Friday, June 21, 2013

ZUWA GA GWAMNAN SOKOTO ALU MAGATAKARDA WAMMAKO

ZUWA GA GWAMNAN SOKOTO ALU MAGATAKARDA WAMMAKO

Assalamu Alaikum Warahmatullah, ina bude wannan wasika tawa da kalamai na yabo da godiya da kira ga Allah madaukakin sarki, mamallakin ranar sakamako, Ina shaidawa babu abin bautawa bias cancanta sai shi, kuma Annabi Muhammad BawanSa ne, kuma ManzonSa ne. Ya mai girma gwamnan, kamar yadda muka sani ba boyayyan al’amari bane a gareka irin yadda jama’ar sakkwato suke cikin matsananiciyar wahalar riwan sha. Ruwa shine rayuwa, kamar kuma yadda ake masa kirari, abokin aiki ne. Bisa la’akari da irin rahotannin da suke fitowa daga jihar sakkwato yana nuna cewa jama’a na kara tagayyara saboda matsananciyar bukatar ruwan amfanin yau da kullum, sannan kuma ruwan yayi karanci musamman a cikin daukacin babban birnin jihar sakkwato.

Mai girma gwamna, hakkinku ne, a matsayinku na shugabanni ku zama hadiman al’ummominku, wajen bayar da kulawa ta musamman da dukkan irin bukatun al’umma na rayuwa. Yanzu a wannan lokacin da muke ciki al’ummar da suka zabeka suka baka kuri’unsu dan tafiyar musu da jiharsu tare da alkinta musu dukiyarsu, ba su da wata bukata ta gaggawa da ta wuce ruwan-SHA. Kamar yadda na fada, maigirma gwamna ba zai kasa jin koken al’umma ba dare da rana akan wannan matsala ta ruwan sha, lallai, muna kira ga maigirma gwamna ayi dukkan mai yuwuwa wajen wadata al’ummar jihar sokoto da ruwan sha tsabtatacce, domin fitar da jama’a daga cikin mawuyacin hali.

Yara da mata da tsaffi da magidanta sun tagayyara matuka saboda halin da suka shiga na farautar ruwa. Duk wani wajen da ake samun ruwa, cike yake da jama’a makil, mutane tun asubahi suke fita domin neman ruwan da zasu sha su yi ibada. Muna fatan Allah ya sa maigirma gwamna yaji wannan kira kuma, a dauki mataki na gaggawa wajen inganta al’ummar jihar sakkwato da ruwan sha. Allah ya bada iko.

Allah ya taimaki Jihar Sokoto.

Allah ya taimaki Yankinmu Na Arewa Maso Yamma, Da Arewa da Najeriya gaba daya.

Yasir Ramadan Gwale
21-06-2013

1 comment:

  1. Allah ya sa wanda akayi dominsa ya ji ya kuma aiwatar da buqatar alummarsa

    ReplyDelete