Sunday, July 28, 2013

MARTANI GA MASU ADAWA DA SANATA YARIMA DANGANE DA AUREN YARA MASU KANAN SHEKARU




MARTANI GA MASU ADAWA DA SANATA YARIMA DANGANE DA AUREN YARA MASU KANAN SHEKARU


Wannan batu da ya dauki hankalin kusan galibin kafafen yada labarai na gida  da na kasashen waje, da kuma musamman shafukan Internet a`yan kwanakin da suka gabata, wato batun auren nan da suke kira “Early Marriage” a turance, Sanata Yarima shine kan gaba wajen tattauna wannan batu, duk wani shakiyyi ko wata shakiyyiya da suka tashi yin batun akan wannan al’amari suna kawo Sanata Yarima ne a zaman jigon tattaunawarsu, ba dan komai ba sai dan shi Sanata Yarima ya auri  wata yarinya ‘yar asalin kasar Masar mai shekaru sha-uku a shekarun da suka gabata. Gaskiya abin bai ba ni mamaki ba da naga yadda ake ta kwarmato akan wannan batu, daman haka Sha’anin Shaidan yake duk da cewa ana azumi yana can a daure, amma waliyyansa da muke tare da suna nan suna rage masa aiki kafin fitowarsa.
Shi dai aure a shari’ar musulunci yana halatta ne a yayin da waliyyan yarinya da waliyan  yaro suka amince su daurawa ‘ya`yansu aure a gaban shaidu.  Ko da mutum uku ne wannan aure ya kullu. Dalilin da shariah ta halatta aure shi ne domin a kare maza da mata daga afkawa makarantar shaidan wato ka zakkewa matar da ba halalinka ba ce.  Aure shi ne yake hallata maka mace ko ya harantamaka ita. shi aure idan a ka yi shi ma’ana da yardar  iyaye da kuma amintar ma’auratan   ya yi koda kuwa shekarun ma’auratan nawane. Aure garkuwa ne.

Dangane da yamadidin da ake ta yi da Sanata Yarima, shi dai musulmi ne kuma ya yi imani musulunci shi ne addininsa, kuma wannan addini da  ya yi imani da shi Musulunci bai haramta masa wannan aure ba, babu kuma inda Musulunci ya kayyade Shekarun Ma’aurata. Kuma shi sha’anin Aure na dauka ya shafi wanda zai aura ne da kuma wadda za’a aura tare da waliyyansu! A dan haka meye wani zai daga hankalinsa akan sha’anin batun auren wasu da bashi da iko akansu. Tunda ba ‘yarka ko uwarka aka ce za’a aura ba me ya sa mutum zai daga hankalinsa har ya dinga aibanta Musulumi akan wannan batu.

Kuma ta inda za ka san cewa wadannan mutane kururuwar iblis suke yi, tare da daurewa karya gindi da neman mayar da halal ta zama haram, da kuma Haramta Halal, yara nawa wadanda ake kira “under age” suke yin karuwanci a manya da kananan Otal-otal a Najeriya, da tituna da lunguna da gidajen gonaki da mashayai?  Ba’a taba cewa yau ga doka da ta hana karuwanci da kananan yara ba,  Sai aure da aka yi shi bisa  shari`a da yardar iyaye da shaidu? Sannan ne za’a bijiro da batun cewa yara kananan suna da hakkin a kare musu ‘yancinsu, shin wane ‘yanci ne ya wuce wanda mace ta samu a gidan mijinta?

Idan sun tashi yin kwaskwarima sai su ce yara suna da damar yin karatun Boko kafin suyi aure. Kaga inda shaidancin wadannan rubabbun mutane da Shaidan ya riga ya gama yi musu huduba irin tasa ya ke, kuma turawa suka sauya musu akalar tunani da hange, ta yadda basa iya yin wani tunani sai da kwakwalwar bature, gasu dai a zahiri bakaken mutane ne, amma tunanin nasu ba na bakin mutum bane, tunani da Lenin suka riga suka dasa a cikin kwanyarsu mai cike da dattin da hangen nesa. Wasu daga cikin Jahilan irin wadannan mutane har kutsawa suke cikin ilimin addinin Musulunci domin kawai su baiwa son zuciyarsu kariya.

Wasu da nake bibiyar abinda suke fada suna neman su kafirta kansu domin kare kururuwar IBLIS. Domin wasu da suke tunanin a zatonsu sun san addinin Musulunci kamar yadda suka san Turanci, sai su ce wai Manzon Allah ya Auri Nana-Aisha (Allah ya yarda da ita) a shekaru 9, amma kuma wai shi manzon Allah ai ya aurar da diyarsa Nana-Fadima (Allah ya kara yarda a gareta) da cewa tana shekaru 18 ya aurar da ita! Kaga anan gabar ne mutum zai kafirta kansa, domin a kaikaice suna son su ce Manzon Allah SAW ya auri Nana-Aisha a shekaru 9 amma kuma shi ya aurar da diyarsa a shekaru 18! Wallahi duk wanda ya zargi Manzon Allah ko waye shi ya kafirta ya sani ko bai sani ba.

Wani jahili dakiki da yake son nunawa duniya cewar shima yana da Ilimin addini tunda shi Musulmi ne. Wai yana neman da’ifanta Hadisin da yake cikin Bukhari. Shin yana da hankali ma kuwa? Ya san wane littafi ne Bukhari har da yake neman ya nuna cewa Hadisin Bukhari bai inganta ba. Ko kuwa kawai saboda addini bashi da gata ko wane dan tasha da yaje yake shirmensa da sunan wai shi “Activist” zai zo yana yiwa kansa tsirara a bainar jama’a, da sunan shi masani ne. To wallahi a hir dinku, da Magana akan abinda kuka jahilta. Wai cewa aka yi dole mu din sai mun zama Turawa ne, waye yace musu shi bature gaskiya gareshi da duk abinda ya fada kamar a Lauhul Mahfuz ya kwafo? Kazamai dattin al’ummar wannan zamanin har sune zasu dinga dora irin wadannan mutane akan wani mummunan gwadabe suna kidifiri da ganin cewa sune wayayyu sune suka iya lankwasa harshe wajen Magana, dan haka dukkan ra’ayinsu da tunaninsu shine ya dace da zamani. Lallai mutum zai ci ubansa nan gaba!

Wadannan miyagun azzaluman suna ina kasashen Turai suke ta batun sai ‘yan Majalisa sun zartar da dokar da zata bayar da damar Namiji ya auri namiji ko mace ta auri mace, suna ina basu fito sun fike alkalumansu sun yaki wannan batu ba, a’a sai batun Namiji ya auri mace bisa Sadaki da Shaidu shine zai zama abinda alkalaminsu zai fi iya watsatstsake akansa. Haka kuma, galibin wadannan mutane da suke yin wannan yamadidi musamman matan da suke zakewa akan batun da yawansu ba Aure garesu ba, sun shantakar da rayuwar da y a kamata su yi a gidan mazajensu a maho, shine suke bakin cikin kada wasu su yi aure, amma idan karuwanci ne sai su ce eh yara suna da ‘yancin zabin abinda ya fi dacewa da su. To Wallahi, ahir, kuma mun ja layi da duk wani dan iska marar kunya ko waye ubansa, da wata da ta kasa zaman aure!

Dan haka, sune da suke fama da kuncin tunani suke zaton cewar sai yarinya ta gama karatu sannan tayi aure. Su je Kano su tambayi wacece AMINA ISYAKU KIRU tun tana shekara 9 zuwa 10 aka yi mata aure, a dakin mijinta ta fara Primary a nan tayi karatu ta wuce har jami’ah kuma ta karanta Likintanci har ta zama kwamashiniyar Lafiya a Kano lokacin Marigayi Abubakar Rimi, idan ba su da wannan labarin su zo mu habarta musu, dan su sani rayuwar aure inganta karatu take yi, ta sa yarinya ta nutsu ta dinga fahimtar karatu yadda ya kamata.

A dan haka Nan gaba ma sai mun dinga sanya shekarun yarinyar da zamu yiwa aure a jikin katin gayyata domin ‘yan bakin ciki idan sun gani su mutu dan damuwa.

Yasir Ramadan Gwale
23-07-2013

No comments:

Post a Comment