Wednesday, November 28, 2012

BABBAR FITINA A RAYUWAR MATASA ITA CE SHA'AWA



                             BABBAR FITINA A RAYUWAR MATASA ITA CE SHA'AWA

A wannan zamanin wani muhimmin abu da ya addabi mutane sosai, musamman matasa maza da mata shine SHA'AWA, kusan kullum matasa na fadawa cikin bala’in fasikanci kala-kala a dalilin rashin sanin hanyar kauce wa haka. Idan mutum ya yi duba na tsanaki tare da la’akari da yanayinmu da kuma yanayin zamani zaiga cewar da yawa wasu na fadawa cikin aikata fas
iqanci ba cikin son ran su ba, sai don abin ya fi karfin su. Sau da yawa za ka ga matashi mai hankali mai tarbiyya mai tsoron ALLAH, ya san illar zina, ya san girman zunubin ta, amma saboda fitinar sha’awa ya kasa daurewa ya je ya aikata din. Wani haka zai ta aikatawa ya na tuba, da haka har zina ta zame ma sa jiki ya runka ganin ai yin ta ba komai bane Subhanallah! Haka zaka ga yarinya kamila mai tarbiyya mai hankali, ta san illar zina, ta san girman zunubin ta amma sai fitinar sha’awa ta sa ta afka cikin wannan bala'i. Domin kaucewa fadawa makaranatar shaidan dole ne duk wani matashi da yake fuskantar barazanar Sha'awa ya yi la'akari da wasu dokoki da addini ya shar'anta masa, sannan kuma ya yi amfani da dabaru wanda zasu taimaka masa.

Mu sani cewa fitinar sha’awa halittace kuma a zuciya take, daga cikin ta take bijirowa, don haka mai son ya iya danne fitinar sha’awar sa duk lokacin da ta taso masa, sai ya fara da gyara zuciyarsa tukunna. To ya ake gyara zuciya? Ana gyara ta ne ta hanyar cika ta da kyawawan tunani da shau’uka, da yanke duk wata igiyar mummunan tunani daga cikin ta, da goge mazaunin duk wani mummunan shauqi. Daga nan sai kyautata dabi’u halaye da ayyuka, duk wata dabi’a, wani hali ko wani aiki da mutum ke yi indai ba mai kyau ba ne, to yin watsi da shi zai kara haskaka masa zuciyarsa. kyawawan dabi’u sun hada da yawan murmushi, taimakawa ‘yan uwa, makwabta da abokai, gaskiya da rikon amana, da sauransu. kyawawan ayyuka su hada da taka tsan-tsan wajen tsaida addini, duk abin da akan sa ba dai-dai ba ne a addinance sai ayi kokari a bar shi komin dadin sa ko ribar sa. Yawan sanya ALLAH a zuciya da yin zikiri. ALLAH madaukakin sarki, Ya fada cikin Alqur’ani mai girma cewa: “Lallai da ambaton ALLAH ne zukata kan sami natsuwa.” Shedan ba ya iya zama cikin zuciyar da ke ambaton ALLAH balle har ya gudana cikin hanyoyin jinin ta, to ta yaya kuwa har zai tafarfasar da fitinar sha’awar wannan zuciya?

Kiyaye ibada yana daga cikin maganin da yakewa mutum kandagarki daga fitinar sha’awa. Lallai ne 'yan uwa su kula da kiyaye sallolin farilla da na nafila da yawaita karatun al-qur'ani da sauran azkar da suka tabbata daga manzon ALLAH sallalahu Alaiihi Wasallam. Sannan dole mu kiyaye maganar Manzon ALLAH SAW, inda yake cewa yaku matasa duk wanda ya ke da hali ko iko to ya gaggauta yin aure, wanda kuma ba shida halin yin aure to ya yi azumi domin wannan ya na dakushe kaifin fitinar sha’awa.

Sannan dole su kansu Iyaye su kula da rayuwar 'ya 'yansu matasa maza da mata, domin kare su daga wannan bala'i. Wani matashi ya taba tambayar wani malami cewa shi wallahi yana Azumi yana karatun Al-qur'ani Amma wallahi Sha'awarsa kullum karuwa take yi, malam ya bashi amsa da cewa to lallai ya dage ya yi aure. Kusan babban dalilin da yakan hana matasa aure shine rashin tsayayya ko kwakwkwarar sana'ar da mutum zai iya rike kansa da kuma Iyalinsa, wannan kam babban al'amari ne, domin babu yadda za'aji dadin aure idan babu wata hanya da mutum zai iya daukan dawainiyar iyalinsa, dan haka dile a dage a koyi sana'a domin a dogara da kai. Ya ALLAH ka baiwa dumbin matasanmu dama da ikon yin aure.

No comments:

Post a Comment