Saturday, June 22, 2013

MAGANA TA GASKIYA


MAGANA TA GASKIYA

Assalamu Alaikum Warahmatullah, Ya dan uwa, zance na gaskiya duk wani Malami komai tsawon gemunsa, komai girman rawaninsa, idan yace maka ga wata Sallah ko wani salati ko wata Ibada da zaka yi Allah zai baka ladan adadi na wasu Annabawa, wallahi summa tallahi tataccen makaryaci ne, kuma dan damfara ne, yayi amfani da irin tsabar san banzaka da san ka da shiga Al-jannah ba tare da kayi wani aiki mai yawa ba ya sa ya yaudareka. Ya dan uwa ka sani akwai Annabi Nuhu yayi shekaru Dubu babu Hamsin yana kira zuwa kadaita Allah da Bauta, da sauran dukkan Annabawa da suka biyo bayansa haka suka dinga jaddada wannan kiran. Wasu annabawan andokesu kai wasu har zarto aka sanya akansu aka raba su gida biyu, saboda kawai sunce Abi Allah.

Duk irin wannan wahalar da Annabawan Allah suka sha, sai kawai wani mutum yace maka ga wata IBADA da zakayi da bata wuce Awa guda ba, Allah zai baka ladan wadannan Annabawa. Tab! Wallahi wannan wasa da Allah ne, sai ka tambayeshi shin Ina matsayin wadancan Annabawa, tsakanin kai da akace Allah zai baka ladansu da kuma su, waye a gaban wani? Wallahi duk sallarka duk Azuminka da Zakkarka da Aikin Hajjinka baka isa ka kama kafar Sahabban Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wasallam ba, ballantana ANNABAWA. Mutane suna son Aljannah suna son shigarta, amma basa san aikin wahala, Al-Jannah kuwa hanyoyinta cike suke da abubuwan da zuciya bata so, wallahi idan kana san shiga Al-Jannah da gaske sai kabi Allah kamar yadda Manzon Allah ya fada, kabi Al-Qur’ani da Sunnarsa Salallahu Alaihi Wasallam, sannan ne zaka rabauta, duk wani abu da ba wannan ba. Sunansa FANKAM FAYO.

Wasu mutane marasa tsoron Allah, suna fadin cewa akwai wasu sallolin Nafila da mutum zaiyi a daren rabin watan Sha’aban (Nisfu-Sha’aban) WAI Allah zai basu ladan Annabawa tun daga farkon duniya har karshenta! Hakika wannan ganganci ne, kuma galatsi ne ga Addinin ALLAH, duk mai furta irin wadannan muna nan kalamai hakika yana cikin tashin hankali ya sani ko bai sani ba.

Allahumma Ihdinas Siradal Mustaqeem.

Yasir Ramadan Gwale
22-06-2013

1 comment: