Tuesday, November 27, 2012

Mobutu Sese Seko Ngbengdu Wa Za Banga


                  Mobutu Sese Seko Ngbengdu Wa Za Banga



Sunan da ya fi shahara da dai shi, shine Mobutu Sese Seko, shine Shugaban kasar Jamhuriyyar Demokaradiyyar Kwango mafi dadewa. Ya dare kan madafun iko kusan tun shekarar 1965 har zuwa 1997. Mobutu dai shine mutumin da ya sauyawa kasar suna zuwa sabon sunanta Zaire. Shugaba Mabutu yana daya daga cikin shugabannin Afurka da tarihi ba zai taba mantawa da su ba, tarihi zai ci-gaba da tunawa da Mobutu ba dan yayi wani abin kwarai ba, sai dan yana daya daga cikin shugabannin da akayi a Afurka Almubazzarai mabarnata masu dan-karan ta'adi.

Shugaba Mobuto mutum ne mai shegen girman kai da nuna isa da kama karya. Ya jefa kasarsa cikin mawuyacin halin fatara da matsanancin talauci da karyewar tattalin arziki a zamanin mulkinsa, domin shi kadaine a Afurka wanda matarsa take zuwa Amerika gyaran gashi a duk lokacin da ta bushi iska, ko kuma ta tafi kasar faransa domin sayan manshafawa da turare a zamanin mulkinsa.

Mobutu shine da na farko na wata mata mai aikin hotel da ake kira Marie Medeliene Yemo. A rayuwarsa ta kuriciya ance mutumne da baya jin magana kuma sannan mai kiriniya, abokanansa da suka yi makaranta tare da shi sunce yana da kaifin kwakwalwa da hazaka sosai, amma kuma mutum ne mai wasa da yawa, wannan yasa kuma bai cika maida hankali a karatu ba, daga mahaifiyarsa ta maida shi garin Coquilhatville dan ya ci gaba da karatu, anan aka ringa zaneshi saboda yiwa turawa rashin kunya, domin ansha kama shi yana yiwa turawa gwalo da dakuwa a cikin aji.

Saboda irin yadda Mobutu ya zama dan kama karya da rashin alkibla ya sa Laurent Kabila ya yi masa juyin mulki a shekarar 1997, inda ya gudu ya koma kasar Morocco dan neman mafakar siyasa. Ya karasa sauran rayuwarsa a can kasar ta Magrib, rahotanni sun tabbatar da cewa ya mutu ne sakamakon bugun zuciya sakamakon damuwar da ya shiga tun bayan hambarar da shi daga kan mulki.

Mobutu dai ana kirga shi a zaman wani irin mutum mai al-mubazzarancin gaske, domin ansha ganin hotunansa ana zuba masa kudi ko fulawa a kasa yana takawa.

No comments:

Post a Comment