Wednesday, June 19, 2013

ZAMFARA: Anya Kuwa Barayi Ne Ke Kashe Mutane?


ZAMFARA: Anya Kuwa Barayi Ne Ke Kashe Mutane?

Duk lokacin da aka ce barayi sun shiga jihar zamfara sun kashe mutane da dama, sai abin yayi ta dawurwura a zuciyata shin anya kuwa barayin ne da gaske? Abin mamaki, me barawo zai samu a Zamfara? Kuma a zamfarar ma a cikin kauye! Shin indai barayin gaskiya ne me ya hanasu zuwa Habuja su yi satar indai da gaske barayi ne? Duk barawon da zaije kauye a zamfara da muggan makamai ya kashe mutane, ai kuwa zai iya zuwa Habuja. Abin akwai daure kai matuqa da gaske, ace irin wannan kisa yana faruwa haka a jihar zamfara. Lallai hukumomi su tashi tsaye wajen baiwa rayukan al’umma kariya tare da dukiyoyinsu. Tun da jimawa ake kawo rahotannin wadannan barayi, maimakon abin ya lafa sai karuwa yake, adadin mutanan da ake kashewa yana karuwa cikin sauri. Tsoronmu kada barazanar da muke fuskanta a yankin Arewa maso gabas ce tayi tsallen badake ta diro a jihar zamfara Arewa Maso Yamma.

Wani Karin abin daure kai, shine duk lokacin da aka ce wadannan barayin sun shiga kauyukan to kisan da suke yiwa al’ummar yafi satar da suke yi, wannan yana kara bayyana mana gaskiya masu aikta wannan aiki ba barayi bane, wasu ‘yan ta’addane suke shiga rigar barayi suna kasha jama’a babu gaira babu dalili. Mutane suna gidajensu basu san hawaba basu san sauka ba, a farmusu da kisa babu kakkautawa. Abin na wannan karon yafi duk wanda akayi a baya muni domin kuwa wannan har ya hada da uban kasa, sannan ga mutane sama da arba’in a cewar hukumomi sun rasa rayukansu.

A kwanakin baya akayi irin wannan kisan na gilla a karamar hukumar birnin Gwari dake jihar Kaduna, inda nanma aka shiga kauye aka kasha jama’a da dama da sunan cewa barayi ne, daman kuma karamar hukumar mulki ta birnin Gwari tayi iyaka da jihar Zamfara. Lallai wannan al’amari akwai lauje a cikin nadi. Ya kamata ayi bincike na gaskiya akan su waye masu aikata wannan aika-aika da sunan fashi da makami.

Kuma anan zamu yi kira ga al’umma lallau su tashi tsaye wajen baiwa kansu da iyalansu da dukiyoyinsu kariya. Domin kuwa lokaci ya wuce da zamu dogara da hukuma kawai wajen tsare mana dukiyoyinmu da rayukanmu, su kansu hukumomin a tsorace suke, bukata suke a karesu suma. Lallai jama’a a dage wajen aikin sintiri na cikin unguwanni, sannan akai rahoton duk wanda aka gain ba’a gamsu da motsinsa ba cikin unguwa wajen jami’an tsaro, ta hanyar haka ne zamu taimakawa kanmu da iyalanmu, mu zauna lafiya.

 Allah ya jikan wadan da suka rigamu gidan gaskiya. Su kuma masu wannan mummunan aiki. Allah karka rufa musu asiri, Allah ka wulakantasu ka hana musu jin dadi. Allah ka karemu da kariyarka, ka tsaremana rayukanmu da dukiyoyinmu.

Yasir Ramadan Gwale
19-06-2013

1 comment: