Monday, December 31, 2012

ME YAKE FARUWA A KANGWAYE NE?


Wata rana wani Bawan Allah da yake gina gidansa, ya gayyaceni akan na raka shi gewayar ganin gidan da yake ginawa. Haka kuwa aka yi, domin mun je a wani irin lumshi da kowa zai so ya danyi tattaki a cikinsa, ba jimawa muka zo unguwar da gidan yake, kasancewar wajen sabon wajene dukkan gidajan da suke kan layin sabbin gidaje ne da ake ginawa, wannan ta sanya muka tarar da tsibi tsibin yashi da duwatsu da kan-kura akan layin, dole ta sanya muka ajjiye mota daga nesa muka taka sayyadarmu domin karasawa gidan. 

Isarmu kofar gidan ke da wuya na kalli gidan nayiwa maigidan murna kasancewar gidan ya kasaita bayan kasancewarsa katafare harda masallaci a jikin gidan da ake ginawa tare. Mai gida ya shige cikin gidansa kai tsaye domin yaga yadda ake gini, Ni kuma na nufi dan-karamin masallacin da ke jikin gidan wanda ake ginawa, shiga cikin masallaci na hangi wani abu da na kasa gasgata ganina da yake daga nesa na hango.

Ina shiga cikin harabar masallacin ta kofar kudu kawai sai naga wani baho madaidaici dauke da wasu kananan kwalaben ruwa da wasu jike-jike a ciki. Abinda ya fara zuwa Raina shine wannan irin kayan masu tallan maganin gargajiya ne da suke shigowa cikin birni daga Panshekara, tsammanina ko na tsintuwa ne, ban damu ba na daga kaina sama daga bakin kofa ina kallon gini, can sai naji sukur-sukur alamar ana motsi, duk da haka ban kawo wani abu mara kyau na faruwa ba, kawai sai na shiga domin ganin meye yake motsi, cikin mamaki na hangi bayan mutum a inda Liman yake tsayawa, na kalli mutumin da alama yana yin wani abu cikin gaggawa, na kara matsawa sosai, sai na hangi wani mutum mai matsakaitan shekaru yana sauri yana daura tazaugen wandonsa kansa babu hula, da alamar a rikice yake, bayansa kuma wata yarinya na hanga tana kokarin gyara kayan jikinta.

Na tsaya ina mamakin abinda idona ya gani, yarinyar nan ta tashi cikin hanzari ta dauki wannan baho ta kinkima tayi waje. Banyi magana ba, wannan mutumin kuwa ya zube a gabana yana rokona dan Allah malam ka rufa min asiri kada ka gayawa Alhaji ka ganni! Nikam Ina tsaye na kasa magana. Mutumin nan da yaga ban kulashi ba, ya leka waje bai hangi kowaba, har ya fita sai ya dawo ya dauki hularsa, kafin ya dauki hular tuni ni kuma na fice daga cikin masallacin.

Na shiga cikin gidan ina mai mamakin abinda na gani, Mutumin nan hankalinsa ya tashi sosai, domin yana yimun wani irin kallo na intausaya masa. Haka dai har muka gama ganin ginin nan bashi da kuzari, yana tsoron kada na fadi abun da na gani. Hakika abinda na gani ya tunasar da ni abubuwa da yawa da na sha-ji ana fade cewa ana yin Lalata da yara 'yan talle a cikin kangwaye. Lallai acikin masu yin sana'ar gini akwai mutanan kirki kuma akwai na banza kamar yadda kowanne fannin rayuwa ake samu. Allah ya shirya ya karemu da mugun-ji da mugun-gani. 

1 comment:

  1. to Allah Ya kare mu daga sharrin kawunanmu da na shaydan.
    Hakika ya kamata duk masu kangwaye suyi kokarin ginesu don wallahi marasa gaskiya sunyi yawa, kusan ko ina akwaisu. Saboda haka, abin da baka zataba sai kaga ya faru.

    ReplyDelete