Monday, November 26, 2012

ZA'A TONO GAWAR MALAM YASSIR ARAFAT DAN BINCIKE



 ZA'A TONO GAWAR MALAM YASSIR ARAFAT DAN BINCIKE

Marigayi shugaban Palasdinawa Malam Yassir Araft an haifeshi ne ranar 24 ga watan agusta a shekarar 1929 a birnin al-kahira na kasar masar. Ya taso cikin matsakaiciyar rayuwa ta babu yabo 
 babu fallasa, ya yi karatu cikin kalubalen rayuwa, a shekarar 1958 shi da abokinsa suka ci nasarar kafa kungiyar gwagwarmayar 'yanto kasar Palasdinu daga mamayar Israela wadda aka fi sani da Al-FATAH sunyi ta kokarin yin managartan tsare-tsare domin yin gwagwarmaya cikin sirri, a shekarar 1959 suka fara buga wata mujallah da take kiran matasa da su fito domin gwagwarmayar kare palasdinu daga mamayar Israela, a karshen shekarar 1964 Malam Arafat ya zama Babban jagoran 'yan gwagwarmayar cetar da Palasdinu. 

Malam Arafat ya fafata da Israela ta sunkuru, sannan ya jagoranci wata kafsawa da kasar Urdun da aka fi sani da Jordan bayan da ya zama Sabon shugaban kungiyar Palasdinawa ta PLO a shekarun 1960 zuwa 1970. Malam Yassir Arafat ya halarci manyan tarukan tattaunawa na shan-shayi da kasar Israela domin neman mafita wanda ya hada da Yarjejeniyar da aka kulla a Birnin Madrid a shekarar 1991, haka kuma, ya halarci Ittifaqiyar da kayai a birinin Oslo a 1998 da kuma Ganawa da sukayi ta karshe da Shugaban Israela Areil Sharon karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Amerika Bill Clinton wadda akafi sani da yarjejeniyar Camp David.

Malam Yassir dai ana yi masa kallon wani mutum dan-gwagwarmaya amma ta neman sulhu wadda za'a zauna akan kujera. Karkashin shugabancinsa ya Amince da kafa kungiyoyin Hamas da Jahadil Islami a matsayin kungiyoyin gwagwarmayar a yankin Gaza da palasdinu baki daya, ana yiwa kungiyoyin biyu dai kallon wasu masu kishin addini sosai, sama da ita Fatah da ta hada da kiristoci a ciki da kuma suke san tattaunawa akan tebur.

Arafat dai ana ruwaito shi a masayin wani mutum mai kishin Palasdinu domin yana yawan maimaita kalaman "kada ku mance da palasdinu" ance kusan duk wani taro da ya halarta sai ya maimaita wannan magana. A ranar 29 ga watan maris na 2002 ya yi wata magana da kusan ta mamaye galibin jaridun kasashen larabawa inda aka ruwaito shi yana cewa "suna san kama ni a matsayin wani fursuna, ni kuma ina ce musu mutuwa cikin shahada nake fata" da kuma wata magana da ya taba fada a Camp david cewa "shugabannin larabawa basu taba mafarkin barin Jerusalem a hannun Yahudawa ba".

Malam Yassir Arafat dai ya rasu yana da shekaru 75 a wani asibiti a kasar faransa bayan ya shafe wani lokaci yana jinya. Sai dai bayan shekaru 8 da mutuwarsa aka fara wani bincike kan musabbabin mutuwarsa, shin mutuwa ce ta ALLAH da ANNABI ko kuwa guba aka sanya masa, inda ya zuwa yanzu bayan wani bincike na sirri da gidan talabijin na Al-Jazeera ya gudanar ya tabbatar da cewar Kashe Malam Yassir Arafat akayi, inda wannan batu ya tayar da kura. yanzu haka dai yau za'a tono gawarsa domin yin bincike na karshe. ALLAH ya jikan Malam Yassir Arafat, ALLAH ya taimaki Palasdinawa ya kawo karshen wannan zama na tashin hankali da aka kwashe sama da shekaru 60 ana yi.

Yasir Ramadan Gwale.

No comments:

Post a Comment