Friday, December 14, 2012

ABDULQADIR MUHAMMAD BELLO: Gwarzona Na Shekara A Shafin Facebook


ABDULQADIR MUHAMMAD BELLO: Gwarzona Na Shekara A Shafin Facebook
Dukkan dangin yabo da godiya da kirari sun tabbata ga ALLAH madaukakin sarki, ubangijin talikai, wanda ya dauki wannan al’umma ya fifita ta akan sauran al’ummatai, ya sanya ta jagora ga sauran mutane don ta shiryar da su ga hanyar cin nasara a rayuwarsu ta duniya da lahira. Tsira da aminciSa su tabbata ga fiyayyen Manzanni, cikamakin Annabawa, wanda ALLAH ya fifita shi ya ba shi littafi mafi cika da kamala wanda ya ke shafe-zane ne ga sauran littatafai, Annabi Muhammadu da Alayansa da Sahabbansa dakuma wadan da sukabi tafarkinsu har ya zuwa ranar sakamko. Dukkan wanda ALLAH ya shiryar shi ne cikakken shiryayye, haka kuma duk wanda ALLAH ya batar babu mai iya shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bauta bisa cancanta sai ALLAH kuma Annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonSa ne.

Hakika nayi nazari sosai kafin zabar wannan gwarzo nawa. Malam AbdulQadir Muhammad Bello matashi ne mai hazaka da juriya kuma jajiratacce. Hakika ina bibiyar dukkan wani rubutu da wannan bawan ALLAH yake yi da kuma wanda yake sharing dare da rana a shafin facebook, na yaba da kwazonsa da juriyarsa wajen kokarin shiryar da mutane ya zuwa ga hanyar ALLAH mikakkiya, bai taba gajiyawa ba wajen sadar da mutane da abubuwan da zasu taimakawa rayuwarsu ta duniya da lahira.

Wannan bawan ALLAH yana kokari matuka da gaske wajen yin da’awa ta gaskiya, tare da kira zuwa ga kadaita ALLAH da bauta akan tafarkin Sunnah da kuma fahimtar magabata na kwarai. Wallahi a wannan zamani Da’awar Sunnah tana bukatar mutane irinsu Malam AbdulQadir, domin samun mutum mai juriya da jajircewa abu ne mai matukar amfani musamman akan hanyar ALLAH.

Malam AbdulQadir ina bibiyar dukkan wasu sakonninka ko da kuwa baka ga comment dina ba. Hakika muna yiwa ALLAH godiya akan wannan baiwa da ya yi mana ta samun matasa jajirtattu masu hazaka irinka. ALLAH ya kara maka san alkhairi da yada shi ga sauran jama’a.

Ina mai yi maka addu’ah tare da tawassuli da sunayan ALLAH tsarkaka madaukaka, ALLAH ya sanyawa rayuwarka Albarka, ya kareka daga dukkan abubuwan ki da kuma kasawa. ALLAH ya yi maka jagora a dukkan lamuranka, Ya sadaka da alkhairan duniya da lahira, ALLAH ya ya daukaka darajarka. ALLAH ya amfanar da al’ummar musulmi da rayuwarka.

Ya ALLAH wannan bawa naka AbdulQadir Muhammad Bello ka yafa masa kurakuransu wadan da ya sani da wadan da bai sani ba. Ya ALLAH kasa muyi tarayyah da shi acikin Al-jannarka. ALLAH ka karfafaeshi ka kara masa juriya da kwarin guiwa, Ya ALLAH kar ka baiwa Shaidan dama akansa.

Daga karshe ina mai kira ga Gwarzona Malam AbdulQadir Muhammad Bello da ya zage dantse ya kara kokari akan kokarin da yake da shi, haka kuma Ina mai yiwa kaina da kai da sauran ‘yan uwa da muji tsoron ALLAH acikin dukkan lamuranmu, kuma mu dogara ga ALLAH a cikin dukkan lamuranmu Lallai ALLAH mai rahama ne mai jinkai, kuma maji rokon bayinSa ne Subhanahu Wata’ala.

Yasir Ramadan Gwale

No comments:

Post a Comment