Wednesday, November 21, 2012

GA ABINDA ABBAS FAGGO YA FADA WANDA YA JA MASA FUSHIN GOV ISA YUGUDA



GA ABINDA ABBAS FAGGO YA FADA WANDA YA JA MASA FUSHIN GOV ISA YUGUDA

'Yan uwanmu da suke Abuja zasu shaida wani gagarumin biki da za'ayi, ba bikin kowa bane ba kuwa Illa bikin dan gidan maigirma gwamnan Bauchi inda zai angwance da Amaryars
a 'yar gidan wani hamshakin mutum wanda ya taba yin takarar Shugabancin jam'iyyar PDP ta kasa. Rahotanni dai sun tabbatar da cewa tuni Ma'aikatar kananan Hukumomi ta jihar Bauchi ta umarci kowace karamar Hukuma da ta bayar da gudunmawa ta Naira Miliyan Biyu (2m) Domin wannan shagali na bikin dan maigirma Gwamna. Tuni Iyalin maigirma gwamna suka bayar da kwangilar Buga kalanda da wasu takardu da za'a raba yayin wannan biki ga wata madaba'a a birnin tarayya Abuja, Sannan kuma anbayar da kwangilar Buga wasu karin kayan tsara da suka hada da Jakunkuna da kofunan shayi na kawa da sauran kayayyaki ga wata mata dake Legas, duk wadannan abubuwa dai za'a rabar da su a yayin wannan biki, kuma za su kasance dauke da hoton Ango ne da Amarya.

Tuni kuma aka baiwa Ango kyautar wata dirkekiyar Mota SUV JEEF a matsayin kyauta ta musamman. Sannan kuma kowanne Shugaban karamar Hukuma daga cikin kananan Hukumomi 20 zasu tura matansu Abuja domin shaida wannan biki na kasaita da za'ayi, tun daman Maigirma Gwamna tuni ya zama dan Abuja.

Labarin wannan biki dai ya karade dukkan jihar Bauchi. Sannan kuma Gwamnatin Jihar Bauchi ta hannun Sakataren Gwamnati ta turawa Ango da kudi wuri na gugar wuri har Dalar Amurka 80,000 domin bikin da zaiyi a Ingila na murnar kammala karatunsa na Jami'ah, wannan kudi dai maigirma gwamna ya bada umarni a aikawa da dansa saboda yana bukatarsu cikin gaggawa, dan yana san sayan wata dirkekiyar marsandi wadda zai hau yayin wannan biki.

Haka kuma, a watan Nuwambar 2009 mai dakin mai girma gwamna ta bukaci a aikawa da danta wanda yake a birnin Washington na kasar Amurka da kudi Fan na Ingila 150,000, wanda wannan kudi tuni aka tura su ta hannun tsohon akawun jihar Bauchi.

Wani abin mamaki dangane da haka shine, maigirma gwamna yana da mata uku (3) da 'ya 'ya ashirin da daya (21) dukkansu anhaifesu a Najeriya amma kuma wasu daga cikinsu suna waje ana yi musu hidima da kudin al'ummar Jihar Bauchi, sannan kuma maigirma gwamna yana yin amfanin da kudin jihar Bauchi wajen nemawa 'ya 'yansa biyu da aka haifa a Amerika izinin zama 'yan Amerika! Tuni maigirma Gwamna ya mallaki wani katafaren gida a birnin Maryland dake kasar ta Amerika. Duk wannan facaka da kudin al'ummar Bauchi tana faruwa ne a yayin da ma'aikata suke tagayyara wajen karbar hakkinsu a matsayinsu na ma'aikata. ALLAH ya ceci jihar BAUCHI.

Ya Mai karatu wannan fa shine abinda ABBAS FAGGO ya fada a shafinsa na facebook wanda ya bakantawa Gwamna Isa Yuguda Rai, har ta kai ya sanya aka kama shi aka daure shi. Yanzu zance da muke Ankori ABBAS FAGGO daga aikin da yake a matsayinsa na dan jihar Bauchi, laifinsa kawai shine yayi magana akan Amfani da maigirma Gwamna ya yi da dukiyar al'umma wajen hidimtawa Iyalansa. ALLAH ya sawwake Najeriya Ina muka dosa?

No comments:

Post a Comment