Wednesday, December 5, 2012

RISALA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNA: Engr (Dr.) Rabiu Musa Kwankwaso FNSE


RISALA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNA: Engr (Dr.) Rabiu Musa Kwankwaso FNSE

Bayan Sallama irin ta addinin musulunci, Assalamu Alaikum, Ya maigirma Gwamna, ina son nayi amfani da wannan damar wajen yabawa tare da jinjina a gareka bisa namijin kokari da gwamantinka ta yi wajen samarwa da yankinmu na Arewa maso yamma jami’a wadda aka radawa sunan yankin, hakika wannan wani babban ci-gaba ne kuma abin a yaba, mun gode maigirma gwman, haka kuma, sauran kwalejojin da aka kirkiro ko ake kan kirkirowa wannanma wani babban al’amari ne kuma abin a yaba, sannan uwa uba, ga dimbin al’ummar kano da aka dauka aka kaisu kasashen da dama domin karo ilimi wannan ma wani muhimmin ci-gabane ya maigirma gwamna muna yabawa tare da fatan alheri. Sannan kuma, dole mu gode tare da yabawa musamman yadda gwamnati ke ci-gaba da kawata cikin birnin kano, da kunna fitulu a manyan tituna, da tsabtace gari, duk wannan abun a gode ne kuma abin a yaba.
Ya maigirma gwamna, Ina mai amfani da wannan damar wajen yin fatan alheri a gareka da kuma gwamnatinka. Hakika Ya maigirma Gwamna wannan wani muhimmin al’amari ne akanka a matsayinka na shugabanmu kuma jagoran jihar kano, ina fatan ALLAH ya sa ka gama da wannan shugabanci lafiya. Ya maigirma gwamna na kira wannan sako nawa zuwa gareka da sunan RISALA wanda asali kalmar larabci ce, wadda take nufin SAKO, ina fata sakona ya isa zuwa gareka cikin aminci.

Ya maigirma gwamna a ranar 21 ga watan Nuwamban da ya gabata, a shafinka na facebook ka saki wani sako kamar haka “Mu duk wata sarauta ta gado muna yinta, amma sarauta ta kale ba ruwanmu da ita, mu duk wani nadi da baka gajeshi ba sunansa TUKUNKUNJI” wannan shine sakon da ya fito daga shafinka a wannan rana, inda kuma ya ja hankalin mutane da yawa. Ya maigirma gwamna, kai shugabane kuma jagora ne na duk al’ummar Jihar kano walau ‘ya ‘yanta ne ko baki, duk mutumin da yake kano karkashin ikonka yake. Ya maigirma Gwamna, hakika wannan magana da ta fito ta shafinka magana ce ta kananan mutane bayan kuma mun san kai ba karamin mutum bane.

Ya maigirma gwamna, duk wani mutumin kano na haliliya yana girmama masarautar kano. Duk wata sarauta da mai martaba sarki ya bayar ga kowa ye, muna kyautata zaton cewa mai martaba sarki ba zai baiwa mutumin banza sarauta ba, haka kuma, duk wata sarauta da wani ke da ita a jihar kano indai masarauta ce ta bashi muna kallon masarauta ne ba shi mai rike da sarautar ba. Ya maigirma gwamna akwai al’amura da yawa a gabanka wadanda ya kamata su dauke maka hankali sama da kankananan maganganu irin wadannan. Ya maigirma Gwamna, dukkan gwamnonin Najeriya 36 kai yayane a garesu domin lokacin da ka zama gwamnan farar hula a zangonka na farko, wasu daga cikinsu ko ritaya daga aikin gwamnati basu yi ba, abin da muke fata, Ya maigirma gwaman, shine ka zame musu alkibla kuma jagora, kamar yadda Jihar kano ta yiwa sauran jihohi zarra a fadin tarayyar Najeriya, haka muke fatan ka yi zarra a tsakanin takwarorinka gwamnaoni.

Ya maigirma gwamna, duk wani mutumin kano burinsa jihar kano ta ci gaba ko da kuwa waye yake rike da akalar gwamnati a jihar kano. Col. Dominc Oneye ba Bahaushe bane karewa ba ma Musulmi bane amma ya bautawa jihar kano da al’ummar jihar kano, haka muke fatan duk wani mutum da zai hidimtawa jihar kano ko waye kuma ko daga ina yake matukar zai kiyaye da yanayinmu da addininmu, Ya maigirma gwamna, hakika muna kyautata maka zaton cewa kai me kishin jihar kano ne da kuma son ci-gabanta da al’ummarta, kuma Alhamdulillah babu abinda zamu ce sai ala-san-barka.

Ya maigirma gwamna, a kwanakin baya kayi wata muhimmiyar magana wadda ta tayar da kura musamman a majalisarku ta gwamnonin Najeriya, wannan magana ta rabon arzikin kasa, da kuma batun man da ake hakowa a cikin teku da kuma man da ake hakowa a tsandauri (off-shore On-shore Dichotomy), Ya maigirma gwamna lallai wannan magana da ka kawo kuma da yawa daga cikin gwamnoni ka motsasu dangane da wannan batu, irinsu muke fatan ji daga bakinka a koda yaushe, domin kare martabar yankin Arewa da al’ummar Hausawa, amma Ya maigirma gwamna, yawan maida martani ga Babban abokinka kuma Amininka tsohon gwamna Malam Dr. Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, wannan ba girmanka bane Ya maigirma gwamna. Malam Shekarau ya yi gwamna a Kano kuma ya bautawa jihar kano tsahon wa’adinsa, fatanmu shine ku kasance abokai kuma aminan juna kasancewar kun hidimtawa al’ummar jihar kano.

Ya maigirma gwamna, a har kullum a rayuwa bama fatan a ce jiya tafi yau, domin wannan shine ma’auni da yake nuna rashin ci-gaba, kullum fatanmu a ce Yau tafi Jiya. Batun da ake ta yawan yi na cewa gwamnatin da ta gabace ka ta Aminika, kayi aikin da bata yi ba a cikin shekaru takwas, wallahi kullum fatanmu shine na-gaba ya fi na baya, idan har kullum zamu ringa cewa na baya yafi na gaba lallai babu ci-gaba, dan haka fatanmu shine gwamnatinka ta yi sama da abinda gwamnatin baya bata yi ba, kamar yadda muke fatan duk gwamnan da zai biyo bayanka ya yi sama da abinda ka yi, wannan shine zai daukaka martaba da kimar jihar kano.
Ya maigirma gwamna, babbar matsalar da take damun al’ummar jihar kano bata wuce matsalar tsaro da zaman zullumi da jama’a suke ciki ba. Ya maigimra gwamna lallai kamar yadda kake da labari kuma ka sani al’umma suna cikin hali na rashin kwanciyar hankali da zaman zullumi wanda yau Takai mutum hatta a cikin gidansa ba shi da kwanciyar hankali kasancewar yana tsoron ko za’a iya jefo masa wani abu da zai halaka shi nan take, Ya maigirma Gwamna nemo hanyar da za’a magance wadannan matsaloli sune abinda suka kamata su daukewa gwamnatinka hankali, ba maganganu irin na hamayya ba, hakika kamar yadda muka sani kuna yin kokari akan haka, fatanmu kuma shine ku kara kokari akan kokarin da kuka yi a baya.

Ya maigirma gwamna, Lallai babban abinda mu al’ummar jihar kano muka dogara da shi shine kasuwanci (saye da sayarwa) lallai makiya da mahassada suna ta yin aiki babu dare babu rana wajen kassara kasuwancinmu, domin yanzu duk kasuwanninmu sun rage lokacin tashi, kasancewar mafiya yawansu matasa ne, masu amfani da kananan ababen hawa, ga kuma dokokin da aka sanya saboda su, lallai ya maigirma gwamna a duba wannan lamari da halin da al’umma suke ciki, domin wani ya fito kasuwa ana kiran sallar la’asar kuma za’a fara tunanin tashi daga kasuwa wanda ko shakka babu wannan gurgunata kasuwanci ne ainun.

Daga karshe, Ya maigirma gwamna ina fatan alheri a gareka da gwamnatinka. Ina kuma yi maka addu’ah ta musamman tare da tawassuli da sunayan ALLAH tsarkaka madaukaka ALLAH ya sahale maka gamawa lafiya da mulkinka, ALLAH ya yi maka jagora a dukkan lamuran rayuwaka, sannan ina fata Ya maigirma gwamna yawan kalamai na hamayya da suke fitowa daga bakinka zasu samu raguwa, duk da cewa ba laifi bane idankayi hakan a siyasance, amma muna ganin girmanka da kimarka ya wuce a ji wasu kalaman daga bakinka. Ya maigirma gwamna ina mai yi muku fatan alheri da fatan gamawa da duniya lafiya kai da Babban abokinka kuma Amininka Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano. ALLAH ya taimaki Jihar Kano ya bamu lafiya da zama lafiya.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment