Monday, July 1, 2013

SHIRIN GWAMNATIN TARAYA NA YOU WIN, MUHIMMANCIN SA A GARE MU.


SHIRIN GWAMNATIN TARAYA NA YOU WIN, MUHIMMANCIN SA A GARE MU.

A shekara ta 2011 ne gwamnatin kasarnan tare da ma'aikatun kudi, mata, sadarwa, kula da cigaban matasa na taraya,da wani ofishin tallafi na kasar Buritaniya (DFID) da wasu bankuna irin su First bank, UBA, Access Bank, GTB, Stanbic IBTC Bank, da kuma wasu da ban lissafo ba suka kirkiro gasar YOU WIN. An ajiye makudan kudi domin matasan Najeriya su kirkiro wa kansu sanao’i ba tare da jiran aiki daga hannun kowa ba.

Masu iya shiga gasar dai ana neman yan asalin kasar Najeriya ne, matasa masu shekaru tsakanin shekara 18 da 45,Masu takardar shaidar yin makarantar gaba da sakandari.

Ita kuma gasar kanta, abu na farko da ake nema shi ne mutum ya tsara kasuwanci, ko noma ko kuma duk wata hanyar neman kudi ta hanyar halal da zai kawatar ya ja hankalin alkalen gasar. Misali idan mutum yana sha’awar noma menene mutum zai yi a cikin tsarin nomansa da ya fita daban ko ya zama abun a zo a gani a cikin harkar noman na sa da zai sa takardar gasar tasa ta yi fice a cikin tarin takardun da aka aika da ga duk sauran sassan kasar nan.

Abu na biyu da alkalan gasar suke bukatar gani shi ne kirkiro aiki, ba wai za a ba wa mutum kudin jarin shi kadai zai yi aiki ba, a’a ana so a kirkiro dubunnan aiyyuka ne ta hannun wadan da suka ci gasar nan.

Na uku kuma shi ne samun kudi da falala daga wannan hanyar neman kudin, ba amfani a kirkiro abun da ba zai kawo kudi ba ,saboda haka dole ne mutum ya nuna ce wa a tsarin da ya biyo kudi za su samu masu kauri ta halartacciyar hanya.

Na yi muka bayanin cewa You win dai gasa ce, to me a ke samu idan aka shiga gasar aka kuma ci? Na daya akwai koyarwa da mutum zai samu na yadda zai tafiyar da neman kudinsa, na biyu kuma a cikin takardun da za a cika a aika ta yanar gizo mutum zai fadi nawa ya ke buka a matsayin kudin jari tsakanin naira miliyan daya zuwa naira miliyan goma. Idan mutum ya yi bayanai masu gamsarwa a cikin gwaji na daya za a ba shi damar shiga sashe na biyu inda a nan ne zai yi bayani dalla dalla. A sashi na biyu a na daukan mutum 6000 ne kacal.

Wadannan mutum 6000 za a sa su, su je su yi wani kwas na kwana biyu a kan hanyoyin neman kudi da inganta neman kudinsu,wanan kwas din na cin yini biyu. Bayan wannan ne sai a cika sashe na biyu ta yanar gizo a aika. Ana ba da a’kalla wata daya kafin a rufe gasar dan a ba wa mutane dama su yi kyakkyawan nazari da bincike dan kar a samu kuskure na bayani da lissafin duk abubuwan da za su nema ko su bukata. Duk bayanin wannan gasar ana iya samu a www.youwin.org.ng .Ya zama dole kuma wadanda suka shiga gasar su rika duba wannan shafin yanar gizon da kuma imel dinsu a kan kari.

Idan aka rufe karbar takardun ta yanar gizo zai dauki kamar wata guda wanda a lokacin ne alkalen gasar da su ke a kasar ingila za su duba su zabe mutum 1200 a matsayin wadanda suka lashe wannan gasa. Abun da ya bawa mutane da dama mamaki da wannan gasa shi ne ba sai ka san kowa a gwamnati ba, iyakaci kwazon mutum shi zai sa ya ci.

A shekara ta 2011 an ba wa matasa maza da mata damar su shiga wannan gasa amma sai ya zamanto mata kalilan ne suka shiga. Ganin haka shine ya sa Gwamnati suka ce gasar ta shekara 2012 mata kadai ne za su gwara kai maza su huta. Mata sun fito an fafata an sake tace mutum 1200 har an kira su Abuja birnin taraya dan su ji me ya rage kafin kudaden da suka bukata su shiga hannunsu.

Kudaden nan dai an raba su gida uku ne kuma ana fara ba da kashi goma zuwa ashirin ne daga farko dan mutum ya yi rajistar duk abubuwan da suka kama sanan a kama wajen aiki.

Kashi na biyu kuma na zama kashi arbain izuwa hamsin ne na kudin da za a ba wa mutum, ana bayar wa dan sayen kayan aiki amma sai jami’an gasar sun tabbatar an kashe kudin farko a yadda ya kamata, ana samunsa Kamar wata uku bayan karbar kudin farko.

Kashi na uku na karshe wanda ake ba da shi bayan wata uku da karbar kashi na biyu shi ne kashi na karshe wanda za a shiga aiki tukuru da su. A cikin takardar da mutum ya rubuta na gasar zai yi bayanin nawa ya ke sa ran zai samu a kowane wata, a kan haka su ma jami’an kula da gasar za su fadi nawa mutum yakamata ya samu a matsayin riba kowanne wata. Za su kuma fadi ma’aikata nawa mutum zai dauka.

You win ba bashi bane, gasa ce kudin da mutum zai samu shine sakamakon gasar, ko mu ce kyautar da mutum ya ci. Bambancin You win da sauran gasa ita ce koyarwar da mutum za a yi masa da kuma kaidojin da za a shimfida masa. Ama fa wani hanzari ba gudu ba duk mai tunanin zai karbi kudin You win ya kwanta a kansu bai yi amfani da su ba zai sha mamaki domin kan ya ankara zai ga jami’an tsaro har gida. Kudin You win ba mai ciwuwa ba ne haka sasakai. Hanya daya da mutum zai mori kudin You win shi ne ya yi abun da a ka ba shi ya yi da su.

Muna sa rai da cewa wannan shekarar ma za a bude gasar a cikin watan tara saboda haka yan uwa sai a fara shiri. Dan haka domin  neman karin bayani akan duk wani abu da ya shige maka duhu dan gane da YOU WIN sai ka aiko imel zuwa saadatuh@live.com 

Yakamata a aika wa yan uwa da abokan arziki da wannan labari domin mu samu mu ceto matasan mu daga cikin kangin talauci da rashin abun yi.Allah ya bad a sa’a ya yi mana jagora Wannan dama ce ga maza da mata gaba daya musamman mu 'yan ARewa domin wallahi anyi mana fintinkau sosai akan cin moriyar wanna tsari.

6 comments:

  1. This comment has been removed by the author.

    ReplyDelete
  2. This comment has been removed by the author.

    ReplyDelete
  3. What a wonderful love story was this that is full of tears and amazement, love is sweet most especially you got the rightfull person who could love you wholeheartedly not because of your wealth or any position been held by you either governmentaly,in private sector or in society, this love story might be worst than Romeo and Juliet love story but never worst than mine and Kushii baloch. I really sympathize to laila and Qais.

    ReplyDelete
  4. Ina sonki khadeejah na Kamar yadda majnun yakeson lailarsa

    ReplyDelete
  5. Ina sonki khadeejah Kamar yadda majnun yakeson lailarsa

    ReplyDelete