Thursday, June 27, 2013

HUKUNCIN KISAN DA AKA YANKE A JIHAR EDO HANNUNKA MAI SANDA GA MANJO HAMZA AL-MUSTAPHA


HUKUNCIN KISAN DA AKA YANKE A JIHAR EDO HANNUNKA MAI SANDA GA MANJO HAMZA AL-MUSTAPHA
A lokacin da za’a kashe Uwargidan Marigayi MKO Abiola, marigayiya Kudirat Abiola wasu abubuwa sun faru a daidai wannan lokacin da suke nuna alamaun cewar tsaro ya sukurkuce a daidai wannan yankin, a kuma wannan lokacin. Babu jimawa da yin wasu fashe fashe da salwantar rayuka aka kashe Alhaja Kudirat Abiola Allah ya jikanta. Haka abin yake lokacin da za’a kashe marigayi Shiekh Jafar Mahmoud Adam, sai da wasu al’amura suka faru da ke nunawa al’umma cewar akwai alamun cewa tsaro ya dan samu tangarda a yankin dorayi zuwa fanshekara da kewa, domin sai da aka samu rahoton cewa anyi fashi a caji ofis na Panshekara kuma an kwashi makamai an gudu, babu jimawa da aikata wannan fashin aka yiwa Shiekh Jafar Adam kisan gilla a wannan yanki. Allah shine masani!

A makon da ya gabata, gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole ya sanya hannu akan dokar zartar da hukuncin kisa akan wasu mutane da kotu ta yanke musu hukuncin kisa a jiharsa. Kafin zartar da wannan hukunci, tuni aka jiyo shugaban kasa Goodluck Jonathan yana karfafawa gwamnoni guiwa akan cewa duk mutumin da aka yankewa hukuncin kisa su gaggauta sanya hannu domin zartar masa da hukuncin kamar yadda doka ta tanada. Sakamakon da ya biyo baya ya bayyana cewar an aiwatar da wannan hukuncin kisa akan wadannan mutane da kotu ta yankewa hukunci, wala’allah bias umarnin Shugaban kasa Adams Oshiomhole ya sanya hannu. Wallahu A’alam!
Shakka babu wannan hukunci, hannunka mai sanda ne ga tsohon dogarin shugaban kasa Gen Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha cewar, za’a aiwatar da irin wannan hukunci akansa, matukar bai samu nasara ba a daukaka karar da yayi akan hukuncin kisan da wata kotu ta yanke masa a jihar Legas, ko da kuwan anje kotun Allah ya isa. Kamar yadda muka sani ne, cewar wata kotu ta yankewa Manjo Mustapha hukuncin kisa ta hanyar rataya a jihar Legas bisa zarginsa da ake yi wajen shirya da kisan da aka yiwa Marigayiya Kudirat Abiola. Allah shine masanin hakikanin wadan da suka kashe Kudirat.

Amma dai kisan Kudirat Abiola ba shine zai sanya a kashe Hamza Al-Mustapha ba ko da kuwa an tattabatar da cewar da umarninsa aka yi kisan. Sanin kowa ne, kamar kuma yadda shi kansa Manjo Mustpha ya bayyana, yasan sirrinin kasarnan ciki da waje, kuma yana da masaniyar irin yadda tsaffi da sabbin shugabannin Najeriya suka aiwatar da wasu al’amura na rashin gaskiya. Wadannan mutane da suka san da cewar Mustapha yana da masaniyarsu a hannunsa, dole zasu yi dukkan maiyuwuwa wajen ganin baifita raye ba, domin kuwa bazasu kai labari ba.

 Kasancewar Manjo Mustapha ya kwashe tsawon lokaci a daure wannan ta sanya ya samu tausayawar al’ummar Najeriya da dama a ciki da wajen Najeriya, wannan kuma wata manuniya ce da take nuna cewar dukkan ranar da Allah madaukakin sarki ya kaddari Manjo Mustapha da fitowa to hakika zai samu farin jini mai yawan gaske a idan talakawa wanda hakan kan iya zama silar shigarsa siyasa har ya kai ga tsayawa takarar Shugaban kasa, abinda ba zai yiwa Mafiyoyin kasarnan dadi ba.

Wadannan mutane da suke da wannan danyan kashi a gidinsu, shakka babu suna yin wannan lissafin, sannan kuma suna tunanin makomarsu. Dan haka kullum suke kwana suke tashi da batun Mustapha. Wannan ta sanya, Sai kaji an dauko shari’ar kamar da gaske za’a yita, sai kuma kaji ta lafa can sai bayan wani lokaci a kuma daukota a sake dogon turanci sannan a kara tafiya dogon hutu. Hakika tsare Mustapha tsawan wadannan shekaru babban zalunci ne da aka yi masa. Dan a kasarnan babu wata Shari’ah da ta taba daukar lokaci irin wannan. Domin kuwa ita kanta matar da ake zargin su Hamza Al-Mustapha da shirya kisan ta, ba wata muhimmiyar mace bace a tarihin siyasar Najeriya, babu wani mukami da ta rike wanda zai sanya a kalleta a matsayin wata mashahuriya, wancan laifukan da gungun mafiyoyin kasarnan suka aikata kuma suke da labarin Mustapha yana da masinyar inda aka je aka dawo, ya sanya aka yi amfani da shari’ar dan dauke hankulan mutane. Ai a Najeriya an kashe Su Tafawa Balewa da Sardauna da Murtala wadan da muhimman muatne ne wanda tarihin Najeriya ba zai taba cika ba sai an lissafo su, amma ba’a dauki wani mataki irin wannan da aka dauka akan kisan Kudirat Abiola ba, na shari’ah, ko kuwa wannan yana nuna mana cewar Kudirat Abiola ta fi su Sardauna da Tafawa Balewa da Murtala muhimmanci a Najeriya ne?

Al-Mustapha idan har anyi masa Shari’ah ta Gaskiya kuma an same shi da laifi aka yanke masa hukuncin kisa babu wanda zai ce ba’a kyauta ba. Amma shakka babu anzalunce shi a bisa tsawon lokacin da ya kwashe ba’a yi masa hukunci ba. Lokaci ne kadai zai bayyana mana gaskiyar yadda lamura suke. Allah ya raba nagari da mugu ya raba yari da barawo.

Yasir Ramadan Gwale

No comments:

Post a Comment