Sunday, December 16, 2012

GWAMNA RAMALAN YERO KADA KA BUTULCEWA UBANGIJI


GWAMNA RAMALAN YERO KADA KA BUTULCEWA UBANGIJI

Jiya yuwar haka, baka taba zaton zaka zama gwamna a yau dinna ba, amma ALLAH shine me yadda ya so, yanzu gashi ka zama gwamna. Kafin haka, Rahotanni suna nuna cewa ana ta kokarin tsigeka kafin wannan lokaci, koma dai wanne irin dalili aka bayar dan yin haka, abu mafi ban mamaki shine Yau gashi ka zama gwamna mai cikakken iko. Dan haka kirana a gareka, kada ka yiwa ni'imar ALLAH dubale kamar yadda sauran shugabanni suke yi ta hanyar ganin wayonsu da dabarunsu na iya basu, ko kuma bin ayarin shaidan wajen samu mulki ta kowacce hanya. Ka sani babu ko daya daga cikinsu da ya baka! Mulki na ALLAH ne kuma shine ya baka shi a dai-dai wannan marra, ka sani wani baya iya baiwa wani mulki.

Dan haka kirana a gareka shine kaji tsoron ALLAH wajen tsare gaskiya da amana da yin adalci tsakanin al'ummar da kake shugabanta a jihar kaduna. Shakka babu kazo a cikin wani lokaci mai cike da kalubale, a wannan mawuyacin
 lokaci babu abinda ya kamace ka illa tsayar da adalci tsakanin dukkan bangarorin Musulmi da Kirista na jihar kaduna.

Ka tsaya tsayin daka wajen tabbatar da Adalci tsakanin al'ummarka, duk kuwa irin kalubalen da zaka gamu da shi wajen yin wannan aiki. Shakka babu wasu zasu kalubalanceka ta karkashin kasa wasu kuma zasu yi hakanne ba tare da jin kunyarka ko tsoronka ba. Idan ka kuskura kabi irin waccan hanya ta gurbatattun mutane tabbas zaka kasance mai nadama matuka da gaske, bayan ka butulcewa ni'imar da ALLAH yayi maka.

Lallai kofarka ta kasance a bude ga kowa da kowa wajen sauraran koke-koken jama'a da korafe-korafen su, ciki kuwa harda wannan kafa ta sadarwa ta yanar gizo wajen jin ra'ayoyin jama'a. Sannan kuma ka baiwa mutane damar mika korafinsu gareka kai tsaye ba tare da wani shamaki ba. Ka yi kokari matuka wajen kaucewa duk wani abu da zai sa ka iya aikata rashin gaskiya ko rashin adalci a tsakanin al'ummarka. Kada ka bari a rabaka da masu fada maka gaskiya, kada ka duba masu fada maka gaskiya ka kalli abin da suke fada, duk wani abu da zai sa ka samu nasara wajen tafiyar da gaskiya da Adalci ka karbeshi ko da kuwa daga hannun wa yake. ALLAH ya yi maka Jagoranci.

No comments:

Post a Comment