Tuesday, December 4, 2012

ME KA SANI DAN-GANE DA HALITTAR RAKUMI


ME KA SANI DAN-GANE DA HALITTAR RAKUMI

Rakumi daya ne daga cikin dabbobin ni’ima guda huda da ALLAH ya yi yiwa musulmi nuni izuwa garesu domin yin lallai ko hadaya. Rakumi wata dabbace da ALLAH ya halitta ba domin kawai a yanka a ci ba, rakumi kan yiwa mutane hidima da dawainiya, ALLAH ya halicci mafiya yawan rakuma a yanki mai cike da sahara, yanki mai zafin rana. Yankin gabas ta tsakiya kusan nanne madinar Rakuma domin ALLAH ya halicci miliyoyin rakuma a wannan yanki haka kuma yankin Arewa wacin Afurka nanma akwai rakuma masu yawan gaske, kasar Somaliya kusan ita ce kasar da tafi kowace kasa yawan rakuma a yankin da ake kira kahon Afurka. Haka kuma, akwai wasu miliyoyin rakuman a yankin Asiya mai nisa wato kasashen Azarbaijan da Tajikistan da Turkuminstan da Uzbakistan da Kyrgistan suma suna da tarin rakuma masu yawan gaske, daga nan kuma sai Arewaci da kudancin Amerika wanda rakumansu kalilan ne sosai.

Rakuman da suke a yankin Sahara sun sha bamban da rakuman da suke a yankin Asiya mai nisa musamman a wadancan kasashen da muka lissafa. Rakumansu ba kamar sauran rakuma bane na gabas ta tsakiya ko Arewacin Afurka, rakuma a yankin suna da yalwar gashi mai yawa kasancewar yanki ne da suke da yanayi na dusar kankara mai yawan gaske, dan haka mafiya yawan dabbobinsu suna da gashi mai yawa a jikinsu, haka suma rakumansu suke. Amma bayananmu zasu fi karkata ne zuwa ga rakuman da suke rayuwa cikin sahara.

Rakumi yana iya yin gudu na tafiyar kilomita 65 a cikin awa guda ba tare da ya gajiya ba. ALLAH mai girma da daukaka ya sanyawa rakumi juriya wajen tafiya, domin a mafi yawancin lokuta sai dai mai jan rakumi ya gaji ya huta amma ba dai rakumin ya gaji ba. Haka kuma, duk da irin wannan juriya ta rakumi sai ya dauki lokaci bai sha-ruwa ba, domin rakumi yakan iya kai watanni uku ba tare da ya sha ruwa ba, kasancewar ALLAH ya halitta masa wani tanki a cikinsa wanda yake adana ruwa. Rakumi yakan sha ruwa lita 200 kimamin galan 53 a cikin mintuna uku, rakumi na iya shan ruwan da ya kai lita 600 a lokaci guda.

ALLAH subhanahuwata ala ya halicci wasu dabbobi da hikimomi da baiwa mai yawan gaske, kamar yadda ya halicci kare zai iya sansano wani abu da aka boye ko gano inda aka boye shi, haka shima rakumi, idan yana bukatar ruwa yana iya sansano inda ruwa yake daga kimanin nisan mita 200, kamar yadda Shamuwa kan sansano zuwan damina, a wasu garuruwan da dama alamun zuwan ruwan sama ko damina shine ganin Shamuwa tana ya yawo domin tana jiyo alamar zuwan ruwa. ALLAH buwayi gagara misali.

Duk acikin dabbobin da ALLAH ya halatta cin su Rakumi ne dabbar da yafi kowacce kawaici da kunya da kuma sanin ya kamata. Rakumi yana da ladabi ainun domin yana bin duk umarnin da aka bashi baya kaucewa, kamar yadda duk inda aka aiki jaki zaije ya dawo ba tare da ya tsaya ba, haka shima rakumi yake, sannan yana daga cikin hikimar da ALLAH ya yiwa rakumi baya mantuwa ko da kuwa shekaru nawa zai dauka, rakumi baya manta uwarsa ko ubansa, sannan baya manta ‘yan uwansa ko abokansa, wannan ta sanya ko barbara zaiyi baya yi tare da ‘yan uwansa da suka fito ciki daya, sabanin sauran dabbobi irinsu akuya da rago. Haka kuma, kamar yadda sauran dabbobi irinsu mage suke da sabo da masu su haka shima rakumi yake da sabo da mai, domin sau da yawa rakumi yana yin kewar rabuwa da uban gidansa.

Rakumi kusan a cikin dabbobin da aka halattamana cin-su dan layya ko hadaya yafi kowacce dabba daukan tsawon shekaru a raye, domin rakumi yakan rayu tsawon shekaru daga 40 har zuwa 60. Sannan kuma, rakumi duk da irin jarumtakarsa ALLAH ya sanya kunama tana cin galaba akansa, domin duk cikin halittun ALLAH babu abinda rakumi yake jin tsoron gamuwa da shi kamar kunama, kasancewar kafarsa tana da taushi sosai kamar ta dan-Adam, wannan ta sanya rakumi yana iya hango kunama daga waje mai nisa, kuma muddin ya hangota to ba zai bi wannan hanyar ba.

Kamar yadda muka bayyana cewa Rakumi yana da hakuri sosai, sannan kuma yana da fada sosai idan aka shiga gomarsa. Kusan duk cikin dabbobin da makiyaya suke kiwo rakumi ne kada ba’a dukansa, domin na farko shi yasan ya kamata gwargwadon irin tarbiyyar da mai shi ya bashi, rakumi yana jin magana kamar mutum kuma yana bin dukkan umarnin da aka bashi, dan haka mai kiwon rakuma zai iya yin gaba ya bar rakumansa ya yi musu umarnin su sameshi a waje kaza kuma so sameshi. Rakumi duk mutumin da ya cuceshi sai ya rama komai tsawon lokaci, kuma rakumi yasan Yaro misali idan Yaro ya tsokaneshi baya damuwa kuma baya masa komai.

A dukkan dabbobin da ALLAH ya halitta Rakumi ne kadai dabbar da babu wani abu a jikinsa da bashi da amfani. Bayaga yanka shi da ake a ci nama,  ana amfanuwa da nononsa da fitsarinsa da kashinsa, wannan ya sa rakumi ya yi zarra a cikin dabbobi domin shi fitsarinsa ba najasa bane kuma ba haram bane. Haka kuma, ALLAH ya yi ishara dangane da yin tsinkaye dangane da rayuwar rakumi a cikin al-qur’ani mai tsarki a sura 88 aya ta 17.

Haka kuma, wasu masana sun tabbatar da cewa Rakumi ya taba rayuwa a wannan duniyar a shekaru sama da miliyan hamsin da suka gabata! Tsarki ya tabbata ga ALLAH da ya halicci rakumi, masanan sunce rakuman da suka rayuwa a wancan lokacin girmansu bai wuce na Akuya ba, sannan sun rayuwa a can a wani yankin kudancin Dakota a kasar Amerika kenan.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment