Sunday, July 28, 2013

HATTARA DAI ‘YAN KAROTA




HATTARA DAI ‘YAN KAROTA

Kusan a kowanne lokaci zaka ji jama’a na yawan korafe-korafe akan ‘Yan KAROTA, na irin cin-zarafi da wulakanta jama’a da muzgunawa da suke yi a kan titunan cikin binin Kano da kewaye, baya ga kuma cin-tarar da ta shige hankali da hukumar Karotan ke yi ga masu ababen hawa. Lallai ya kamata Hukumar Karota su sani cewar jihar Kano jiha ce ta dukkan al’ummar Arewacin Najeriya dama sauran masu zuwa yin fatauci su koma a kullum ranar Allah daga sassa da dama na Najeriya da wasu daga cikin kasashe makwabtan Najeriya. Yana da kyau Karota su sani gwamnatin Kano bata kafa su ba dan su ci zarafin al’umma ba, a’a sai dan su kawo gyara da tsabtace al’amura da suka danganci harkar sufuri da harkar futo a jihar KANO, shi kuma aiki irin nasu yana bukatar hakuri da taka-tsan-tsan da kiyaye al-farmar mutanen KANO da bakinsu.

Wasu rahotanni na nuna cewar da yawan bakin da suke shigowa KANO dan yin fatauci ko safarar hajoji suna kaurcewa saboda tsoran wulakancin ‘Yan Karota. Ko shakka babu, indai wannan batu gaskiya ne, to akwai mummunan koma baya a harkar kasuwanci a jihar Kano, domin kasancewar Jallah-Babbar-Hausa cibiya ce ta kasuwanci ga dukkan kasashen Arewa da makwabtanmu kamar Nijar da Kamaru da Chadi, bama fatan ace mun rasa bakinmu ‘yan kasuwa ko kadan, Bil-hasalima kullum fatanmu wadan da basu zo ba ma su zo dan yin kasuwanci a jiharmu Me Albarka. Haka kuma, bayanai sun tabbatar da cewar Karota suna yankawa mutane tara mai yawan gaske da ta wuce kima, bayanai sun nuna cewar ana yankawa mutane tara tun daga dubu dari har zuwa miliyan daya, wanda wannan ko shakka babu akwai zalunci da kuma tsanantawa a cikinsa! Haka kuma, akan tursasawa mutane biyan tara ba tare da ambasu rasid’I ba, sai dai kawai a basu “teller” su je banki su biya, idan mutane sun bukaci rasid’ sai ace masa babu, wannan kam indai haka abin yake zalunci ne tsabage, kuma Allah ba zai kyale ba ko da wanda aka zalunta ya kyale.

Da farko, Anan, muna kira ga al’umma da su kiyaye da bin dokoki da kuma ka’idojin da hukumomi suka gindaya. Lallai bin doka da Oda shine cikar wayewa da kuma sanin ya kamata da ciwon kai. Ba dai-dai bane jama’a su yiwa mota karama lodin kayan da ya huce hankali alhali kuma doguwar tafiya za’a yi, irin wannan ke sanyawa abin Allah ya kiyaye Hatsari ya auku sai kaji anyi mummunar Asara, lallai ayi kokarin kiyayewa da bin tsari da rashin makare kananan motoci da lodin da ya wuce kima.

Haka kuma, muna kira ga mai girma Gwamnan Kano Engr. Rabiu Musa Kwankwaso, da cewa lallai gwamnati ta binciki yawan korafe-korafen da jama’a suke yi akan ‘yan Karota, akan muzgunawa da tsanantawa wani lokacima har da cin zarafi da suke yiwa jama’a, lallai wannan hakkin kune Maigirma Gwamna wajen kare hakkin jama’ar da kuke shugabanta da kuma tabbatar da abinda ya fi zama maslahawa wajen habakar kasuwancin jihar Kano da walwalar al’ummar jihar Kano da bakinta.

Daga karshe zan sake jaddada kira ga Shugabannin Hukumar Karota da suji tsoron Allah a cikin ayyukansu, su sani aikinsu baya nufin cin-zarafin mutane ko muzguna musu ko da kuwa sun aikata laifi, lallai kyakykyawar Mu’alama itace Musulunci inji Manzon Allah.

Allah ya taimaki jihar Kano ya kara habaka tattalin Arzikinmu da Arewa da kuma Najeriya baki daya.

Yasir Ramadan Gwale
18-07-2013

1 comment:

  1. A gaskiya ''IDAN BERA YANA DA SATA TO DADDAWAMA TANA DA WARI'' Rashin sanin ka'idodin tuki shine babban dalilinda ya jawo kirkirar hukumar Karota, abin takaicine kwarai mutane suna mayarda kansu kamar dabbobi, kowa so yake a barshi yayi abinda yaga dama, akwai littafi musamman akan yadda ka'idodin tuki suke amma zaka samu 90%100 na masu tuki a kasarnan basu san akwai littafinba ballantana su karantashi. hakan yasa zaka ga mutane da yawa basu san menene koriya da yalo da ja yake nufi ba a lokacinda suka zo mahadar hanya, sannan ga masifar gaggawa da mutane suke da ita, ga son siye da siyarwa akan kolta ba gefen titi ba, wadannan da wasu abubuwa suna daga dalilai da suke jawo kafa hukumar karota, ni a matsayina na wanda wadannan abubuwa suke damu ina goyon bayan wannan hukuma

    ReplyDelete