Wednesday, December 12, 2012

ZOGALE SAMARIN DANGA


ZOGALE SAMARIN DANGA
Ada can akan yiwa zogale kirari da “zogale samarin danga” saboda itacansa bashi da wata wuyar samu a garuruwan Arewa. Zogale yakan fito ne birjik galibi lokacin da ruwan sama ya zuba wato lokacin damina. ‘yan uwanmu na karkara sukan yi kariyar gidajensu da itacansa, su ringa gyara katangar zana da shi inda a mafiya yawancin lokuta ake yin dirka da shi, domin rike dangar kara ko zana da akayi, amma cikin ikon ALLAH da albarkar kasa da muke da ita, ruwan sama na dukansa sai kaga ya yi tsiro kuma bishiya ta tashi a jikin dangar kara, sai aka wayi gari kusan galibin gidaje sai ka samu zogale ne ya kewayesu, wannan ta sanya ake masa kirari da zogale samarin danga. Saboda shi zai fara yi maka maraba idan ka shigo gida. Wannan ta sanya har manoma suke amfani da shi wajen sanya alama ta iyakar gona, saboda bashi da wuyar tashi.

Bayan haka, bincike a baya bayannan yana kara fitowa dangane da irin muhimmanci da ganyan zogale yake da shi. Masana a wannan zamanin suna ta kara fadada bincike dan gano irin muhimmanci da kuma irin sinadaran da zogale yake da su dan taimakawa rayuwar dan adam. A halinyanzu dai masana sun tabbatar da cewar babu wani ganye da yakai zogale amfani ga rayuwar mutane a wannan zamanin, domin yana dauke da sinadarar masu bayar da garkuwa ga lafiya, da kuma kawar da ciwace-ciwace. Kamar cowon suga, damuwa da sauran cututtuka da dama.

Mu kam a kasar Hausa munyi dace, domin tun tale-tale mun taso mun tarar da iyayanmu da kakanninmu suna dafa zogale inda ake yin kwadansa domin aci dan marmari. Wasu kuma suna yin miya da shi, kusan mu haka muke amfani da zogale tun zamani na dauri. Sai yanzu da ilimi da bincike na masana yake ta gano irin alfanun da zogale yake da shi. Domin ba wai ganyansa da muke ci ba, saiwarsa da itacensa da kwayoyinsa duk abubuwa ne masu matukar amfani da kara lafiya. Ana yin shayinsa a sha ko a tafasa shi a sha, yana maganin ciwuka irinsu shawara basur da sauransu.

Masana sun gano cewa Zogale yana dauke da sinadarin Betamin A wanda ake samu a jikin karas har sau 10, sannan yana dauke da kashi 17 na sinadarin da ake samu a jikin madara, sannan kuma yana dauke da kashi 5 na sinadarin betamin C wanda ake samu a jikin lemon zaki da dangoginsa da kuma kashi 15 na sinadarin da ake samu a jikin ayaba, dukkan wadancan sinadarai zogale ya hadasu shi kadai.

Saboda irin yadda bincike ya tabbatar da sahihancin magungunan da zogale yake yi ya sa kasashen Thailand da Malaysiya da Meziko da Kambodiya da Indonisiya da Afurka ta kudu da sauran kasashe da dama suka maida hankali sosai wajen nomansa da sarrafashi domin amfanin jama’a. Lallai muma bai kamata a barmu a baya ba, lallai mu tuntubi masana domin sanin irin alfanun da zogale yake da shi domin cin moriyarsu.
Yasir Ramadan Gwale

No comments:

Post a Comment