Tuesday, June 18, 2013

MESSIN PDP YAYI FADUWAR BAKAR TASA


MESSIN PDP YAYI FADUWAR BAKAR TASA

A daidai lokacin da fitaccen dan wasa, kwararre, wanda ya iya yanka da zilliya a cikin fili kamar tarwada a kududdufin me Allo, yake tsaka da nuna gwanintarsa, aka shammace shi bai sani ba. Messi dai yana hango zaren APC “empty” ya kwaso kwallo a guje aka tadeshi ya fadi, cikin nasarar da Messi yake nema Lafari ya busa usur, inda aka baiwa Messi bugun tazara. A wannan lokacin ne kuma, Messi ya fara gwalangwaso da gwadari wai shi ga fitaccen dan kwallo, mai makon ya tsaya ya shirya ‘yan wasansa  dan ganin yadda zai yiwa kwallon”shaudul awwal” ta fada ragar APC masu hamayya,. Kawai sai aka hangoshi yana sallamar wasu ‘yan wasa wai su koma suci benci bayan suna cikin etin da su aka raba wasa.

Ganin haka ya sanya Lafari ya baiwa Messi jankati tare da busa tashi daga wasan. Saboda maimakon Messi ya yi amfani da damarsa ta kwararren dan wasa ya takarkare ya zura kwallaye ba kwallo ba, a ragar ‘yan hamayya, sai ya bige da nuna rashin sanin inda wasan ya dosa. Watakila ko dai Messi bai fahimci cewa wasan shine na kusa da na karshe bane, alamu sun nuna cewa Messi yayi zaton cewa a kwata fainal ake har yanzu shi ya sanya bai maida hankali sosai ba, a matsayinsa na dan wasan da duniya ta sallamawa. Kuma shi da kansa aka jiyoshi yana cewa duk fadin wannan nahiya babu wani kulab da yakai nasa, manyan ‘yan wasa, da iya sanin sirrin tamaula. Yanzu dai zamu iya cewa Messi yayi faduwar baker tasa, domin kuwa duk irin cika bakin da yayi na yayyanke ‘yan kulab din APC tare da zuzzura musu kwallaye, ashe Mazugal ya dinga shatatawa.

Watakila zamu ce ko Messi ya manta da tarihin tamaula ne, a tarayyar Haurobiya. Domin kuwa magabatansa ai basu kwashe da dadi a cikin kulab din ba, domin daga wanda aka kora ana tsaka da take wasa, sai wanda aka dinga basu katin gargadi har suka fita daga filin da kansu saboda tarin katukan da suka karba. Dama dai tuni ‘yan kallo suka zurawa Messi ido dan ganin yadda zai kwashe da manyan manajojin kulab dinsa na PDP. Da yawa sun san da cewa an tursasawa ‘yan wasan Messi ne dan ayi amfani das hi wajen cimma wata boyayyar manufa, watakila a tunaninsu Messi yaci kwallo da hannu, kamar yadda Maradona ya taba cin kwallo.

Lallai zamu iya cewa Messi lissafinsa ya kwace a wannan wasa. Domin kuwa ya manta cewa duk dan wasan da aka baiwa Jan-kati sai ya rasa dammar buga wasanni biyu. Yanzu kenan Messi zai jira a bayan filin wasa har sai bayan angama wasan 2015 da 2019 sannan a duba yuwuwar dawo das hi idan anga d’a’arsa ta canza. Amma kuma, da alama shekaru zasu yiwa Messi kancar, domin kuwa lokaci ba zai jirashi ba. Sai dai ya tara wani jikon, ko kuma dansa da yake tunanin amfani da shi a can garinsu a matsayin sabon jini, kuma me rike da akalar ‘yan wasan can din, yam aye gurbinsa nan gaba idan yana da rabo.

Muna fatan yanzu Messi zai koma ya yi karatun baya, ya kalli tsaffin ‘yan wasa irinsu Soloman Lar da Barnabas Gemade da Ahmadu Ali da Vincent Ogbulafor domin ya dauki darasi ko kuma shima ya bi sahunsu. Bamu sani ba ko ‘yan wasan da Messi ya sallama su yi masa bita da kulli, su cajeshi da cin hanci a tsakainsa da ‘yan wasa ko kuma zargin da ake yiwa dansa a tabbatar das hi. Anan sai muce kwallo bata yiwa Messi Kyau ba.

Yasir Ramadan Gwale
19-06-2013

No comments:

Post a Comment