Friday, June 28, 2013

SHUGABA MURSI ZAI BAIWA MARA 'DA KUNYA A MASAR INSHA ALLAH



SHUGABA MURSI ZAI BAIWA MARA 'DA KUNYA A MASAR INSHA ALLAH

Daga Yasir Ramadan Gwale

Nasarar shugaba Muhammad Mursi nasara ce ba ga siyasar kasar Masar ba, Nasara ce ga dukkan masu kishin Islama. Hakika idan shugaba Muhammad Mursi ya samu Nasarar aiwatar da mulkin Demokaradiyya bisa tsarin sauye sauye na Islama ya kawo wani babban cigaba a tsarin gwagwarmayar tabbatar da Mulkin Dimokaradiyya bisa tsarin Musulunci. Shugaba Mursi ya dare kan karagar Mulki a cikin wani irin mawuyacin lokaci da saiyasar kasar Masar ta auka ciki tun bayan tunbuke gwamnatin Mubarak ta kama karya. Sanin kowa ne cewar tun bayan kifar da gwamnatin Mubarak kasar Masar ta kusan durkushewa ta fuskar tattain arziki da harkokin Diplomasiyya, bayan da soji suka karbe ragamar iko karkashin Filmashal Tantawi. 

A karon farko kafin bayyanar shugaba Mursi, wani fitaccen attajiri a cikin Jam'iyyar Muslim Brotherhood da ake kira Khairat Al-shata tauraruwarsa ta haska kafin daga bisani a haramta masa tsayawa zabe. Haramtawa su Khairat Al-shata tsayawa zabe ya baiwa Muhammad Muhammad Mursi damar shiga jerin sahun masu zawarcin kujerar gwamnati. Fitowar Mursi ta fara sauya akalar Siyasar kasar, domin yanayi ya nuna cewar masu kishin Islama daga Muslim Brotherhood ne zasu karbe ragamar ikon kasar. Bayan da aka yi zabe Mursi ya kai labarai wadan da basu yi nasara ba musamman daga cikin 'yan Adawa wadan da galibinsu gyauron gwamnatin Mubarck ne, suke ta aiki babu dare babu rana wajen ganin Mursi bai ci nasarar kawo sauye sauye masu ma'ana ba.

Da farko shugaba Mursi ya fada wani wadi na tsaka mai wuya, wanda za'a iya kiransa da gaba kura baya siyaki, domin yayi ta kiran mutane su zo su taimaka masa amma suna zillewa, sannan a gefe guda kuma, al'ummar kasar sun zurawa shugaba Mursi ido dan ganin ya kawo sauye sauye cikin kankanin lokaci, wannan ta sa da dama suka kasa baiwa shugaba Mursi uzuri, inda rahotanni suka dinga nuna cewar ana yawan samun arangama da daui ba dadi tsakanin magoya bayan Muslim Brotherhood da magoya bayan 'yan adawa wadan da ake hurewa kunne daga kasashen Turai da Amerika wajen ganin sun gurgunta tafyar siyasar shugaba Mursi.

Da yawan kasashen yamma basa son Masu kishin Islama su samu nasarar tafiyar da gwamnati bisa tsarin Musulunci. Wannan ta sanya suke mara baya ga 'yan adawa dan hanawa masu bin tsarin Islama zama lafiya a cikin gwamnatinsu. Irin haka ne ya faru a siyasar kasar Algeria inda su Boutouflika suka hana masu kishin Musulunci tafiyar da mukin bisa tsarin Isama zama lafiya. Yanzu ma irin misalin haka ne yake faruwa a kasar Tunisiya tun bayan tafiyar Zain-el Abideen Ben Ali.

Da dama daga cikin masu yin fashin bakin siyasar kasar masar, da kuma masu aiko da rahotanni musamman ga kafafan watsa labarai na waje, basa yin adalci ga gwamnatin Mursi, kullum suna ta yin kokari ne wajen nuna gazawar gwamnatin Mursi ba tare da bata wani uzuri ba, duba da irin yanayin da ta shigo, haka kuma, da dama daga cikin masu fashin bakin siyasar kasar daga ciki ko daga waje suna goyon bayan 'yan Adawa ne, wadan da suke da burbushin gwamnatin Mubarak a tare da su. Amma duk da haka insha Allah muna taya shugaba Mursi da addu'ah Allah ya bashi Nasara ya baiwa mara 'da kunya.

Yasir Ramadan Gwale 
28-06-2013

No comments:

Post a Comment