Monday, January 14, 2013

WA YE ZAI HANA GOODLUCK JONATHAN TSAYAWA TAKARA?


Wani zubin idan wadan da suke kiran kansu sune shugabannin 'yan Adawa suka yi magana akan siyasa sai kaga tsiraicin siyasarsu. A kwanakin da suka gabata rahotanni suka ce anga fastocin shugaban kasa a Abuja dauke da bayanan da suke nuna cewa zai sake neman zabe a 2015. Na sausari wata hira da akayi da Farouk Adamu Aliyu a BBC yana cewa su fatansu Allah ya sa shugaban kasa ya sake fitowa neman zabe . . . Ban san wanne shiri suke da shi na tunkudeshi ba. 

Amma Shakka babu babban aikin da ya kamata a dukufa haikan akansa shine ayi dukkan mai yuwuwa wajen hana wannan mutumin tsayawa takara a 2015, kamar yadda aka kashe 3rd Term na Obasanjo a kakar zaben 2007. Bahaushe ya ce "ba a iya yashe rijiya sai anshiga cikinta" ko dai ka shiga ka yaso dukkan dattin da yake cikinta, dan samun tsabtataccen ruwa, ko kuma ka tsaya daga waje kana kwarfe ruwa mai kyau amma dattin yana kasa.

Dan haka, dukkan zaratan yakin siyasa irinsu Atiku Abubakar da suka hana Obasanjo sakat, suka fatattakeshi da shi da 3rd term dinsa, irinsu muke fata su hana wannan mutumin tsayawa takara a 2015. Amma muddin muka ce zamu sake yin irin kasassabar cewa zamu iya kada shi a babban zabe maimaikon zaben fitar da gwani to lashakka Garin Zubar da Ruwan Wankan Yaro to zamu zubar da ruwan har da Yaron, mai makon a zubar da ruwan kawai.

PDP da gaske suke yi akan wannan zabe zasu iya kashe ninkin baninkin abinda suka kashe a 2011 domin samun zabe ko ta halal ko ta haram, kuma sunyi shiri akan hakan, duk wata satoka sa katse da 'yan PDP suke yi karya ce, kuma yaudara ce, domin zabe yana zuwa sai ka tarar bakinsu ya zo daya. Kowa yaga irin yadda aka bada labarin tsamin dangantaka tsakann Atiku Abubakar da Gwamnan Murtala Nyako amma da zaben Nyako ya zo Atiku sai da ya fita ya kira jama'a su zabi Nyako.

Lallai abinda zamu tambayi kawukanmu shine, Shin waye zai hana shugaban kasa sake tsayawa zabe Idan har ya nace akan haka?

No comments:

Post a Comment