Wednesday, November 28, 2012

Julius Kambarage Nyerere: Shugaba Mafi Kima A Afurka



                             Julius Kambarage Nyerere: Shugaba Mafi Kima A Afurka


Julius Nyerere kamar yadda aka fi saninsa shine shugaban kasar Tanzaniya na farko, ya zama shugaban kasa tun kasar tana amsa tsohon sunanta na Tanganyika. An haifi Nyerere a ranar 13 ga watan Afrilu a shekarar 1922 a kauyan Butaima, mahaifinsa cif Zanaki mutumin kirki ne da ake girmamawa, Nyerere ya fi shahara da sunan “Mwalimu” wanda a yaren Suwahila yake nufin “Malami”. Bayan da ya yi karatu a jami’ar Makere da ke kampala a kasar Uganda ya wuce jami’ar Edingbugh a kasar Burtaniya, daga nan ya dawo gida ya zama malamin makaranta.

Kasancewar Nyerere mutum mai kima a idanun jama’a wannan ya bashi damar sanin jama’a sosai da kuma zama tare da tattaunawa da mutanansa domin basu shawarwarin yadda zasu warware matsalolinsu na rayuwa. A shekarar 1954 ya jagoranci kafa wata jam’iyyar siyasa mai suna Tanganyika African National Union, an zabe shi a matsayin Prime Minista a shekarar 1961 a wannan lokacin ya kasance shugaban kasar tanganyika na farko. A shekarar 1964 ya ci nasarar hade kan tsiburin Zanzibar da Tanganyika inda suka zama kasa daya wadda aka radawa suna TANZANIYA, haka kuma a shekarar 1967 ya kaddamar da shirin nan na Tanzaniya ta dogara da kanta wanda aka fi sani da Arusha Declaration.

Nyerere ana kwatantashi da mutum mai tsananin kishin al’ummarsa da kuma Nahiyar Afurka. Yayi matsakaiciyar rayuwa a lokacin da yake shugaban kasa. Shuagab Nyerere dai bai zakewa turawa ba kamar sauran shugabannin Afurka, a mafiya yawancin lokuta baya boye akidarsa dangane da yadda turawa suka yi kaka-gida a nahiyar Afurka, sannan ya kalubalanci prime ministan Burtaniya Harold Wilson da Ian Smith akan 'yancin kasar Rhodesiya wadda ake kira Zimbabwe a yanzu, a saboda haka ne yafi kusanci da kasar chana sama da sauran kasashen yamma, amma sunyi zaman lafiya da tsohuwar rusashshiyar Tarayyar Sobiya da sauran kasashen duniya, musamman masu adawa da mulkin danniya na turawan mulkin mallaka. Haka kuma, yana daya daga cikin mutanan da suka jagoranci samun 'yancin kasashen Zambiya da Botsuwana da Muzambique da Angola da kuma Rhodesiya ko Zimbabwe. Nyerere ya taba zuwa Najeriya har fadar mai martaba sarkin Kano a zamanin mulkinsa.

Shugaba Nyerere ya sauka daga shugabanci bisa radin kansa a shekarar 1985 domin ya koma ci-gaba da matsakaiciyar rayuwarsa. Ana bayyanashi a matsayin wani mutum mai kaifin Harshe da iya magana, shugaba Nyerere yana da kima sosai a idon takwarororinsa Shugabannin Afurka, ya rasu a shekarar 1999 ba tare da ya mallaki ko da filin da zai gina gida ba. Turawa suna yi masa kirari da mutum mai gaskiya da rikon amana a lamuransa. Nyerere yana daga cikin shugabannin Afurka da suke da kima ainun.

Yasir Ramadan Gwale.

No comments:

Post a Comment