Sunday, December 16, 2012

BAN-KWANA DA MALAM IBRAHIM YAKOWA


BAN-KWANA DA MALAM IBRAHIM YAKOWA

Masu magana suka ce idan an bugi jaki a bugi taiki! Idan zamu fadi magana ta gaskiya akan tsohon gwamnan Kaduna Marigayi Malam Patrick Ibrahim Yakowa lallai mutum ne da ya siffantu da wasu kyawawan dabi'u da wasu halaye na gari. Yakowa tun bayan hawansa gwamnan Kaduna shi da kansa yasan yana da babban kalubale akansa domin ya zama gwamna a jihar da galibin al'umm arta suke da rinjayen Musulmi, dan haka yasan wannan gagarumin kalubale ne akansa.

Yakowa ya yi kokarin gyara siyasarsa da kuma dangantakarsa ko alakarsa da Musulmi. Amma kuma ya tsinci kan-sa a wata tsaka mai wuya, domin ya zama gaba kura baya sayaki. Abu na farko yana kokarin ganin ya samu goyon bayan musulmi masu rinjaye kasancewar jihar kaduna tayi kaurin suna wajen rashin zaman lafiya musamman tsakanin Kiristoci da Musulmi. Da farko Yakowa yayi ta kokarin mika hannunsa ga musulmi domin su yarda da shi a matsayin sabon jagoran jihar, kasancewar irin yanayin da ya kawo shi gwamnan musamman a matsayinsa na sabon zababben gwamna zaiyi wahala a yarda da shi kai tsaye ko lokaci guda.

Sannan kuma ta bangaren 'yan uwansa tsirarun kiristoci da suke ganin nasu ya samu, sai suke masa wani irin kallo na Inuwar giginya. Kalubalen da yakowa ya samu a karon farko shine su tsirarun kiristoci suna masa kallon daman can a cikin Musulmi ya taso tun rayuwarsa, kuma sune abokan mu'amalarsa, dan haka sai ya samu kansa a wani irin yanayi ta yadda 'yan uwansa kiristoci suna masa kallon yana neman juya musu baya a matsayin nasu, sannan kuma musulmi na dari-dari da shi. Amma duk wannan yayi ne domin gyara siyasarsa.

Yakowa yayi kokarin ganin yayi mulki ba tare da nuna wani bambanci na zahiri ba tsakanin Musulmi da Kirista. Kuma kamar yadda aka bayyana shi dan kishin kasa ne da kishin Arewa wannan yabo kam shakka babu anyi masa, kuma biri yayi kama da mutum. Haka Kuma, a yadda yake gudanar da gwamnati hakika yana taka tsantsan wajen ganin bai bata zamansa ko alakarsa da Musulmi ba. Kamar yadda rahotanni suka nuna a aikin hajjin da yagabata Yakowa yayi rawar ganin wajen ganin gwamnatin Kaduna ta taimakawa Alhazan Jihar Kaduna. Hakika idan zamu kalli wadannan halaye dama wasu zamu ga cewa yayi kokari.

Haka kuma wasu suna ganinsa a matsayin macijin sari ka-noke ta yadda yake ta kokarin daddasa 'yan uwansa a manya manyan mukaman gwamnati domin basu dama. Wannan kuma a siyasance a Najeriyyance haka kowanne gwamna yake yi wajen ganin mutunan da zai nada ya nada na-gindinsa ko da kuwa basu cancantaba.

Sai dai a tsarin addinin Musulunci duk wani mutum da ya mutu baiyi Imani da ALLAH da manzonsa ba, haramun ne a roka masa gafara a wajen ALLAH duk kuwa irin alkhairin da ya shuka. Hakika dukkan wani yabo ko suka da za'a yiwa Yakowa a yanzu babu ko daya da zai amfaneshi, dan munyi Imani duk mutumin da ya mutu ba akan hanyar ALLAH ba shakka babu makoma ta munana a gareshi. Anan sai dai mue ALLAH ya tabbatar masa da makomarsa. Haka kuma, Musulmi basa yin murna da wani mutum ya mutu, ko mutum yayi murna ko kada yayi wanda ya mutu ya riga ya mutu. Sannan kuma kowannemu jiran lokaci yake, kamar yadda ALLAH yayi alkawari kowacce Rai sai ta dan-dana dacin mutuwa. ALLAH ya jikan Musulmi.

Ta bangaren Sabon gwamna Malam Ramadan Yero, muna yi masa addu'ah ta fatan alheri ALLAH yayi masa jagoranci ALLAH ya bashi ikon sauke nauyin da yake akansa. Muna kuma yi masa addu'ah ALLAH ya sa ya kasance abin misali wajen yin adalci tsakanin Musulmi da Kirsita a Jihar kaduna. ALLAH ya taimakeshi.

Yasir Ramadan Gwale

No comments:

Post a Comment