Friday, January 18, 2013

ZUWA GA COMR. BILYAMINU ABDULLAHI ADANJI


ZUWA GA COMR. BILYAMINU ABDULLAHI ADANJI

Da sunan Allah mai gamammiyar rahama mai jinkai tsira da amincinSa sukara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad salallahu alaihi wasallam da sahabbansa da iyalan gidansa da wadan da suka bi tafarkinsa har yazuwa ranar sakamako, ina shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah tsarki ya tabbata a gareshi.

Lokacin da na fara kiranka a waya Comrade Bilyaminu Abdullahi Adanji baka dauka ba na sake sannan ka kashe na kuma a karo na uku ka sake kashewa, ko shakka babu Raina yayi matukar baci a wannan lokaci daga baya, nayi tunanin watakila kana cikin wani Uzuri ne da ba zai baka damar amsa waya ba, bayan wani lokaci sai ga kiranka Bilya, kamar bazan dauka ba sai dai kawai na dauka na amsa maka cikin murya mai nuna damuwa nace "MENE" abin da na fara fada sannan kace TUBA NIKE DAN MUTAN GWALE, don Allah kayi hakuri, na amsa maka da cewa babu matsala comrade, ko shakka babu munyi tattaunawa mai tsawo a wannan lokaci kuma mun fahimci juna sosai da gaske, kuma wani abu da bazan manta da shiba shi ne tun a wannan lokaci duk sanda mukayi waya Bilya ka kan kirani da "Danmutan Gwale", kusan a wajenka na fara jin wannan suna, haka kuma duk wanda ya kirani da wannan suna acikin 'yan kungiyar Muryar Talaka to yajine daga bakinka, kuma wannan sunan yabini har gidanmu.

Mun fara hada ido da juna nida kai Bilya lokacin taronmu na farko a shekarar 2010, kuma abin da Bilya ka cemin shi ne "Nice to meet you Danmutan Gwale" nima na amsa maka da "I'm Pleased to meet you my dear comrade", daga nan ka bani wayarka na saka maka ita a chaji, muka ci abinci tare sannan kuma muka shiga cikin hada-hadar al'amuran kungiya, na iya tuna bayan gari ya waye Zaidu Bala da tawagarsa sunyi wanka zasu tafi gurin taro, sun tafi da wuri domin yin shirye-shirye, ina zaune a daki sai ga Bilya ka dawo ka ce dani Danmutan Gwale don Allah ina zan samu Weeklytrust? Na amsa maka da cewa zan taho maka da ita, Bilya ya kalleni yayi murmushi yace sai ka taho danmutan Gwale.

Hakika munsami fahimtar juna sosai da Bilya domin yana turamin sakon tunasarwa kusan duk ranar Juma'a 'karta kwana' kuma nima ina tura maka, ko shakka babu zan dade ina tunawa da kai Comrade Bilyaminu Abdullahi Adanji. Bana manta ranar wata Litinin na shiga makarantar CAS Kano, sai ga Kiran Zaidu Bala a lokacin ba daga dan banji alamar wayata ta yi ruri ba, sai bayan da na fito zan hau dan acaba sai na dauko waya ta na duba lokaci, nan naga kwantaccen kiran Zaidu Bala, nan na mayar masa da kira ina mai bashi hakuri, kawai sai ji nayi Zaidu yayi salati, take gaba na ya fadi domin nasan sakon da alama na rashi ne, amma kuma ban san ko waye ba, cikin murya mai ban tausayi Zaidu Bala ya sanar da ni cewa Abokinmu Comrade Bilya! Nace me ya faru da shi? Nan muryarsa ta sake raurawa ya ce Yasir Allah ya yiwa Bilya rasuwa yana hannun mahaifiyrsa! Hakika na kadu matuka da samun wannan labari, ban mantawa acabar da na kasa hawa kenan tsawon lokaci ina ta salati tare da maida lamari ga Ubangijin talikai.

Bilya kasani wallahi baka yi gaggawa ba kuma inda ka tafi muma muna nan zamu biyoka komai tsawon zamani, ya zuwa lokacin da zamu zo nasan kazama dan gari mu kuma zamu zo a baki tunda karigayemu. Bilya ka tafi a daidai lokacin da kake begen ganin rayuwar 'yan najeriya ta kyautatu dan talaka ya ci moriyar arzikin kasarsa, Hakika ina yima bushara da cewa Allah zai cika maka burinka na ganin an sami kyautatuwar rayuwa a Najeriya. Bilya na dauki alkawarin duk lokacin da na tunaka zanyi maka Addu'ar samun Rahama a wajen mahalicci.

Bilya rahamar Allah ta yalwaci kowa, inayimaka fatan samun wannan rahama kamar yadda nake yiwa kai na fata Allah ya sadamu a Aljanna baki daya. Allah ya jikanka ya gafarta maka.

Wassalamu Alaikum.

Daga Naka Yasir Ramadan Danmutan Gwale

No comments:

Post a Comment