Tuesday, January 1, 2013

BOKA SHAIDANIN AL'UMMA


Da can mukanji labarin cewa mata ne suke cin kasuwarsu a wajen bokaye. Sannan babban dalilin da yake kai mata wajen Boka galibi bai wuce wasu batutuwa guda biyu ba, wato KISHIYA da kuma MALLAKAR MIJI, mafiya yawancin mata da suke zuwa wajen boka wannan shine dalilin zuwansu. Bokaye da dama sun halakar da mata da yawa kuma sun kashe aure da yawa akan wannan batu, bayan wannan abunda suke yi, Bokaye sun shahara da FASIKANCI da matan da suke zuwa wajensu, wannan kuma zamu Iya cewa alhaki kuikuyo ne, bayan kasancewarsu Sun sabawa ALLAH da ManzonSa, Sannan sunci amanar Aure da mazajensu. Allah ne kadai yasan adadin mazajen da suka sha jike-jiken bokaye ko suka sha-ruwan tsarkin mata a cikin al'ummarmu, wasu a abinci wasu kuma a cikin abun-sha.

Matan da suke zuwa wajen Bokaye sunyi Imani da maganganunsu sosai, domin suna ganin duk abinda boka ya fada mai faruwa ne. Amma Alhamdulillah, Malamai suna ta yin wa'azi sosai da karantarwa akan hadarin da yake tattare da zuwa wajen Boko da kuma bayanin fushin ALLAH akan mai zuwa wajen Boka, domin Boko Mushiriki ne. Allah ya yafewa wadan da suka tuba suka dena.

Yanzu kuma abin ya sauya salo, Inda bayanai suke nuna cewa Adadin matan da suke zuwa wajen Boka yana raguwa, amma kuma Na mazan da suke zuwa wajen Boka yana karuwa. Yanzu dai masu neman Mulki ta kowacce hanya sune suke daurewa bokaye Gindi suke tsula tsiyarsu ganin dama, satar mutane ya karu alfasha ta karu domin duk wannan yana daga cikin Sharrin Bokaye, domin bayanai sun nuna cewa suna baiwa masu zuwa wajensu umarnin samo wasu sassan jikn dan Adam domin hadawa da su a yi Tsafi, Haka kuma, bokaye kan dora mutane akan mummunar hanyar Yin jima'i da mahaukata, sai kayi mamaki kaga Mahaukaciya da kurtsetsen ciki ita ba Aure ba kuma ita ba Hankali ba balle a tambayeta ina ta samu ciki! Sannan sukan dora mutane akan hanyar yin Luwadi, kamar yadda bayanai suke nunawa duk domin samun Mulki ko direwarsa ko kuma karuwar arziki.

Idan me zuwa wajen Boko yaje wajensa, Bokan ya gaya masa cewa zai zama Shugaban kasa ko gwamna ko shugaban karamar hukuma ko kuma zai kudance sai mutumin yayi Ammana da maganar Bokan. Amma kuma da Bokan zai gaya masa cewa bazaka zama Shugaban kasa ba, amma zaka zama SARKI nan take zai karyata Boka, dan yasan Babu yadda zai a yi ya zama Sarki. Idan da masu zuwan suna amfani da hankali da tunani ko basu san addini ba, nan take zasu karyata Boka ko me yace musu zasu zama, amma da yake Boka wakilin Shaidan ne a tsakanin mutane, kuma Shaidan yayi alkawarin Halakar da al'umma dan haka suke ta samun karin Tagomashi. 

Allah kuma yayi alkawarin cika Wuta da Duwatsu da mutane. Dan haka Bokaye da masu zuwa wajensu muddin basu tuba sun bi Allah ba, muna yi musu albishir da cewa Wutar Jahannama Itace makomar dukkan wani mushuruki. Tir da wannan makoma, muninta yayi yawa. Allah ka tsaremu ka tsare mana Imaninmu. Masu zuwa wajen Bokaye daga cikin mata da maza Allah ka shiryesu.

No comments:

Post a Comment