapha ya kai ziyara zuwa ga Pastor TB Joshua. Al-Mustapha yana da iko da 'yancin ya kai ziyara ga duk wanda yaga dama a matsayinsa na me 'yancin yin haka. BAn san mece ma'anar wannan ziyara ba! Amma shakka babu ziyararsa ga Pastor TB Joshua babban abin Allahwadai ne, eh Allahwadai! Kasancewar Pastor Joshua a matsayin Mutumin da ya fara kaiwa ziyara wannan ya sanya ziyarar ta zama Mummuna. Ga zatona Hamza Al-Mustpaha zai fara kai ziyara Masallaci ne yayi Sallah raka'a biyu domin nuna godiya ga Ubangiji bisa kubutar da shi da yayi daga wannan kangi da ya samu kansa a ciki, kamar yadda yin hakan Sunnah ne a duk lokacin da manzon Allah ya dawo daga tafiya ko wani al'amari yakan fara yada zango a Masallaci ne ya yi sallah.

A lokacin da aka bayar da sanarwar cewar Olushegun Mimiko ne ya lashe zaben Gwamnan Jihar Ondo abin da ya fara yi shine garzayawa Coci domin yin sujjadar godiya ga ubangiji ga nasarar da ya samu kamar yadda aka ruwaito, haka shima Adams Oshiomhole sai da ya fara zuwa Coci don yin addu'a, wanda hakan a garesu bin addini ne sau da kafa. Haka kuma, Al-Mustapha dan bai je masallaci ba, ba laifi yayi ba, kuma ba zunubi ya aikata ba, amma dai zabin Pastor Joshua a matsayin mutumin da ya fara ziyarta ya sanya muka yi tir da wannan ziyara tasa.

Waye Pastor TB Joshua? Wannan mutumin pastor Joshua wani irin hatsabibin malamin addinin kirista ne, da zaka iya kwatantashi da "Malam Gobe Da Nisa" kamar yadda Bahaushe kan kwatantan Malamai masu siddabaru da dabarce-dabarce. Domin Joshua yayi ikirarin cewar shifa Allah ne ya aiko shi domin yin wa'azin Addinin Kirista har yake bayyana asalin haihuwarsama ta zo da Mu'ujiza ne a cewarsa. Bayaga wadannan karayrayi da wannan Pastor yake yi, yana yin wasu abubuwa da suka saba da hankali kuma suka yi kama da tsafe-tsafe a harkar wa'azinsa inda aka ce yana warkar da masu cutar tabin hankali da kuturta da makanta da gurguntaka da sauransu, wanda wannan ne ya mayar da shi daya daga cikin fitattun masu wa'azi a Nahiyar Afurka. Bugu da kari lokacin da Al-Mustapha ya kaiwa Joshua ziyara sai da shi Joshuan ya fada cewar daman ya gayawa Al-Mustapha a can baya cewa wannan abin zai same shi kuma gashi ya tabbata, inda yake kara tabbatar da kansa a matsayin wai masanin fake! 

Haka kuma, su Joshua nanna tare da wasu malaman kiristoci suka so kawo wani mutum mai wa'azi Bajamushe daga Kasar Jamus da ake kira Ryan Hard Banky zuwa Kano a shekarar 1992 domin ya zo yayi wa'azin da zai dinga kama hannun guragu su fara tafiya ya kuma shafa idanun Makafi su bude da dai sauran tsafe-tsafe banda Allah ya sa anyi yunkurin da ya sanya wannan gayya bata samu nasara ba a lokacin da Allah ne kadai yasan wadan da zasu yi ridda daga cikin al'ummarmu.

A takaice irin wannan hatsabibin Mutum ace shine mutum na farko da Hamza Al-Mustapha zai fara ziyarta ya kyale matarsa da 'yan 'yansa da suka fi kowa kishirwar ganinsa! Lallai wannan babban abin takaici ne matuqa. Ina fatan Allah ya yafe masa kurakuransa ya kuma sa abinda ya sameshi ya zama kaffara a gareshi ya shiryeshi ya shiryemu baki daya. Ina masa barka da sauka Kano.

Yasir Ramadan Gwale.
14-07-2013


No comments:

Post a Comment